Sakonnin Masu Karatu (2018) (4)

Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

402

Salam Baban Sadik da fatan kana cikin koshin lafiya. Allah yasa haka, kuma Allah yasa mu dace. Daga Hashim Adam Bakin Lahadi, Jahun LGA, Jigawa State, 07036441408.

Wa alaikumus salam, ina lafiya kalau Malam Adamu.  Na gode.  Allah saka da alheri ya kuma bar zumunci.  Na gode sosai.


Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata a gareka Abban Sadik, tare da daukacin masu bibiyar wannan fili, da fatan aiki yana tafiya cikin koshin lafiya.  Abban Sadik a kwanakin baya shafina na Facebook idan aka aiko mini sako ko aka mini ta’aliki ko “like” ko “Post”, duk ina samun sakon tes a layina; ko da ba na kan layi.  Amma yanzu sai na hau shafina nake ganin abin da yake faruwa a shafina.  Matsalar layina ne ko shafina. Ina maka fatan alhairi a dukkan al’amuranka. Allah yayi maka jagora da mu baki daya. Naka Abdullahi B. Anka,  Zamfara: 08060809091

Wa alaikumus salam, barka dai takwarana.  Wannan ke nuna akwai abin da ya canza kenan.  In har baza ka iya tuna sadda ka canza wannan tsari a bangaren “Settings” din shafinka ba, kuma babu wani wanda ke hawa shafin sai kai kadai, ta yiwu daga sababbin tsare-tsaren da kamfanin Facebook ke samarwa ne a kullum.

Akwai tsare-tsare na kariya da hukumar Facebook ke samarwa tare da dabbaka su a dandalin baki daya.  Sai kana lura za ka iya ganewa.  Duk da haka, idan kana son gyarawa abu ne mai sauki.  Kaje bangaren “Settings”, ka gangara “Mobile”, sai ka zabi tsarin da sake baka damar karban sakonni kan dukkan abin da ke faruwa a shafinka.  Sai dai fa, kamar yadda ka sani, in dai kana da jama’a sosai, zaka ta samun sakonni ne kai tsaye ba kakkautawa.

Allah sa a dace, amin.


Assalama alaikum da fatan kana lafiya. Gaskiya muna jin dadin aikinka, Allah ya kara basira. Bayan haka, don Allah ina so kayi min bayani akan: “DropBox”; yaya yake? Kuma yaya ake amfani dashi, da kuma yadda ake budeshi?  Kuma akwai wasu manhajoji makamantansa ne?

Wa alaikumus salam, barka dai.  Kalmar ‘DropBox’ manhaja ce da ake amfani da ita wajen adana bayanai a Intanet, da karban sakonnin kasidu ko makaloli masu nauyi, da kuma tsara mu’amala tsakaninka da mutane da dama dake aiki kan wani bincike na musamman da ya shafi rubutu.

Misali, kana iya amfani da tsarin “DropBox” idan wani ya aiko maka kasida ka masa bita, ko littafi da yake rubuta, ko kuma idan kuna aikin rubuta wani littafi ko wani bincike na ilimi kamar ku biyar ko sama da haka.  Kowannenku zai yi rajista, sannan ya saukar da manhajar a kan kwamfuta ko wayarsa ta salula.  Wannan manhaja dai tana dauke da jaka ko burganin adana bayanai ne, wato: “Folder”.  A cikin wannan rigiza za ka jefa kasida ko rubutun ko bayanan da kuke aiki a kai.  A duk sadda ka aiwatar da wasu canje canje, sai ka jefa kasidar ko asalin jakar bayanin a wannan rigiza.  Nan take wanda kake aikin tare da shi ko dasu zasu samu sako cewa ka aiwatar da wasu sauye sauye a kasidar.  Idan suka bude suka karanta, su ma suka aiwatar da sauye-sauye, nan take kai ma za ka samu sako cewa sun yi sauyi.  Haka dai za ku ci gaba da yi hark u gama.

Fa’idar da ke tattare da tsarin ‘DropBox’ dai shi ne, samun damar aiki cikin tsari.  Sannan ga tsaro ga bayanai.  Domin idan kwamfutarka ta samu matsala komai ya goge, da zarar ka je shafin “DropBox” a kan wayarka ko wata kwamfuta, za ka samu bayananka, domin duk da cewa manhajar na dauke kan waya ko kwamfutarka ne, sai dai hakikanin bayanan ba a nan suke ba; makwafinsu ne kawai.  Bayanan sunan kan kwamfutocin kamfanin “DropBox” a wata uwa duniya.  Kana hawa za ka same su cikin cif-cif.

