Hanyoyin Da Kafafen Sada Zumunta Ke Samun Kudaden Shiga (4)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a 6 ga watan Agusta, 2021.

270

Kamfanin Twitter

Wannan kamfani an kafa shi ne a shekarar 2006; shekaru 15 kenan a halin yanzu.  Kamar abokan hamayyarsa a fagen kasuwanci (Facebook da Google), kamfanin Twitter shi ne mamallakin shafin Twitter, wanda daya ne daga cikin manyan kafafen sada zumunta dake Intanet.  A halin yanzu yana da adadin masu rajista sama da miliyan 350.  A duk yini, an kiyasta yana samun maziyarta da ba su kasa miliyan 192 daga fadin kasashen duniya.

Asalin shafin Twitter an kirkireshi ne don baiwa masu rajistar damar wallafi manufofinsu da fahimtarsu a fagen rayuwa baki daya – al’ada, siyasa, addini, dabi’u, shugabanci da sauransu.  Da daidaikun mutane da kamfanonin kasuwanci, duk kowa na da damar wallafa bayanai don tallata kansa, ko kasuwanci, ko manufofinsa na siyasa, muddin hakan bai ci karo da ka’idojin mu’amala da kamfanin ya tanada ba.  Babbar manufar shafi ko kamfanin Twitter ita ce baiwa kowa fadin albarkacin bakinsa, tare da cire kowane irin tarnaki ne dake dabaibaye hanyoyi da na’urorin sadarwa, wajen samun ingantattun bayanai a Intanet, musamman.

Kana iya wallafa ra’ayinka cikin haruffan da basu shige 280 ba.  A farkon lamari an kayyade haruffan ne zuwa 140. Daga baya ne aka kara zuwa 280.  Bayan haka, a rana kana iya wallafa sakonni daga daya har zuwa 2,400.  Wannan ke nuna iya girman ‘yan ci da aka baiwa mai shafi a kan wannan dandali na Twitter.

- Adv -

Shafi ko Dandalin Twitter na dauke da mafi girman hanyoyin wallafa bayanai ne guda hudu.  Hanya ta farko ita ce rubutaccen sako mai ninki daya.  Wannan shi ake kira: “Single Tweet”.  Sako ne guda daya, wanda ke dauke da haruffan da basu wuce 280 ba.  Nau’in hanyar wallafa sako na biyu shi ne sako mai goyo, wanda ake kira: “Tweet thread”.  Wannan nau’in sako na dauke ne da sakonni daya bayan daya, a jikin sako daya.  Saboda karancin adadin haruffan da aka kayyade wajen rubuta sakonni a Twitter, an bullo da wannan hanya ce don baiwa masu son isar da sako mai tsayi, wanda ke dauke da bangarori daban-daban masu alaka da juna, damar yin hakan cikin sauki.  Shi yasa, galibin masu shugabannin kasashe dake Twitter, da Gwamnoni, da shugabannin kamfanoni, da ‘yan jaridu da kamfanonin yada labarai, duk suna amfani da wannan hanya wajen rubuta sakonni masu tsayi, musamman jawabin bayan taro, ko jawabin shugaban kasa, da sanarwa ga al’umma da dai sauransu.  Wadannan hanyoyin wallafa sakonni biyu sun shafi zallar rubutu ne, wato: “Written texts”.

Sai nau’in hanyar wallafa sako na uku, wato ta hanyar daskararren hoto, wato: “Images”.  Wannan hanya tana da sharudda, duk da cewa ba dole bane binsu, wajen tsara hoton da za a wallafa a shafin.  Kamar Dandalin Facebook, duk wani hoto mara motsi, ko bidiyo, duk suna da ka’idar girma – wajen tsayi, da fadi, da nau’i, da kuma inganci.  To, haka ma a Dandalin Twitter.  Amma idan ka dora hoton da bai cika wadannan siffofin ba, ba ya nufin bazai hau ba.  Galibi dandalin kan dauka, musamman idan yanayin tsayi ne ko fadin hoton da ake son dorawa bai kai ba.  Amma idan hoton da kake son wallafawa mai dauke da sakon da kake son isarwa bai dace da nau’in jakar bayanin ba (file type), wannan ba ya yiwuwa.  Misali, galibn nau’in hoton da shafukan sada zumunta suka shardanta ga hotunan da ake son wallafawa a shafukansu su ne wadanda suka kare da: “.jpg”, ko “.jpeg”, “.ping”, ko kuma “.svg”.  Wadannan sune shahararrun nau’ukan jakan bayanan da hotuna ke dauke dasu a Intanet.

Sai hanyar wallafa bayanai a Twitter na karshe, wato hanyar hoto mai motsi.  Wannan ya hada da hotunan bidiyo, da sauran makamantansu irin su hotunan katun (cartoons), da “memes”, da kuma “gif”.  Dukkan wadannan nau’ukan hotuna ne masu motsi da ake amfani dasu wajen isar da sakonni a Intanet a yau.  A Twitter duk kana iya amfani dasu wajen wallafa ra’yoyinka a kan wannan dandali, muddin ka cika sharuddan da dandalin ya tanada wajen wallafa, kamar yadda bayani ya gabata a baya.

Sabanin dandalin Facebook dake dauke da kowane irin nau’in jama’a, Dandalin Twitter na dauke ne kamfanonin kasuwanci, da hukumomin gwamnatoci, da shugabannin kasashe, da ministocin kasashe, da mashahuran mtuane da duniya ke ji dasu a fannoni da dama.  A takaice dai, Dandalin Twitter mahalli ce ta ‘yan kwari.  Ko kuma, kamar yadda wasu ke cewa, mahalli ne na “’yan boko”.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.