Sakonnin Masu Karatu (2019) (11)

Tsarin Amfani da Na'urar "Power Bank"

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Afrailu, 2019.

368

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina so ayi mini cikakken bayani, wai shin, da gaske ne na’urar “Power Bank” tana kashe batir din waya?  Daga Abdul Gwangwan.

Wa alaikumus salam Malam Abdul Gwangwan.  Na’urar “Power Bank” dai na’ura ce dake taimakawa wajen cajin batirin wayar salula a lokacin da mutum ke nesa da na’urar cajinsa ko kuma aka dauke wutar lantarki.  Wannan na’ura dai tana dauke da bangarori guda uku ne.  Bangaren farko shi ne asalin gangar-jiki ko bodin dake dauke da kayan dake ciki.  Bangare na biyu kuma kwayar batirin dake bayar da makamashin caji, wato: “Battery Cell” kenan.  Sai bangare na uku, wato allon dake dauke da batirin da sauran hanyoyin da makamashin lantarki ke bi don isa ga batirin wayar.  Wannan allo shi ake kira “Printed Circuit Board” ko “PCB” a gajarce.  Shi ne bangare mafi mahimmanci a jikin na’urar “Power Bank”.  Kusan galibin na’urorin sadarwa na lantarki na zamani suna amfani da wannan allo.  Idan ka bude zaka ganshi a kwance, sauran kayyaki na kanshi.  Yana da zane-zane da kuma ramuka kanana, inda wayoyi ke kutsawa ciki.  Wannan shi ne “Printed Circuit Board”, ko “PCB” a gajarce.

Wannan na’ura na “Power Bank” dai na da matakan caji guda uku ne, da zarar ka jona ta da wayarka don yin caji.  A matakin farko na’urar na bulluko makamashin lantarki ne cikin gaggawa, don ingiza kaso mafi yawa na caji zuwa cikin batirin wayarka.  Wannan mataki shi ake kira “Rapid Charging Stage.”  Sai matakin caji na biyu, wanda ke ci gaba da aika makamashin lantarki aka-akai, amma ba da gaggawa irin yanayin mataki na farko ba.  Wannan mataki shi ake kira:  “Continuous Charging Stage.”  Sai mataki na uku kuma na karshe, wanda ke aika makamashin caji kadan-kadan, don cika batirin wayar, tare da karfafa sinadaran cajin dake cikin batirin wayarka, don daukan lokaci mai tsayi kafin cajin ya fara sauka.  Wannan mataki shi ake kira:  “Trickle Charging State.”  Idan aka yi kuskuren zare waya daga jikin wannan na’ura ko jikin makamashin lantarki yayin da take wannan mataki na caji, to, cajin bazai dade ba zai kare.

- Adv -

Tambayarka na son sanin ko wannan na’ura na lalata ko kashe batirin wayar salula ne idan aka lazimci caji da ita?  Amsar ita ce, ya danganta.  Shi amfani da na’urar “Power Bank” wajen cajin waya yana da ka’idoji.  Na farko shi ne, ya zama mizanin batirin wayarka kasa yake da mizanin batirin “Power Bank”, ko daidai dashi.  Abin da wannan ke nufi shi ne; kowane batir na da mizani. Misali, idan mizanin batirin wayarka 2,500 mAh ne, to, ya zama mizanin “Power Bank” dinka ya dara shi – ya zama kamar 3,000 mAh ne.  Amma idan mizanin batirin wayarka ya fi na na’urar “Power Bank”, to, bazai iya cajin wayarka ba daga 0 – 100% ba.

Na biyu, ya zama karfin sinadarin batirin wayarka (Voltage) ya dara na na’urar “Power Bank.”  Misali, idan karfin sinadarin batirin wayarka boltej biyar ne (5V), na na’urar “Power Bank” kuma hudu da rabi (4.5V), nan ma za a samu matsala.  Dole na na’urar “Power Bank” ya dara na wayarka.  Amma idan na wayarka ne ya dara na “Power Bank”, to duk sadda ka jona wayarka maimakon na’urar “Power Bank” ta caja maka batirin, sai ya zama ragowa cajin dake batirin wayarka ne zai rika komawa jikin na “Power Bank” din. Ma’ana, karfin sinadarin batirin wayarka ya gaza kenan.  Sai ka’ida ta karshe, shi ne ka samu na’urar “Power Bank” mai inganci, na asali, gangariya daga kamfani sananne.  Idan ya zama bangaren PCB dinta jabu ne, to duk sadda ka tashi caji zaka ji wayarka ta dauki zafi, kamar za ta kone.  Idan kaga haka, to, hanya mafi sauki kawai ka zare wayarka, in ba haka ba tana iya bindiga ta kone, ko ta babbake muddin hakan ya ci gaba.  Kuma alamar cewa lallai sinadaran batirin wayarka sun gaza na na’urar “Power Bank” din da kake caji da ita kenan.

Daga bayanan da suka gabata zai bayyana maka cewa lallai muddin ba a bi ka’idar cajin waya da na’urar “Power Bank” ba, to, a karshe hakan zai iya sabbaba matsa ga batirin har ma wayar.  Da fatan ka gamsu.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.