Sakonnin Masu Karatu (2013) (1)

Wannan fadakarwa daga daya daga cikin masu karatu. Muna masa godiya matuka. Allah bar zumunci.

84

Sakon Fadakarwa


- Adv -

“Assalaamu Alaikum, Baban Sadik don Allah ina son in ja hankalinka.  Idan masu tambaya suka rubuto maka tambaya, tare da yi maka sallama, maimakon ka amsa sallamar, sau da yawa sai kace “Barka da warhaka…” Da fatan za a gyara don kwadayin samun lada.”  Daga CPL Mamman B. Abdul Dambatta, Police College, Kaduna.

Wa alaikumus salaam, hakika na yi farin ciki da wannan fadakarwa naka.  Allah saka da alheri, ya kuma ba damar kara tunatar da ni a duk sa’adda aka hararo wani kuskure da na tafka ko nake tafkawa.  Kamar yadda na sha sanarwa, ni dan Adam ne, ina gafala kamar yadda kowa ke rafkana.  Hakika Allah ya bani ikon gyarawa daga yanzu.  Allah mana jagora, amin.

 

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.