Sakonnin Masu Karatu (2018) (7)

Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

167

Assalamu alaikum Baban Sadik, sunana Aliyu Tahir, amma akan kirani da “Dct Alikson”. Tambayata a nan shi ne: wai shafin nan yana aiki kuwa? Saboda a kullum ina yawan ziyartarsa amma ba na ganin sababbin kasidu, musamman na wannan shekaran, ko me yasa? Sai na ji daga gareka. Naka har kullum: aliyutahir072@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aliyu.  Lallai shafin yana aiki, kuma ana loda sababbin kasidun da ake bugawa a shafin AMINIYA.  Idan kana son ganin sababbin kasidu, da zarar ka hau shafin, bangaren farko daga can sama kurya, za ka sababbin kasidu suna yin zirya daga dama zuwa hagu.  Bayan haka, da zarar ka gangaro inda jerin kasidu suke masu dauke da tambarin hotunansu, duk kasidar da ka gani tana zirya (Sliding) daga dama zuwa hagu, dauke da hotuna, to, duk sababbin kasidu ne. 

Sai dai kuma, kasancewar wannan shafi dake AMINIYA a duk mako yake bayyana, wannan yasa ba za a wata sabuwar kasida ba sai bayan mako.  Duk da cewa ina sa ran bude wani shafi na musamman karantar da wasu nau’ukan ilimi kan fannin sadarwa a matsayin makaranta, wanda hakan zai ba da damar samun bayanai sababbi akai akai, sai dai a yanzu wannan tsari ne ke gudanuwa.

Kuma idan baka mance ba, kusan watanni biyu zuwa uku da suka gabata muna ta amsa tambayoyi ne.  Wannan yasa dukkan sababbin kasidun na tambayoyi ne da amsa, kamar yadda za ka gani.  Da fatan ka gamsu kuma na gode.


Assalamu alaikum, ina fatan kana lafiya.  Shin ko kana da makarantar koyar da ilmin kwamfuta ne?  Na gode. Ni ne: Alhassan Beli, karamar hukumar Shira, jihar Bauchi:  Imel: alhassanelbabeli@yahoo.com 

Wa alaikumus salam Malam Alhassan, a halin yanzu ban da makaranta a zahiri na karantar da wannan ilimi, sai dai nan kusa cikin dacewar Allah ina sa ran samar da makaranta ta Intanet don aiwatar da hakan.  Idan lokaci yayi zan sanar in Allah yaso.

Na gode matuka kuma Allah saka da alheri, amin.


- Adv -

Assalamu Alaikum Baban Sadik, sunana Hassan Muhd Hassan Daurawa, Kano.  Don Allah kasidun Prof. Abdallah Uba Adamu wadanda yayi kan ICT muke neman alfarmar in an samu lokaci a turo mana, don mu karanta mu amfana. Mun gode: Hassan Muhd Hassan: hmhmgr07@gmail.com 

Wa alaikumus salam Malam Hassan, barka dai. Kana iya duba akwatin Imel dinka don daukan wannan kasida.  Kasida ce guda daya wacce yayi mai take: “Hausa and Information Communications Technologies (ICTs)”, kuma ya gabatar da kasidar ne a shekarar 2004.  Bayan haka, kasidar na dauke ne da wasu haruffa na Hausa masu lankwasa, wadanda ke bukatar manhajar harafi na musamman kafin su bayyana.  Farfesa Abdallah ya samar da wannan manhaja wanda sai ka yi amfani da ita kafin ka gansu.  Na hada maka da manhajar (mai suna: “abdallah.ttf”).  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, muna godiya da fatan alheri gareka.  Wai me yasa ba a ganin kasidu kamar kashi na (1), da na (2), da na (3), sai dai na (4), ko na (8), ko na (9)?  Me yasa ba a ganinsu a jere?  Na gode.  Usman Muazu: usmanmuazu14@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Usman barka dai.  Ina kyautata zaton kana nufin a Taskar Baban Sadik (www.babansadik.com) ne.  Hakan ya faru ne saboda kasidun karshe ne ke zama a sama, duk wanda yazo sai fara dasu.  Idan kana bukatar ganin sauran, a kasan kowace kasida, za ka ga wacce ta gabace ta a bangaren hagu.  A bangaren dama kuma za ka ga taken wacce ke zuwa bayan wacce ka karanta.

Misali, idan ka karanta kashi na (3) ne, kana zuwa kasan kasidar, za ka ga wacce ta gabace ta mai lamba ta (2) a bangaren hagu, sannan da wacce ke zuwa bayanta mai lamta ta (4), in akwai Kenan.  In kuma ita ce ta karshe a bangaren, to, za ka ci karo da wani sabon maudu’i ne.

Har wa yau, idan kana son ganin dukkan kasidun da wani bangare ya kunsa gaba daya, ka gangara kasan shafin gaba daya, zaka ga dukkan bangarorin.  Sai ka bi wanda kake so.  Zaka ga dukkan kasidun dake karkashinsa.  Da fatan ka gamsu.  Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Ina yi maka fatan alkhairi da fatan Allah ya kara basira, amin.  Sako daga dalibinka: Idris Ghali Abdu, Bich Kano: Idrisabdughali@yahoo.com

Wa alaikumus salam, Malam Idris barka dai.  Ina godiya matuka da wannan sako naka na fatan alheri.  Allah saka maka da mafificin alheri, ya kuma inganta rayuwarmu baki daya.  Na gode matuka.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.