Sakonnin Masu Karatu (2018) (5)

Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

240

Salamun alaikum Baban Sadik don Allah a mini karin bayani kan yadda kafafen sada zumunta irin su Facebook da Twitter suke samun kudaden shiga, ganin yadda bude irin wadannan kafafen kyauta ne. Sannan ina son karin bayani akan tsarin da kamfanin Youtube yake bayarwa ga wadanda suke sanya fina-finai ko wani talle a kan shafin domin basu wani ihsani. Ta yaya ake iya samun wannan damar ne kuma ta yaya wannan ihsani na kudi ke kaiwa ga mutum?  Daga Bello Isiyaku Birin Fulani Jihar Gombe: ishiyakubello@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Bello.  Wadannan kafafe dai na samun kudaden shiga ne ta hanyoyi da yawa.  Shahararru daga cikinsu su ne: tallace-tallace da suke karba daga wajen kamfanonin kasuwanci dake kasashen duniya daban-daban, da kuma sayar da kididdiga ko alkalumar adadin masu rajista dasu, da kuma bayar da shawarwari ga kamfanonin kasuwanci ko hukumomin gwamnatocin wasu kasashe a duniya, sai kuma manhajoji da suke kirkira wadanda ake iya amfani dasu wajen ci gaban kasuwanci da sadarwa.  Galibi suna sayar da wadannan manhajoji ga manyan kamfanonin duniya na kasuwanci wadanda suka kasaita. 

Wadannan hajoji da na lissafa kadan ne cikin abubuwan da suke yi wajen samun kudaden shiga.  Kuma hakan ya danganci kamfanin sadarwa.  Ma’ana bat sari iri daya suke amfani dashi ba.  Misali, bayan kamfanin Twitter da Facebook, hatta Google, da Yahoo!, da Microsoft, da Baidu (na kasar Sin), duk suna da nasu tsare-tsare.

A bangaren Facebook suna dora tallace-tallace na hajojin kamfanoni.  Idan ka hau shafinka a bangaren sakonnin jama’a (News Feed), za ka ga wasu sakonni cikin hotuna ko bidiyo ko rubutattun sakonni na wasu kamfanoni ko hukumomin gwamnati, ba mutane ba, wadanda kuma ba abokanka bane.  Baka ma sansu ba.  Idan ka lura a gefen hotunan ko sakonnin, ko a sama da su kadan, za ka an rubuta: “Ad” ko “Advertisement”; alamar cewa tallace-tallace ne.  Bayan wannan, Facebook na iya tallata maka sakonnin da kake rubutawa a shafinka (Facebook Page), wanda ka bude don yada wata manufarka ta siyasa ko kasuwanci.  Haka idan karantarwa kake yi, duk kana iya baiwa Facebook talla su tallata maka abin da kake yadawa na manufa.  Kusan dukkan bankunan Najeriya suna baiwa Facebook tallata ta hanyoyi daban-daban. 

Sannan hatta adadin masu rajista a Facebook, da yawan shafukan da suke budewa, da yawan sakonnin da suke zubawa a shafukansu, da kuma yawan abokansu, da kasa ko garin da suke zama, da abubuwan da suka rubutawa na tarihinsu, da kuma yawan “Like” da suke matsawa a kan kowane sako suka gani ko karanta, dukkan wadannan abubuwa da na zayyana, hajoji ne ga kamfanin Facebook kuma iya “sayar” da su ga kamfanoni a yanayi da farashin da baka taba tunani ba.  Abin sirri ne.

A bangaren Twitter ma suna da wannan tsari, sai dai tsarinsu ya sha bamban da na Facebook.  Sannan Facebook ya fi Twitter yawan jama’a, da shahara, da kuma tsabar dukiya.  Domin alkaluman bayanai na nuna cewa adadin masu dora tallace-tallace ma a Twitter ya ragu matuka, musamman tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016.  Wannan yasa har masu kamfanin suka fara yunkurin sayar da kamfanin ma gaba daya, amma hakan bai yiwu ba a karshe.

