Shahararrun Kamfanonin Wayar Salula a Duniya (1)

Kashi na biyar cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

469

Shimfida

A yau kuma zamu bude wani sabon faifai don ci gaba da bayanai kan wayar salula da tsarinta, da tasirinta wajen habaka sadarwa a duniya baki daya.  Daga cikin bayanan da zasu taimaka wa mai karatu fahimtar wannan tasiri kuwa, akwai fahimtar yadda kamfanonin wayar salula suka faro, da yadda suka habaka, da kuma tsarinsu wajen kera wadannan kayakkin fasahar sadarwa.  Hakan na da muhimmanci, musamman ma idan muka yi la’akari da cewa, duk da yawansu, kowanne daga ciki wayoyin na dauke ne da tsari na musamman da kamfani ya bi wajen kera shi.  Don haka muka shigar da wannan sashe, don yin gajerun bayanai na musamman kan shahararrun kamfanonin wayar salula a duniya.  Amma kafin mu yi nisa, zai dace mu fara kawo bayani kan asali da tarihin Hukumar Lura da Harkar Sadarwar Tarho ta Duniya, wato International Telecommunication Union, ko kuma ITU a gajarce – domin ita ce uwa wajen harkar sadarwar wayar tarho a duniya.


International Telecommunication Union (ITU)

An kafa wannan hukuma ta ITU ne tun a ranar 17 ga watan Mayu, shekarar 1865, wato shekaru kusan dari da arba’in da biyar kenan yanzu.  Ita ce daya cikin kungiyoyi bigu da suka fi kowace kungiya ko hukuma dadewa a duniya.  Dayan hukumar ita ce The Rhine Commission.  Hedikwatan wannan hukuma ta ITU dai yana birnin Geneva ne na kasar Suwizaland da ke nahiyar Turai a halin yanzu.  Kuma reshe ce cikin rassan Majalisar Dinkin Duniya, wato United Nations (UN).

Babbar manufar da tasa aka kafa wannan hukuma dai shi ne lura da kuma samar da ka’idojin sadarwa ta wayar tarho da kuma siginar rediyo a duk nahiyoyin duniya.  Bayan haka, hakkinta ne lura da Tafarkin Sadarwar Siginar Rediyo (Radio Spectrum) a tsarin sadarwa, tare da samar da Tsarin Zumuncin Sadarwa (Radio Interconnectivity) a tsakanin kasashe.  Wannan tasa kake iya buga waya daga kasarka zuwa wata kasa dabam, ba tare da sadarwar ta yanke ba.  A takaice dai, dukkan wasu ka’idoji da ke sawwake sadarwa na wayar tarho da kuma tsarin yada labarai ta rediyo, Hukumar ITU ne ke kirkira da kuma lura da su.

Wannan ba ya nufin babu wasu hukumomi na kasashe da ke samar da ka’idojin sadarwa a kasashe ko nahiyoyinsu, a a.  Akwai ire-iren wadannan hukumomi a kasashe dabam-daban, ko nahiyoyi, masu lura da yanayin kasashe ko nahiyarsu, don samar da ka’iadojin sadarwar da suka dace dasu.  Amma duk da haka, dole ne wadannan ka’idoji da suke samarwa ko kirkira, su dace da gamammun ka’idojin da hukumar  ITU ta gindaya.

Wannan hukuma ta ITU na da rassa guda uku masu zartar da dukkan kudurorin da ta yanke kan harkar sadarwa a duniya. Reshen farko shi ne The Telecommunication Standard Sector (ITU-T), wanda hakkinsa ne samar da ka’idoji tare da daidai tsarin sadarwar wayar tarho a duniya.  Wadannan ka’idoji dai sun shafi tsarin sadarwa ne a tsakanin kasashe, na wayar kan tebur (Landline) da wayar salula (Mobile phones), da kuma hanyoyin kera su, don tabbatar da sadarwa mai inganci a tsakanin kamfanonin sadarwa ko kasashen duniya.  Sai reshe na biyu mai suna The Radio Communication Union (ITU-R), mai samar da ka’idojin sadarwa ta rediyo a tsakanin kasashen duniya da kuma tashoshin rediyo da ke wadannan kasashe.

Wadannan ka’idoji sun shafi na’urorin da ake amfani dasu, da tsarin sadarwar, da kuma yadda tasoshin rediyo zasu tafiyar da wadannan tsare-tsare ba tare da matsala ba.  Reshe na karshe kuma shi ne wanda hukumar ta kira The Telecommunication Development Sector (ITU-D), wanda aikinsa shi ne habakawa tare da fadada harkar sadarwa a kasashen duniya.