Dangane da ko akwai wasu manhajoji makamantan “DropBox”?  Sosai ma kuwa.  Akwai “Google Drive” na kamfanin Google.  Sannan akwai “One Drive” wacce ke kan dauke kan babbar manhajar kwamfuta na “Windows”, domin kamfanin Microsoft ne ya gina ta.  Idan kana da adireshin Imel na Gmail, ko adireshin Hotmail na kamfanin Microsoft, to, kai tsaye ka mallaki “Google Drive” da kuma “One Drive”.  Bayan wadannan, akwai wasu masu dimbin yawa wadanda suka kebanci wasu ayyuka na musamman.  Misali, idan kai maginin manhaja ne, wato: “Programmer” ko “Developer”, kana iya amfani da shafin “GitHub” don aiwatar da aiki tsari makamancin wannan ko ma wanda ya fi shi.

- Adv -

Wannan kadan ne cikin abin da za a iya fada kan DropBox.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, ni sunana Hamza, daga Toro, jihar Bauchi. Baban Sadik wayata ce ta samu matsala; Service ya dauke gaba daya.  Na kai gyara an kwance ba a ga matsala ba.  Shin, ko akwai wata shawara. Daga Bar. Hamza Tilde

Wa alaikumus salam, barka dai.  A gaskiya bazan iya sanin hakikanin abin da ke damunta ba, musamman ganin cewa ka kai wa masu gyara amma ba abin da ya canza.  Kana iya canza mai gyara, domin masu gyara suna suka canza.  Idan kuma za ka iya, kayi “Resetting” wayar ko kace a matsa filashin.  Wannan zai mayar da ita baya kamar yadda aka kera ta a farkon lamari.  Da fatan ka gamsu.


Salamun alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Kai da jama’arka, amin. Wato na dade ina tare daku saboda ina sayan jaridar aminiya mai albarka tun daga watan biyar na shekarar 2014. Sannan nakan yi kokari wajen ganin na karanta abin da ke cikin jaridar gaba daya.  Sai dai na fi mayar da hankali wajen Baban Sadik da Gizago da Duniyar Ma’aurata da Kiwon Lafiya na Dokta Auwal Bala, da Tauhidi Ginshikin Musulunci da dai duk wani shafi mai kayatarwa. Ka huta lafiya.

Wa alaikumus salam, barka dai kuma muna godiya matuka da yadda lazimtar karatun shafukan AMINIYA.  Wannan ke nuna tsananin himmarka da sha’awarka ga irin bayanan da ake dorawa a shafukan jaridar.  Da fatan za ka ci gaba da kasancewa tare damu a kullum.  Mun gode matuka.  Allah bar zumunci.


Assalamu alaikum mai gidana Baban Sadik, Allah ya kara basira kuma da fatan kana lafiya. Wallahi karatun shafinka a jaridar AMINIYA ya kaini har na bi ka a Duniyar Computer. Allah dai ya biya ka. Na gode.  Nine:  Muhammadu Sani Galadima:  08024080026

Wa alaikumus salam Malam Muhammad.  Muna godiya da wannan kebantacciyar kauna garemu.  Allah bar zumunci ya kuma saka da alheri, amin.


Salamun alaikum, da fatan alheri a garemu baki daya. Tambayata ita ce: ina son in bude shafin ‘Facebook’ ne a wayata, amma idan na fara shigar da bayanai, bayan na rubuta lambar wayata sai suce in rubuta ranar haihuwata.  To, idan na rubuta na aika sai ace bai yi dai dai ba su sake dawo dani baya to yaya zanyi?  Na gode.  Sako daga Tasiu Auwal Hotoro, Kano: 08146263679

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Tasi’u.  Daga bayananka, ta yiwu baka shigar da bayanan da ake bukata ko tsammani bane.  Misali, watakila wajen shigar da shekarar haihuwarka baka zabi shekarar ba, sai ka barshi a shekarar da ake ciki (2017), wanda hakan zai sa a dauka kamar a wannan shekarar aka haifeka.  In kuwa haka ne, to, baka cancanci bude shafi a Facebook ba.  Domin daga masu shekaru 13 zuwa sama suke da damar bude shafi a dandalin.

Zai kuma iya zama wani dalili ne daban wanda baka lura ba balle ka hakaito mana sakon da aka turo maka don sanar da kai dalili ko dalilan da suka sa aka ki ko kasa baka damar budewa. 

Don haka, kana iya komawa, sai kabi dukkan bangarorin da ake bukatar bayananka, kowanne ka tabbata hakikanin abin da aka so ne ka shigar.  Da haka, za a baka damar budewa shafi naka na kanka, ba tare da wata matsala ba.  Ina maka fatan alheri da dacewa.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.