Daga cikin manyan kamfanonin sadarwa da suka fi kowa yawan dora tallace-tallace a duniya akwai Google da Microsoft da kuma Yahoo!.  Wadannan su ne iyaye a fannin karba da bayar da tallace-tallace a shafuka, saboda damar da suke da ita na sanya tallace-tallacen a shafukan neman bayanai da mutane ke amfani dasu a kowane dakika na lokacin duniyar nan.

Dangane da tambayarka ta biyu kan tsarin da Youtube ke bayarwa na sanya tallace-tallace da abin hasafi da yake bayarwa ga wadanda suka yi rajista da wannan tsari, lallai akwai ka’idoji da suka tanada da kuma sharudda da suka gindaya mai son yin hakan.  Da farko dai tukun, ya kamata ka san cewa shafin Youtube dai shafi ne da kamfanin “Alphabet Inc.” (kamfanin Google) ya mallaka.  Kuma shafi ne dake dauke da sakonnin bidiyo, wanda jama’a ke zubawa ko lodawa.  Su abin da suka tanada shi ne mahalli da ma’adana.  Amma hakikanin bidiyoyin da ke kan wannan shafi duk jama’a ne ke zubasu.  An kiyasta cewa a duk minti daya, ana kallon sakonnin bidiyo da tsawonsu ya kai sa’o’i biliyan uku!  Ma’ana, yawan bidiyon da ake kallo a duk minti guda, idan aka tara tsawon lokacin da sakonnin bidiyon suka dauka ana kallonsu, ya kai awanni ko sa’o’i biliyan uku.

Shafin Youtube na karban tallace-tallace daga kamfanoni kamar sauran shafukan da bayanansu ya gabata.  Sannan yana dora wadannan sakonni ne ga masu kallon bidiyon dake shafin, ta hanyoyi daban-daban.  Hanya ta farko ita ce ta amfani da tsofa tallace-tallacen bidiyon a farkon bidiyon da jama’a ke kallo.  Wannan tsari shi ake kira “Embedded Video Ads.”  Da zarar ka budo bidiyo za ka kalla, za ka fara cin karo da talla ne na tsawon dakiku biyar (5 seconds).  Daga nan sai a isar da kai ga bidiyon da ka budo.  Haka idan bidiyon na da tsayi, bayan wasu lokuta ma zaka sake cin karo talla.  Haka dai har ka gama kallonka.  Manufa dai ita ce, idan ka matsa kowanne daga cikin bidiyon dake dauke da tallan nan, to, shafin Youtube yaci kudin kamfanin da ya bashi tallan.  Sannan akwai tsarin loda tallace-tallace a tsakanin gungun sakonnin bidiyo da ke shafin, a gefensu, ko a saman jadawalinsu, ko kuma a tsakaninsu.  Idan ka lura sosai, a gefen wasu bidiyon za ka ga wata alama mai launin rawaya (Yellow), dauke da Kalmar “Ad”.  Wannan ke nuna wannan bidiyon na talla ne. Idan ka kalla, shafin Youtube yaci kudin mai tallar.

- Adv -

Bayan haka, shafin Youtube ya kasu kasha uku ne.  Akwai babban shafi, na kowa da kowa Kenan.  Inda za ka iya kallon bidiyo kyauta, amma masu dauke da tallace-tallace, kamar bayanin da nayi a sama Kenan.  Sai kuma bangare na biyu, mai suna: “Youtube Red”, wanda ke dauke da nau’ukan bidiyo marasa tallace-tallace a ciki ko harabarsu.  Shi wannan bangare ba kowa ke iya shiga ba sai wanda yayi rajista kuma ya biya kudi. Idan kana bukata, a duk wata za ka rika biyan dala goma ne ($10), kwatankwacin Naira dari uku da hamsin Kenan (N350), a kalla.  Sai bangare na karshe, wanda ke dauke da nau’ukan bidiyo ne daga tashoshin talabijin na duniya, shahararru.  A wannan tsari ko sashe, dukkan shirye-shiryensu ne suke watsawa, amma ta hanyar tashar Youtube.  Wannan shi suke kira: “Youtube TV”, kuma shi ma na kudi ne; ya ma fi “Youtube Red” tsada.  Iya kudinka iya shagalinka.