- Adv -

Bayan wadannan rassa, hukumar na da Babban Sakatare (Secretary-General) da ke shugabantarta, a tsawon dukkan shekaru hudu.  Tana da mambobi na kasashen duniya guda dari da casa’in da daya; a takaice dai dukkan mambobin Majalisar Dinkin Duniya mambobinta ne, in ka kebe kasashen Taiwan, da Timor ta Gabas (East Timor), da tsibirin Palau, da kuma Hukumar Palasdinawa da ke Gabas-ta-tsakiya.  Don Karin bayani, mai karatu na iya ziyartar gidan yanar sadarwar wannan hukuma a http://www.itu.int.

Kamfanin Nokia Corporation

Kamfanin kera wayar salula ya Nokia ya samo asali ne shi ma tun shekarar 1865, wato shekaru dari da arba’in da biyar kenan.  Asalin kamfanin dai yana kera gasassun robobi ne, wato Plastics, da manyan takalman ruwa, wato Rubber Boots.  Daga baya masu kamfanin suka fadada sina’ar, inda suka samar da reshen kera kayayyakin lantarki.  Wannan suna da kamfanin ke amfani da shi, wato “Nokia”, ya samo asali ne daga sunan kauyen da aka bude kamfanin a ciki, wato “Nokianvirta”, wanda ke kusa da babban birnin kasar Finland da ake kira Helsinki yanzu.  Bayan haka, shi kanshi garin ya samo sunan “Nokia” a farkon sunansa ne sanadiyyar wani rafi da ke bayan garin, wanda ya tara wasu bakaken tsuntsaye kanana masu gashi lallausa.

Wadannan tsuntsaye, kamar yadda tarihin kamfanin Nokia Corporation ya tabbatar a yau, su ake kira da suna “Nokia” a harshen mutanen kasar Finland.  Don haka kamfanin ya dauki wannan suna shahararre, ya baiwa kamfaninsa.  A halin yanzu Hedikwatar kamfanin na wani gari ne mai suna Keilaniemi da ke Lardin Espoo, gab da birnin Helsinki.

Wannan kamfani ya ci gaba da kera takalman danko da kayayyakin lantarki, da kuma wayoyin tarho irin na da, har zuwa shekarar 1990, lokacin da aka raba kamfanin gida biyu, don ware fannin da ke kera wayoyin tarho zalla, da kuma sanya masa suna Nokia Corporation, kamar yadda yake yanzu. Wannan tasa kamfanin ya samu lokaci na musamman don gudanar da bincike kan kera wayoyin tarho na gida da na ofis da kuma na tafi-da-gidanka, wato Mobile Phones.  Bayan haka, kamfanin na kera na’urar MP3, masu dauke da ma’adanai don jiyar da wakoki ko sauti.

A halin yanzu dai kamfanin Nokia Corporation shi ne na daya a sahun kamfanoni masu kera wayoyin salula masu inganci, kuma shi ne ya fi kowane kamfanin kera wayar salula ciniki a duk shekara.  Wannan kamfani dai ya fara samun wannan shahara ne tun shekarar 1998, lokacin da yayi wa kamfanin Motorola fintinkau wajen yawan wayoyin salular da ya sayar a shekarar.  Tun sannan kuma ya rike wannan kambi.

Kamfanin Nokia Corporation dai bai shahara wajen kera wayoyin salula kadai ba, a a, ya shahara ne har wa yau wajen samar da wayoyi masu inganci, da dadin sha’ani wajen sadarwa.  Galibin wayoyinsa basu damu da kyale-kyale ba ko kadan.  Kuma suna iya jure yanayi dabam-daban ba tare da sun lalace ba.  Duk sauran kamfanonin sadarwa da kuma masu amfani da wayoyinsa sun sheda haka.  Ya samar da ka’idoji da kuma tsarin sadarwa masu inganci a dukkan wayoyinsa.  Cikin makon da ya gabata ne kamfanin ya sanar da cewa zai fara kera wayoyin salula masu katin SIM guda biyu, wato Dual SIM Phones, kafin watan Afrailun shekarar 2010

A halin yanzu dai yana da ma’aikata guda dubu dari da ashirin da takwas da dari hudu da arba’in da biyar (128,445) da ke masa aiki a kasashe dari da ashirin da ke warwatse a duniya.  Duk mai neman Karin bayani na iya ziyartar gidan yanar sadarwar kamfanin a http://www.nokia.com.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.