Ku Inganta Mana Makarantunmu Na Kimiyya da Kere-Kere (2)

Wannan shi ne kashi na biyu a jerin kasidar da muka faro makon jiya. A sha karatu lafiya.

178

A wani bincike na musamman da ya gudanar, Salawu Abidin Alamu (2012), daya daga cikin kwararru da ke Cibiyar Bincike kan Zamantakewa da Tattalin Arziki  (Nigerian Institute of Social and Economic Research – NISER) da ke Ibadan, ya dada fito da lamarin fili, saboda gamewar binciken.  A cikin bincikensa mai take: Halin da Kayakkain Karantar da Kimiyya da Kere-kere Ke Ciki a Makarantun Sakandare (The State of Science and Technology Infrastructure in Nigerian Secondary Schools), ya gudanar da bincike ne kan Cibiyoyin Binciken Kimiyya da Kere-kere da ke makarantun sakandare na jihohi shida dake dukkan shiyyoyin kasar nan, wato: Science and Technology Laboratories.  Ya kasa kasar zuwa shiyyoyi shida; inda ya dauki Jihar Bauchi, da Katsina daga Arewacin Najeriya. Ya dauki jihohin Edo da Inugu daga bangaren kudu maso gabas.  Sannan ya dauki jihohin Legas da Kwara, a shiyyar kudu maso yamma.  A kowace jiha kuma ya dauki samfurin makarantu 20 ne.

Kenan, sakamakon wannan bincike ya kumshi makarantun sakandare guda 120, wadanda suka shafi makarantun jeka-ka-dawo (Day Secondary Schools), da na kwana (Boarding Schools), da wadanda ke cikin maraya, da na karkara, da makarantun gwamnati, da na masu zaman kansu (Private Schools).  Binciken dai kan halin da tsarin karantar da fannin kimiyya da kere-kere da sana’o’in hannu ke ciki, tare da ingancin kayayyakin karantar da wannan fanni a makarantunmu na sakandare.  To me wannan bincike ya gano?

Abu na farko da wannan bincike ya gano shi ne, kashi 31 daga cikin kashi 100 na malaman wadannan makarantu ne kadai ke karantar da fannin kimiyya da kere-kere.  Sauran suna karantar da wani fanni ne daban.  Wannan kuwa ya saba wa tsarin dokar Kundin Ilimi na kasa (National Policy on Education) da ya tilasta baiwa fannin kimiyya da kere-kere da sana’o’i muhimmanci a dukkan makarantu a Najeriya.  Wannan adadi na kashi 31 cikin dari, bai yi la’akari da inganci ko cancanta ko kwarewarsu ba fa.  Wannan a bangaren adadin malamai kenan.

A daya bangaren kuma, daga cikin wadannan makarantu 120, binciken ya gano cewa kashi 17.5 ne suka mallaki dakunan gwaje-gwajen kimiyya da kere-kere fiye da 5, a yayin da sauran kashi 82.5 din duk dakunan gwaje-gwajensu basu shige tsakanin 1 zuwa 5 ba.  Dangane da dadewar gine-ginen dakunan gwaje-gwajen kuma, binciken ya gano cewa mafi karancin shekarun gininsu shi ne shekara 1, mafi yawancin shekaru kuma shi ne 30!  Wannan ke nuna galibin gine-ginen tsofaffin gini ne; kashi 55 an gina su ne tsakanin shekara 1 zuwa 10, kashi 45 kuma an gina su ne tsakanin shekaru 10 ne zuwa 30 ko sama da haka.

Dangane da abin da ya shafi tallafi wajen tafiyar dasu, hukumomin makarantun ne ke hidimar kashi 68.5 na dawainiyar tafiyar da wadannan dakunan gwaje-gwajen kimiyya.  Gwamnatin jihohi kuma na daukan kashi 70.9 cikin dawainiyar tafiyar da dakunan. A yayin da hukumar Hadin Gwiwa tsakanin Malamai da Iyaye (Parents Teachers Association – PTA) ke daukan dawainiyar kashi 7.5 na hidimar ingantawa da lura da wadannan dakunan gwaje-gwaje.

