Sakonnin Masu Karatu (2019) (9)

Tsarin Gudanuwar Na'urar ATM

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Afrailu, 2019.

253

Assalamu alaikum Baban Sadik. Da fatan kana lafiya. Ina bukatan bayani a kan na’urar cire kudi ta ATM, a sawwake.  Daga Abdullahi Jalingo.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdullahi.  A baya mun gabatar da bayani mai tsayi kan wannan na’ura tun farkon bayyanarta a Najeriya.  Amma a takaice, na’ura ce da ake amfani da ita wajen cire kudin da ka adana a taskar bankinka.  Bayan cire kudi ma, kana iya amfani da na’urar ATM wajen aika wa wani kudi kai tsaye, wato “Instant Transfer” kenan.  Abin da haruffan “ATM” ke nufi shi ne, “Automated Teller Machine”, wato na’urar bayar da kudi mai sarrafa kanta.

Wannan na’ura dai tana dauke ne da manyan bangarori guda uku.  Na farko shi ne asalin na’urar, wato kwarangwal dinta kena.  Wannan shi ake kira “Hardware”.  Sai bangare na biyu wanda ya kunshi manhajar dake sarrafa na’urar, wannan shi ake kira: “Software”.  Sai bangare na uku da ya kunshi yanayin sadarwar da na’urar ke amfani dashi wajen aiwatar da harkokinta.  Wannan kuwa ya hada da tsarin sadarwa tsakaninta da kwamfutocin da ke sarrafata daga cikin bankin da take makale a farfajiyarsa.  Sai kuma yanayin sadarwar dake hada alaka tsakanin ita na’urar da kuma kamfanin dake aiwatar da tsarin musayar kudade tsakanin bankuna a Najeriya.  Wannan kamfani shi ake kira “Interswitch”.  Shi kadai ne ke da alhalin wannan aiki a Najeriya a halin yanzu.

Yadda wannan na’ura ke aiki kuwa shi ne, a duk sadda kazo ka zira katinka a cikinta, za ta bukaci ka bata kalmar sirrin da bankinka ya baka sadda kake karban katin.  Da zarar ka rubuta, za ta tambayeka me kake son yi?  Kana iya zaban cire kudi, ko duba balas, ko sauya kalmar sirri ko wani abu daban.  Da zarar ka zaba, sai a kaika inda kake so.  Idan cire kudi ne, za a tambayi nau’in taskarka; “Current” ne ko “Savings”? Idan ka zaba, nan take sai na’urar ta kaika inda zaka zabi adadin kudin da za ka cire.  Kana gaya mata, sai ta aiwatar da sadarwa da bankinka don tabbatar da samuwar adadin kudin da kake son cirewa.  Idan ka cika ka’ida, sai kawai ta aiko maka.  Idan kuma na’urar da kake amfani da ita ba na bankinka bane, bayan an baka kudin kuwa, sai kamfanin Interswitch ya zaftare adadin kudin da na’urar ta baka daga taskarka dake bankinka, ya zuba a taskar bankin da ka ciri kudin daga na’urar ATM dinsu.

Wannan a takaice shi ne bayani kan na’urar ATM.  Don Karin bayani, kana iya ziyartar shafin TASKAR BABAN SADIK don karanta asalin kasidar da na gabatar kan wannan na’urar, shekaru 8 da suka shude.  Kana iya isa ga wannan kasida a wannan adireshi: https://babansadik.com/yadda-naurar-atm-ke-aiki-1.  Da zarar kaje karshen wannan kasidar, za ka ci karo da kashi na biyu.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina yi maka fatan alkhairi tare da godiya da irin abubuwan da muke amfanuwa da su. Allah ya kara basira.  Ina neman shawararka game da wani wanda ya sace min account dina na Facebok ya canza sunana kuma yake amfani da sunansa.   Amma kuma da abokaina yake mu’amula.  Ta yaya zan dawo da sunan nawa?  Sako daga Idris Ibrahim Yarganji.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Idris.  Ina godiya da addu’o’i.  Dangane da bukatarka kan wanda ya sace maka shafinka na Facebook, ya canza sunan sannan yake mu’amala da abokanka da shafin, zai dace in san shin, ya zuwa yanzu da aka kwace maka shafin, kana iya hawa shfin ne?  In eh, to, sai ka canza kalmar sirrinka kawai kai tsaye ba tare da wani bata lokaci ba.  Bayan ka canza kalmar sirri, sai kaje bangaren “Settings” ka canza sunan zuwa sunan shafin na asali.  Wannan zai kare shafin nan gaba daga kutse.

Amma idan ya kwace shafin ne gaba daya ba ka iya komai a kai, shin, ya cire lambar waya ko adireshi Imel din da ka sanya a shafin ne?  Za ka iya gane gakan idan kayi kokarin hawa shafin da “Password” dinka na baya, za a ce ba daidai bane, “Kana son canza password dinka ne?”, sai ka matsa eh.  Daga nan za a zarce dakai wani shafi mai dauke da bayanan da kake amfani dasu wajen hawa shafin.  A nan ne zaka gane idan ya cire su ko bai cire ba.  Idan bai cire su ba, to, abin da sauki, wai cire wando ta ka.  Sai kawai ka bukaci a aiko maka lambobin tantancewa (Verification Code) zuwa lambar waya ko adireshin Imel din.  Ana aiko maka sai kayi maza ka shigar a inda aka tanada, za a zarce dakai shafin da zaka sanya sabuwar kalmar sirri (Password).  Da zarar ka canza sai kawai kaje bangaren “Settings” ka canza sunan zuwa sunan da kake sha’awa.  Sai dai kuma wani abin lura, idan har bai kai watanni shida da canza sunan ba, ba za a bari ka iya sake canza sunan ba sai bayan watanni shida.

To, amma idan ka samu ya cire dukkan bayanan da Facebook za su iya tuntubarka dasu ya sanya nashi, a nan kam sai hakuri, a galibin lokuta.  Don haka, idan ka tarar da hakan, kana iya tuntubata ta hanyar aiko mini sakon tes (kada ka kira layin), don duba lamarin, inga ko za a iya kwato shafin.

Wannan shi ne takaitaccen bayanin da zan iya yi.  Allah sa a dace, ya kuma yi jagora, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.