Sakonnin Masu Karatu (2019) (12)

Kare Shafin Facebook Daga Masu Kutse

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Afrailu, 2019.

523

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aka ji da kokari? Ni ma a taimaka mini da bayani akan yadda zan kare shafin Facebook dina daga masu kutse.  Na gode. Daga Haruna Usman: usmanharuna265@gmail.com.  

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Haruna.  Idan kana son tsare shafinka na Facebook ko akwatin Imel dinka daga sharrin masu kutse (Hackers), na farko ka zabi kalmar sirri (Password) mai tsauri, mai dauke da haruffa da lambobi da kuma alamomin rubutu (irin su @ ko # ko $ misali), kuma kada ta kasance gajeriya.  Ana son adadin kalmar sirrinka ya fara daga takwas zuwa sama, iya abin da za ka iya tunawa.  Kada kasa lambar wayarka.  Kada kasa sunanka.  Kada kasa suna gari ko danka ko wani na kusa dakai.  Kada kasa ranar haihuwarka.  A takaice dai, ka zabi abin da idan ba kai ba, babu wanda zai iya hararo shi, sai in ka gaya masa.

Na biyu ka tanadi lambar waya da kuma adireshin Imel a shafinka, saboda bacin rana.  Na uku, ka boye su daga shafinka, ma’ana kaje bangaren “Settings” ka canza tsare-tsaren dake can, ya zama ba kowa zai ga lambar wayarka ba, ko adireshin Imel dinka, sai wanda ya kaga damar bayyana masa bayan ya nema.

- Adv -

Abu na hudu, kada ka taba bai wa wani kalmar sirrinka.  Idan har bukata ta sa ka ba wani ya sani, to, da zarar dalilin ya wuce kayi maza ka canza.  Na biyar, idan a waya kake amfani da Facebook, ya zama duk sadda ka gama aika sako ko karantawa, ka sauka, ma’ana: “Sign Out”.  Wannan zai taimaka maka matuka idan wayar ta fadi ko wani ya sace, bazai iya isa ga shafi ko sakonninka ba. Amma idan kullun a kan shafin kake, don kawai kana son ka rika ganin sakonnin dake shigowa, to ana samun matsala nan take wanda ya dauke wayar zai iya ganin dukkan sirrikanka.

Abu na shiga, ka san da wa zaka rika abota, sannan da wa zaka rika hira a Facebook.  Sannan wasu kalmomi kake fada ko rubutawa.  Duk wata kalma da kana yawan ambatonta a Facebook, kada ta zama cikin Passowrd dinka.

Wadannan, a takaice, sune matakan da a yanzu zan iya hararowa.  Allah mana tsari da miyagu, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    MASHA ALLAH

Leave A Reply

Your email address will not be published.