Kimiyyar Sararin Samaniya a Sawwake (1)

Masu karatu, cikin yardar Allah, yau za mu fara tunkudo muku littafin Dakta Adnan Abdulhamid na Kwalejin Ilmi da ke Kano, malami a fannin Ilmin Kasa (Geography). Wannan littafi mai take: “Why Astronomy? –  Personal Experience of a Muslim Geographer,” littafi ne da marubucin ya rubuta tarihin gwagwarmayar da ya sha don ganin ya karanta fannin Ilmin Sararin Samaniya, wato “Astronomy,” da irin fahimtarsa da ta addini, kan abin da ya shafi wannan fanni. Na nemi izninsa don fassara wannan littafi saboda bugawa a wannan shafi, ya kuma amince.  Don haka za mu fara tunkudo littafin daga yau.  Muna mika godiyarmu ga Dakta Yusuf Adamu na Jami’ar Bayero, wanda ya taimaka wajen sada mu da marubucin wannan littafi.  A sha karatu lafiya.

1,636

BABI NA DAYA – Mabudin Kunnuwa

Tun ina yaro dan karami nake sha’awan kwanciya rigingine a kasa, cikin duhun daren karkara irin ta Afirka, ina lura da taurarin da ke warwatse suna ta kyalli a cikin sama.   Wasu lokuta in yi ta tunanin ina cewa, “ina ma a ce ni tsuntsu ne in rika tashi ina shawagi a sama, in ma ta kama, in samu karin fika-fikai da za su riskar da ni ga tauraro mafi kusanci da ni!”  Na tuna sa’adda nake dan shekaru shida ko bakwai, na taba lura da wani tauraro da ya keto daga sama, mai dogon wutsiya, sai kace wata doguwar sanda.  “Me ye wannan kuma?”, na tambaya.  Sai gwaggo na tayi caraf da amsa: “wata tauraruwa ce mai wutsiya, kuma hakan na nufin wani mummunar abu zai faru kenan”.  Da na dage da tambaya kan wannan tauraruwa, sai aka ce mini wani abu ne mummuna zai faru a duniya.  Wannan lamari ya faru ne cikin shekarar 1966.  Daidai wannan lokaci ne aka kashe Sardauna Firimiyar Jihar Arewa na farko, tare da Firanministan Najeriya, Sa Abubakar Tafawa Balewa.  Daga nan kuma sai Yakin Basasa ya barke nan take.

- Adv -

Ban sani ba, ashe ranar 20 ga watan Yuli na shekarar 1969 an harba kumbo Apollo 11 zuwa duniyar wata.  Wannan shi ne karon farko da kasar Amurka tayi nasara kan wannan aiki da Neil Armstrong ya shugabanta.  Daidai wannan lokaci ne har wa yau, aka yi wa shugaba John F. Kennedy kisan gilla.  Tun sannan na rike sunan kumbo Apollo 11 a bakina, ba tare da sanin abin da hakan ke nufi ba.  Na yi ta kwaikwayon marigayi Mamman Shata cikin wakar da yayi wa kumbo Apollo 11, duk sa’adda aka sanya wakar a gidan rediyo.  Alhaji Mamman Shata ya yi ta yabon wadanda ke cikin wannan kumbo da ya fara zuwa duniyar wata.  Daga baya, wajen shekarun 1970s, sai ga Muhammad Gawo daga Jumhuriyar Nijar da shahararriyar wakarsa mai sabanin ra’ayi kan tafiyar da Apollo 11 yayi zuwa duniyar wata.  Wakar Muhammad Gawo ta yi tasiri matuka wajen sauya wa mutane tunani, inda har wasu ke tunanin wannan tafiyar da kumbo Apollo 11 yayi ba gaskiya bace.  Kai, har yanzu cikin masana akwai masu shakkar ingancin labaran da ke tabbatar da wannan tafiya ta Apollo 11.

A kullum na kan nemi gamsasshen bayani kan fasarar duk abin da na gani a sararin samaniya.  Musulmi kan yi amfani da taurari guda uku da ke jere a gabas-maso-yammacin duniya ne don gano alkibla.  Haka tauraron nan mai suna Gamzaki da ke fitowa a duk asuba – tsakanin karfe hudu zuwa biyar na safe – bayyanarsa alama ce da ke nuna lokacin sallar asuba ya shigo.  Jinjirin wata, tare da makwabciyarsa Zarah mai kyalli, da kuma taurarin da ake cillo su cikin dare dauke da tartsatsin haske a sararin samaniya, duk suna cikin abubuwan da mutanen karkaranmu ke lura da su.

Na yi tambayoyi masu yawa lokacin yarinta na. Amma ba na samun amsoshin da ke gamsar da ni.  Sau tari sai gwaggo na ta rika kwaba na da kalmar “idon matambayi,” wanda a fahimta ta hakan na nufin “Yi shiru, ka cika surutu!”  Idan aka yi sa’a mahaifina yana nan, sai ya ce musu “Ku barshi yayi tambaya mana.”  Na kan so samun gamsassun hujjoji tare da amsar duk abin da na tambaya.  Misali, na taba tambayar wani dan uwana kan wani gungun taurari da nake gani a sama, sai kawai ya ce mini, “Kaza ce da ‘ya’yanta a kewaye”.  Sai ya sake nuna mini wani gungun taurarin, ya ce, “Wadancan kuma garken shanu ne.”  Sai nayi ta mamakin ta yaya kaji ko shanu za su iya haurawa zuwa wannan wuri mai nisa haka?  Me yasa wadannan taurari suke yin kyalli?  Da dai sauran tambayoyi makamantansu.

- Adv -

You might also like
3 Comments
  1. Abdulmalik hassan danmoyi says

    don Allah Amsa

    1. Baban Sadik says

      Malam yahaya kayi hakuri. Abin da ka bukata abu ne mai matukar hadari. Amma zan samu lokaci inyi rubutu a kan haka, sannan zan maka cikakken bayani kan hakan. Na gode

      — Baban Sadik

  2. Abdulmalik says

    Muna godiya Allah yasaka da Alheri

Leave A Reply

Your email address will not be published.