Sakonnin Masu Karatu (2017) (8)

Ga wasu daga cikin sakonninku da kuka aiko. A sha karatu lafiya.

97

Cikin yardar Allah a wannan mako zamu duba jakar wasikunku ta Imel, don amsa wasu cikin sakonninku.  Daga wannan mako zuwa makonni biyu bayan Sallah zamu shagaltu da sakonninku ne.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu da’iman. 

Ina kara sanarwa ga masu aiko sakonnin neman kasidu na musamman cewa a halin yanzu na gina shafin Intanet mai take: “TASKAR BABAN SADIK”, wanda za a same shi a:  www.babansadik.com, don karantawa tare da saukar da duk kasidar da ake bukata, kyauta.  Don haka, daga yanzu na daina aiko kasidu ta Imel sai dai aje shafin a dauko.  Wannan, a ganina, shi yafi sauki ga mai karatu.

Da fatan za a ci gaba da hakuri dani.  In kuma rokon Allah ya karbi ayyukanmu cikin wannan wata mai alfarma.  Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadik, ni mai bibiyar shafinka ne a Jaridar Aminiya.  Ina nan ina ta nazari akan wannan makalar taka mai take:  “Mu Koyi Programming”.   Wani lokacin sai inji zan iya, wani sa’in kuma sai in sare.  To amma za mu gwada.  Allah yai mana jangora, amin.  Aminu Musa Aliyu:  aminumusaaliyu2016@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Aminu barka ka dai.  Lallai idan ana bayanin abin tare da fa’idojin dake tattare dashi sai duk mutum yaji yana tsuma.  Amma aikin kam aiki ne.  Sai dai kuma duk da haka, ba abu bane da zai gagara.  Da zai gagara da ba a samu masu yi ba balle har a rika hakaito fa’idojin dake tattare da shi.   Don haka, kamar sauran fannoni ne na ilmi, idan har mutum yana da sha’awa mai karfi kan abin, to, koyonsa bazai masa wahala ba.  Kafin a fara ne, amma da zarar an fara shikenan.

Kuma wani abin sha’awa ma shi ne, akwai zumunci mai karfi tsakanin yarukan gina manhajar kwamfuta (Programming Languages); asalinsu daya ne, tarihinsu ya samo tushe ne daga tubali guda, kuma suna da kamaimaiceceniya.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, muddin kaci nasara ka nakalci wani yare guda daya, to, kwarewa a sauran ba shi da wahala ko kadan.  Don haka, ina maka fatan alheri, kuma Allah maka jagora wajen nakaltar wannan fanni mai matukar tasiri a fannin sadarwar zamani, amin.


Assalamu alaikum barka da aiki Baban Sadik.  Dan Allah ina tambaya: wai shin idan aka goge abu daga kan Kwamfuta ko wayar hannu, ina yake tafiya?  Domin na ga ana yin “Data Recovery”, ma’ana dawo da abin da aka goge daga kan memory card? nasirukainuwahadejia1@gmail.com

Wa a alaikumus salam, barka dai Malam Nasiru.  Lallai dukkan na’urorin sadarwa masu iya taskance bayanai suna dauke ne da ma’adana ta musamman da ake kira: “Storage” da kuma mahallin haddace abubuwa mai suna: “Memory”, wato kwakwalwa kenan.  Kuma kamar yadda suke da hanyoyin da ake bi wajen shigarwa ko loda musu bayanai, wadannan na’urori (musamman kwamfuta da wayar salula) suna da hanyoyin da ake bi wajen gogewa ko share bayanan da aka zuba musu.

- Adv -

Idan aka goge bayanai daga cikin ma’adanar kwamfuta ko wayar salula, abin da wannan ke nufi shi ne an share su ne daga wuraren da aka ajiye ko taskance su a farko.  Daga nan sai a aika su wani wuri na musamman.  Wannan ya faru ne saboda kowace ma’adana ta adana bayanai tana dauke ne da gurabu da take zuba bayanai a tsarin sifili (0) da daya (1).  Wadannan gurabu su ake kira: “Sectors”, kuma suna warwatse ne a kan ma’adanar.  Iya girman ma’adanar iya yawansu da watsuwarsu.  Haka abin yake dangane da faifan CD da faifan DVD da na Garmaho, duk suna dauke ne da wadannan gurabu, wadanda asalinsu ramuka ne da kwamfuta ko wayar salula ke amfani dasu wajen taskance bayanai a tsarin sifili (0) da daya (1).  Shi yasa ma idan kan dauki faifan CD ko na DVD ka karce shi da reza ko wani abu mai kaushi har yayi zane a samansa, da zarar ka sanya a na’urar CD ko DVD sai kaga hotunan suna yayyankewa.  Dole, domin ba ta iya kaiwa ga bayanan kamar yadda aka taskance su, saboda toshewar gurabun da suke ciki.