Nau’ukan bidiyon dake shafin Youtube sun kunshi wadanda jama’a ke lodawa don kashin kansu, da wadanda tashoshin talabijin suke lodawa, da wadanda kamfanonin fina-finai ke lodawa, da dai sauransu.  Har wa yau, akwai nau’ukan bidiyo masu dauke da wakoki na shahararrun (tantiran) mawakan duniya.  Duk a ciki.  Wasu masana na ganin cewa duk wani ilimi da kake son koyonsa, idan ka hau shafin Youtube, akwai tabbacin wani ya taba yin bidiyo yayi bayani a kansa.

Bayan tallace-tallace da suke dorawa na kamfanonin kasuwanci, shafin Youtube na baiwa masu mu’amala dashi damar dora tallace-tallace a kan bidiyon da suke lodawa, don su ma su samu wani abin hasafi.  Wannan tsari shi ake kira: “Youtube Monetization Programme.”  Tsari ne dake baka damar samun kudaden shiga ta hanyar sakonnin bidiyo da kake lodawa a tasharka ta Youtube.  Sharuddan dai su ne kamar haka:

Na farko dai dole ne ka mallaki tasha (Channel) a shafin Youtube.  Hakan kuwa zai yiwu ne ta hanyar yin rajista a shafin.  Shi kuma rajista na yiwuwa ne ta hanyar adireshin Imel na kamfanin Google, wato Gmail Kenan.  Idan kana da adireshin Gmail, to, kana iya hawa shafin sai ka matsa: “Sign In”, inda zaka shigar da suna da Kalmar sirrin Imel dinka. 

Abu na biyu shi ne mallakar tasha, wato: “Channel” kenan.  Ka kiyasta “tasha” a matsayin “Profile Page” dinka ne a shafin Facebook.  Nan ne ke dauke da yawan tashoshin da kayi rajista (Subcribe) dasu da sauran tsare-tsaren da suka shafi sunan tashar, da sauran bayanai.  A nan ne har wa yau kake da dakin shirye-shiryenka, wato: “Studio”, inda ta nan zaka iya loda bidiyon da kayi, ka gyara su, da canza wa shafinsa siffa da dai sauran hanyoyin kayatarwa.

Abu na uku shi ne yin rajista don karbar tallace-tallace daga shafin Youtube.  Wannan tsari, kamar yadda na ayyana a sama, shi ake kira: “Youtube Monetization Programme.”  Idan ka hau tasharka za ka alama mai dauke da wannan tsari.  Sai ka matsa don yin rajista.  Yin rajista na da sharudda.  Na farko daga cikin ka’idar rajista sai ka mallaki rajista da tsarin “Google Adsense,” wanda shi ne asalin tsarin dake lura da biyan masu baiwa Google damar dora tallace-tallace a shafukansu na Intanet.  Daga can tashar naka zasu cillo ka shafin Google Adsense, don kayi rajista.  Idan k agama, za a koma dakai tasharka ta Youtube, don ci gaba da maka tambayoyi.

Abu na hudu shi ne, bayan ka gama rajista, ba nan take za a fara dora talla a kan sakonnin bidiyo dinka ba.  Dole sai ka mallaki adadin masu rajista a tasharka sun dubu daya (1,000 subscribers).  Sharadi na biyu kuma, dole ne ya zama an kalli sakonnin bidiyo a shafinka wanda tsawon lokacinsa ya kai sa’o’i dari hudu (400 hours).

Abu na karshe, shi ne, shafin Youtube bai yarda ba ka dora bidiyo masu da dauke da tsantsar batsa, ko cin mutuncin wata al’umma ko addini kai tsaye, ko kuma nuna tsana ga wani jinsi, ko kuma masu dauke da hanyoyin koyar da miyagun ayyuka ko satar yara ba, misali.

Da zarar ka cika wadannan ka’idoji da sharudda, nan take za a fara dora sakonnin tallace-tallace a kan bidiyon da kake loda, don baiwa masu kallonsu damar kaiwa gare su.  Akwai iya adadin da ake la’akari dashi kafin a fara biyanka.  Sauran bayanai kuma sai in ka shiga cikin tsarin tsundum.  Allah sa a dace, kuma da fatan ka gamsu wannan gajeren bayani. 

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.