A bangaren makamashin lantarki kuma, kashi 30 daga cikin wadannan makarantu ne ke samun wutar lantarkin gwamnati tsakanin sa’o’i 2 zuwa 4.  Kashi 21 kuma na samun wutar lantarki tsakanin sa’o’i 6 zuwa sama.  A daya bangaren kuma, kashi 74.1 daga cikin wadannan makarantu na dogaro ne da janareto, ko  makamashin hasken rana (Solar Energy), ko kuma na’urar taskance makamashin lantarki mai suna Inverter.  Wannan, a takaice, na tabbatar da cewa wadannan dakunan gwaje-gwaje na fama da matsaloli da dama, musamman kan makamashi da kuma rashin ingancin malamai da dakunan gwaje-gwajen kimiyya da kere-kere. Wannan kadan ne daga cikin manyan matsalolin da wadannan makarantu ke fuskanta.

Bayan dukkan wannan, mai bincike yayi hira da jami’ai ko shugabannin wadannan makarantu, inda suka dada tabbatar da manyan dalilan da suka jefa su cikin halin da suke ciki.  Gaba dayansu sun yi amanna cewa rashin isassun kudaden shiga da tasarrafi na da nasaba da abin da ya jefa su cikin wannan hali.  Bayan haka, kashi 80 daga cikinsu sun yarda cewa, rashin kwararrun malamai a fannin kimiyya da kere-kere da sana’o’i matsala ce babba da ta taimaka wajen kawo rashin inganci a wadannan fannoni.  Sai kuma kashi 60 da suka amince cewa matsalar rashin wutar lantarki ko karancinsa, na cikin manyan matsalolinsu.

- Adv -

Mummunan Tasiri

Daga bayanan da suka gabata mai karatu zai fahimci hakikanin halin da karantar da ilimin kimiyya da kere-kere da sana’o’i ke fuskanta a matakin sakandare.  Mummunar tasirin hakan kuwa ba a boye yake ba.  Duk da yawan makarantun da muke dasu (duk da cewa wasu na ganin sai an kara, saboda karancinsu), babu inganci cikin karatu balle hakan ya bayyana.  Na sanar damu a farko cewa, galibin masu aikin kafinta, da masu aikin lantarki, da masu aikin gine-gine, duk za ka samu ba wani sakamakon karatun kwarewa suke dashi ba a fannin.  Koyo ne irin na kan titi, har Allah yasa albarka cikin lamarin.

Shekaru 20 da suka gabata, galibin wadanda suka yi karatu a kwalejin kimiyya na gwamnati da ke warwatse a jihohi, sun samu karatu mai inganci, da kwarewa ta hakika. Wani bawan Allah ke gaya min cewa, sanadiyyar horo da ya samu a matakin sakandare shekarun baya, ya yi wa wani baffansa aikin jona wutar da lantarki a sabon gidansa da ya gina.  Yace har yanzu wannan aiki da yayi masa yana nan daram, ba a canza ba kuma ba a samu matsala ba.  Yace akwai abokinsa da ya samu horo a fannin sarrafa katako (Wood Work) sadda suke sakandare, a yanzu ya bude shago nasa na musamman inda yake horar da wasu, sannan ya kware ta yadda duk kyaun kujera ko gado ko duk wani abu da za a iya sarrafa shi, idan ya ganshi, zai iya kera irinsa.  Duk wannan daga horon da ya samu ne a matakin sakandare. Yanzu samun irin wannan karewa da wahala yake, in ma za a samu.  Amma a zamanin baya yace za ka samu makaranta musamman, kusan duk abin da ake amfani da shi na kayayyakin zama, da abubuwan lantarki, da kayayyakin aiki a dakunan gwaje-gwaje, duk daliban makarantan ne ke kerawa; ba sai an kira wani kanfani ko an sayo daga wata kasa ko wuri ba.  Ire-iren wadannan abubuwa a halin yanzu zai yi wahala a same su a makarantunmu na kimiyya da kere-kere, na gwamnati ne ko na masu zaman kansu.  Me yasa?