Idan aka goge bayanai daga wata ma’adana, abin da ke faruwa shi ne, ana matsar dasu ne daga inda suke a asali, zauwa wani bigire daban da kwamfuta ba ta iya ganinsu.  Shi yasa idan ka duba ma sai ka ga babu su.  Ko nemo su kayi, sai ace maka “ba sa nan” ko ace maka “an matsar dasu daga inda suke.”  Wannan yasa ake iya samun manhajar kwamfuta ko wayar salula ta musamman wacce ke iya zakulo wadannan bayanai da aka goge a baya, don samunsu.  Amma duk da haka, yana da kyau ka san cewa idan bayanan suna da yawa, kuma an dauki tsawon lokaci da goge su, samunsu cikin sauki yana da wahala.  Idan ma za a same su, to hakan zai dauki lokaci mai tsayi ana nemansu; iya girman ma’adanar iya tsawon lokacin da za a dauka ana neman bayanan.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik.  Don Allah ina son ka taimaka mani da bayani akan yadda zan koyi ilimin sarrafa kwamfuta cikin sauki amma da turanci (English) ina godiya.  Sarkin Fulani Tsafe:  sfulani10@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Sarkin Fulani, da fatan kai ma kana lafiya.  Lallai akwai shafuka ko ince “Makarantun” koyon ilimin kwamfuta kyauta a Intanet.  Wadannan makarantu ko wurare dai sun kasu kashi-kashi; akwai na kudi, akwai na kyauta, akwai wadanda bayanan a rubuce suke – sai ka karanta – sannan akwai wadanda suke dauke da bayanan bidiyo ne tsantsa.  Sai dai wani abu kuma, galibinsu, kashi 90 cikin 100, duk da harshen Turance suke.  A wasu shafukan kuma, dole ne kayi rajista kafin ka fara daukan darasi.  Wasu shafukan na bayar da takardar shedar gama karatu, wasu kuma ba su bayarwa.  Wasu na dauke da wuraren gwaji, wasu kuma ba su da wuraren gwaji, sai dai kayi amfani da kwamfutarka.

Duk da ba dai ban san wani bangare kake son koyo ba, shafin da yafi kowanne shahara kuma yake baiwa masu bukatar koyon nau’ukan ilimi daban-daban (ba wai na kwamfuta kadai ba), shi ne shafi mai take: “Tutorials Point.”  Wannan shafi ko makaranta tana dauke ne da rubutattun darussa da suka shafi fannoni daban-daban na ilimi.   Duk wani fanni na kimiyya da kere-kere za ka iya koyonsu a wannan shafi kyauta.  Kusan dukkan fannonin ilimin kwamfuta za ka iya koyonsu a wanan shafi.  Sannan shafi ne dake koyar da kai a tsarin mataki-mataki; daga farko har zuwa karshe.  Adireshin wannan shafi dai shi ne: www.tutorialspoint.com.  Kana hawa shafin daga sama sai ka matsa: “Tutorials Library,” don zaban fannin da kake son koyo.  Ko kuma ka gangara can kasa, za ka wani dogon jadawali mai dauke da dukkan fannonin da za ka iya koyo a wannan makaranta.  Duk na nuna cewa makaratar na dauke ne da rubutattun darussa, sai dai akwai bangaren darussan cikin bidiyo, sannan akwai bangaren kwatanta abin da ka koyo, idan ilimi ne mai dauke da koyo a aikace.  Misali, idan bangaren gidan shafin yanar Intanet kake son koyo (Web Design), akwai bangaren da za ka je ka kwatanta abin da ka koya a aikace, ba sai kana da kwamfuta ta kashin kanka ba.  Kana iya samun wannan wuri a shafin farko daga sama, can bangaren dama, mai take: “Coding Background.”

