Sakonnin Masu Karatu (2019) (19)

Rufe Shafin Facebook

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na ranar Jumma’a, 8 ga watan Nuwamba, 2019.

62

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki?  Allah ya taimaka, amin. Don Allah ina son a taimaka a turo mini da kasidar nan ta Bamuda Triangle ta wannan adireshin: nawaibrahimkabir346@yahoo.com.  Na gode.  Ibrahim Kabir Bakori: 08107110505

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ibrahim. Kamar yadda na sha sanarwa, akwai gidan yanar sadarwa na buxe inda nake taskance dukkan kasidun da nake rubutawa a wannan shafi mai albarka.  Kana iya ziyartar wannan shafi don samun dukkan maqalar da kake bukata, muddin na taba rubutu a kai.  Ga adireshin kamar haka: https://babansadik.com/category/teku.  Idan kabi wannan rariyar likau, za a riskar dakai ne kai tsaye ga vangaren dake dauke da maqalolin da suka shafi Teku, wanda maqalar Tsibirin Bamuda na daga cikin maqalolin dake wannan vangare.  Sai ka bisu daya bayan daya, za kaci karo da ita.  Allah sa a dace, ya kuma amfanar damu abin da muke karantawa ko rubutawa, amin.  Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina fatan kana lafiya.  Allah ya kara daukaka da basira. Dan Allah a taimaka ayi min bayani akan shafin Facebook dina.  Idan na jima ban yi amfani dashi ba, duk lokacin da na hau nasa lamba da kalmar sirri, sai ace na manta kalmar siirin.  Sai su turo min wata, da zarar na sa sai kawai inga ya buxe.  Amma kuma idan na sake hawa na sa wannan da suka turo min sai taki buxewa.  Dan Allah ayi min bayanin wannan matsala.  Daga Bashiru Musa Kura: 08105283189.

Wa alaikumus salam Malam Bashir, barka ka dai. Ina godiya da tarin addu’o’inku gareni.  Allah albarkacemu baki daya, amin.   Bayani kan matsalar da kake samu, ina iya cewa matsalar daga gareka take.  Tsawon lokacin da kake dauka baka hau ba ke sa ka mance kalmar sirrinka, wato: “Password”.  Shi yasa da zarar ka sa, sai ace ba daidai yake ba.  Lambobin da ake aiko maka ba su bane “Password” dinka.  Ga alama kana matsa inda aka ce: “Forget Your Password?”, sai a kaika inda za ka bukaci a aiko maka da lambobin tantancewa, wanda suke aiko maka ta layin wayarka ko imel dinka.  Wannan wata hanya ce ta musamman da hukumar Facebook ta tanada don taimaka wa masu mance kalmominsu na sirri ko wadanda wasu suka musu kutse a shafukansu, don samun damar sabunta kalmar sirri.  Shi yasa da zarar ka shigar da lambobin nan take sai a buxe maka.  Asali ya kamata a kaika shafin da za ka sake zaban sabuwar kalmar sirri ne, wato: “New Password”.  Wataqila baka lura ba, ko kuma an zarce da kai ne kai tsaye, domin tsare-tsarensu kan canja lokaci-lokaci.

- Adv -

Don haka, lambobin da aka aiko maka ka shigar na wannan lokacin ne kadai.  Aikinsu ba ya wuce mintina 15.  Wannan yasa da zarar ka zo hawa a lokaci na gaba, ka shigar dasu, sai ace maka ba daidai bane.  Aikinsu ya kare.  Abin da zaka yi yanzu shi ne, ka koma shafinka, ka shigar da lambar waya ko sunan da ka saba shigarwa, sannan ka latsa inda aka rubuta: “Forget Your Password?” ko wani abu makamancin haka.  Idan aka zarce da kai inda ake neman ka bukaci a aiko maka lambobin tantancewa, sai ka latsa.  Da zarar an aiko maka lambobin, sai ka shigar.  Shafi zai budo, zaka ga an rubuta: “Add New Password”, a kasa kuma an sa: “Retype New Password”.  Wurin farko ana so ne ka zabi sabuwar kalmar sirri.  A wuri na biyu kuma ana so ne ka maimaita kalmar da ka zaba, don tabbatar da cewa lallai kai xan adam ne, ba wata na’ura bace.  Kana gama haka shikenan.  Nan gaba idan ka zo hawa, sai kayi amfani da sabuwar kalmar sirrin da ka zaba.  Za a baka kofar shiga kai tsaye.

Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.

Salamun alaikum Baban Sadik. Da fatan anyi hidimar Sallah lafiya. Dan Allah na buxe shafi a dandalin Facebook, yanzu ba na bukatarsa. Yaya zanyi in rufe shi? Daga Aminu Ado.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Aminu.  Ai wannan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.  Kawai ka hau shafinka, idan a wayar salula kake hawa, sai kaje vangaren “Settings” sai ka gangara vangaren “Privacy”, ka shiga wajen.  Shafi zai buxe, inda za ka ga zabi guda biyu.  Na farko “Deactivate Account”.  Idan ka zabi wannan tsari za a kulle shafin na wani lokaci kawai.  A duk sadda kaga dama ka sake hawa, shafin zai dawo da dukkan bayananka.  Na biyu kuma shi “Delete Account”.  Wannan tsarin idan ka zabe shi, za a rufe shafin ne, sannan a goge shi gaba daya, bayan makonni biyu.  Idan makonni biyu basu gama cika ba ka dawo ka hau, za a tambayeka ko kana son ci gaba da tafiyar da shafin ne?  Idan kace eh, sai a zarce da kai.  Amma idan kace a a, za a wullar dakai waje, a sake kulle shafin.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.