Babban abin da ke damunmu a farko, wanda ya shanye kowane irin matsala da dalili, shi ne matsalar rashawa.  Wannan matsala, kamar yadda kowa ya sani, ta shafi kowane bangaren rayuwa a kasar nan, har da bangaren ilimi.  Don haka, muddin muna bukatar inganci a cikin al’amuranmu baki daya; daga mulki zuwa karatu, da kiwon lafiya, da sana’a, har zuwa addini, dole ne mu yi wa kanmu adalci wajen aiwatar da abin da ya kamata, a yanayin da ya kamata, a kuma lokacin da ya kamata.  Duk kasashen duniya sun gane cewa wannan ita ce babbar matsalar Najeriya.  Me yasa?

Cikin karshen watan Afrailu ne wata jarida mai suna Premium Times ta nakalto labarin cewa hukumar Najeriya ta baiwa wani kamfanin kasar Isra’ila mai suna EL-BIT SYSTEMS kwangilar lura da shafukan yanar Intanet da ‘yan Najeriya ke mu’amala da su, da irin sakonnin Imel da suke aikawa ko suke karba; duk a karkashin kokarin hukuma wajen yaki da ta’addanci.  Wannan kwangila an bayar dashi ne a kan Dalar Amurka Miliyan 40 ($40 million).  Daga baya gwamnatin tarayya, kamar yadda wannan jarida ta sake nakaltowa, bata jin dadin yadda wannan kamfani ya bayyana wannan kwangila ga ‘yan jarida ba.  Domin a yanzu duk hankalin jama’a ya tashi, cewa za mu koma ‘yan gidan jiya kenan. Duk abin da muke yi Gwamnati na lura damu.  Hatta sakon Imel da kake aikawa ko aka aiko maka, hukuma na iya ganinsa.  Ba wannan bane matsalar.

Shin, me zai hana gwamnati tayi amfani da wannan zunzurutun kudi (wajen Naira Biliyan shida ne) don inganta rayuwar ‘yan Najeriya, ta hanyar samar da ayyukan yi, da inganta makarantu, da inganta tsarin sadarwa don sawwake tsananin rayuwa ga jama’a.  Daga shekara ta 2010 zuwa yanzu, mutum nawa suka rasa rayuwarsu?  Mata nawa suka zama gwagware?  Yara nawa suka zama marayu?  Makarantu nawa aka kona ko aka rusa?  Mutum miliyan nawa suka rasa gurabun ayyukansu?  Kuma mutum miliyan nawa ke rayuwa cikin firgici da raurawan zuci?  Hukuma ta san halin da ake ciki tabbas, amma me yasa za a ciyar da wannan zunzurutun kudi kan abin da babu tabbacin zai yi aiki ko bazai yi ba, saboda yadda wasu makamantansu suka kasance a baya?  Sannan me ye tasirin wannan aiki waje kawo zaman lafiya ma ga kasar baki daya?  Yana da kyau gwamnati ta sake tunani kan wannan lamari.

Akwai bayanai da ke nuna rashin jin dadin gwamnati sanadiyyar bayyana wannan kwangila da kamfanin yayi, wanda bayan wannan kudi da kamfanin zai samu, akwai wasu dala miliyan 20 ($20 million) da aka kebance don “sauran ayyuka masu nasaba da kwantiragin.”  Idan wadannan labarai sun tabbata, wannan na nuna har yanzu bamu san halin da hukumomin kasar nan suke ciki ba.  Wannan a bangaren rashin tsari kenan, kafin mu fara tattauna wannan lamari ta bangaren mahangar kimiyyar sadarwar zamani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.