Idan kana son kuma inda zaka koyo nau’ukan kwamfuta musamman yadda ake gina manhajar kwamfuta ne (Programming) ne kai tsaye, daga farko har zuwa karshe, tare da takardar shedar karatu (Certificate), duk a kyauta, sai kaje shafi mai take: “Solo Learn.”  Wannan makaranta na daga cikin makarantu dake karantar da ilimi cikin sauki, tare da hanyar kwatanta karatun, cikin sauki.  Ba ma wannan kadai ba, ana karantar dakai ne mataki-mataki, cikin tsari mai dauke da nishadantarwa da saukin fahimta.  Ba a cika ka da tarin bayanai.  Rubutattun bayanai kadan ne, sai misalai birjik.  Cikin kankanin lokaci za ka koyi ilimi mai yawa, wanda ke dauka da dabbakawa.  Idan ka gama karatun nan take za a aiko maka da takardar sheda ta adireshin Imel dinka.  Amma dole sai ka yi rajista kafin ka fara daukan darasi.  Idan nace rajista ban nufin biyan kudi.  A a.  ina nufin za ka bude “account” ne.  Idan kuma ba ka son bude wani “account”, kana iya hawa da adireshinka na “Facebook” ko “Gmail,” kai tsaye, a duk sadda ka tashi shiga.  Bayan dukkan wannan, kana iya saukar da manhajar wannan makaranta a wayarka daga cibiyar “PlayStore” na wayoyin Adroid, sai dai kuma dole ne sai kana da Intanet za ka iya hawa a kowane lokaci.  Adireshin wannan shafi yana:  www.sololearn.com.

A daya bangaren kuma, akwai shafukan koyon ilimi ta hanyar bayanan bidiyo, su ma kyauta.  Wannan na samuwa ta hanyar shafin “Youtube” na kamfanin Google.  Wannan shafi na Youtube dai wata duniyar ilimi ce, mai dauke da kusan “kowane” nau’in ilimi kake bukata ko abin da ya dangance shi.  Jakar magori ce!  Idan kana da wayar salula irin ta zamani mai iya mu’amala da fasahar Intanet, to lallai baza ka rasa samun manhajar Youtube a kan wayar ba.  Ko dai ya zama wanda wayar tazo dashi ne (musamman idan Android ce), ko kuma ka same ta a cibiyar Play Store ko Store, idan nau’in “Windows Phone” kake amfani da ita.

Idan kuma da kwamfuta kake son hawa shafin, kana iya shigar da: www.youtube.com.  Da zarar ka hau, a sama daga tsakiya akwai inda aka tanada don yin “tambaya” (Search) kan nau’in ilimi ko bayanan da kake bukata.  Kada ka mance, galibin ire-iren wadannan ilimi dai cikin harshen turanci suke.  Don haka, duk tambayar da za ka yi ta zama cikin harshen turanci ce, kan wani fanni na ilimin kwamfuta kake son koyo.  Kana tambayowa kuma za a baka amsa bila-adadin.

Wadannan su ne wadanda zan iya baka shawarar ka lazimta a halin yanzu.  Ba wai iyakansu ba kenan, a a, suna da yawa.  Aika maka dandazonsu zai rikitar da kai, har ka kasa tabbatuwa a kan guda daya.  Idan ka lazimci wadannan, ka fa’idantu, da kanka za ka nemo kari, ba sai ka sake tambayar wani ba.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
2 Comments
 1. Lawal Ibrahim says

  Muna godia maiyawa
  Amma dan allah malam baban sadiq munaso kayimana bayani akan kasidun wannan shafi akan yar da zamu saukar dashi

  1. Baban Sadik says

   Saukar da kasidu ba wahala. Idan wannan kake nufi, sai dai ka taskance shafin a wayarka. Ka matsa yatsar hannunka a kan shafi ka rike na tsawon dakika biyu ko uku, bayanai zasu bayyana. Cikinsu zaka ga “Save” ko “Bookmark”, ka zabi kowanne za a taskance maka bayanan ko kuma adireshin a kan wayarka.

   Sannan kana iya zuwa inda na tanadi kasidu masu tsayi don saukar da wanda kake so, a wannan adireshin: https://babansadik.com/dunkulallun-kasidu. Allah sa a dace, amin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.