Hanyoyin Da Kafofin Sada Zumunta Ke Samun Kudaden Shiga (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 23 ga watan Yuli, 2021.

168

Hajojin Kafafen Sada Zumunta

Hajojin kafafen sada zumunta suna da yawa, amma hajarsu ta asali ita ce tallace-tallace, wanda suke karba daga kamfanonin kasuwanci da hukumomin gwamnati a kasashe daban-daban.  Kamar yadda bayani ya gabata a makon jiya, tsarin shafukan kafafen sada zumunta shi ne samar da mahalli ga masu rajista, da tanada musu kayayyakin da zai taimaka musu wajen aiwatar da sadarwa da sauran abokansu, sannan da basu damar rubuta ra’ayoyinsu da dandanonsu a rayuwa da siyasa.  A  wannan dandali, wadannan kafafe sada zumunta sun gina wasu manhajoji ne na karkashin kasa, wadanda ke iya tantance musu rajistar a dandalin, da yawan abokan kowannensu, da irin nau’ukan bayanan da suke wallafa a shafukansu – zallar rubutu, ko sauti, ko hotuna ko bidiyo.  Wadannan manhajoji har wa yau suna iya tantance ra’ayoyin dukkan masu rajista a wadannan kafafe cikin sauki, don baiwa kamfanoninsu damar amfani da wadannan bayanai wajen karban tallace-tallace.

Manhajojin dake taimaka wa masu wadannan kafafe tantance masu tajista dasu dai an gina su ne da wasu ka’idojin gina manhajar kwamfuta, wadanda ke iya hankaltar dabi’un mutanen dake dandalin, da iya gudanar da hasashe kan abin da nan gaba zasu iya bukata na hajojin rayuwa.  Daga cikin dabarun dake kunshe cikin manhajojin dai akwai fasahar “Artificial Intelligence”, wato: “AI”, da fasahar “Machine Learning”, da kuma “Deep Learning”.  Wadannan fasahohi ne na zamani, wadanda hatta na’urorin sadarwa irin su wayar salula, da kwamfuta, da talabijin, da na’urar dafa abinci, da sauransu, duk suna dauke dasu.  Kuma su ne a baya nake kira: “Na’urori” ko “Manhajoji masu fasaha da basira.”  A yanzu ga bayani nan a takaice kan kamfanonin kafafen sada zumunta, da manhajojinsu da kuma tsarin da suke bi wajen samar da kudaden shiga.

Kamfanin Google

- Adv -

Kamfanin Google na da shafuka da manhajoji da na’urorin sadarwa sama da 100, wadanda yake amfani dasu wajen tara jama’a, da tatsar bayanansu, da kuma tallata musu hajojin kamfanonin da suka bashi talla.  Ba wannan kadai ba, an kai matsayin da kamfanin Google ya fara dillacin tallace-tallace.  Idan kana da gidan yanar sadarwa, kana iya rajista da Google. Idan ya yi nazarin gidan yanar sadarwarka yaga ya cika sharuddan da ya gindaya, zai baka tallace-tallace ka rika dorawa.  Duk wanda ya matsa wadannan tallace-tallace cikin maziyarta shafinka, akwai adadi na kudi da kamfanin zai biya ka a duk karshen wata (idan adadin kudin yakai dala 100 ko sama da haka).  Kamfanin na da tsarin tallace-tallace guda biyu ne.  Na farko shi ne: “Google AdWords”, wanda yake amfani dashi wajen karban talla daga kamfanoni, suna biyansa a iya yarjejeniyar dake tsakani.  Sai na biyu mai suna: “Google AdSense”, wanda kamfanin ke amfani dashi wajen dillacin tallace-tallace ga wasu shafukan Intanet (Websites) ko dora bidiyo a shafin Youtube.

Mafi girman hajar kamfanin Google ita ce tallace-tallace da yake karba daga wasu kamfanoni dake kasashen duniya.  Sannan yana da manyan manhajoji ko shafuka guda biyu da yake samun kudaden shiga ta hanyar tallace-tallace.  Babbar manhajarsa ita ce: “Google Search”, wato manhajar neman bayanai a Intanet.  Wannan ita ce hanya mafi girma da yake samun kudaden shiga ta hanyar tallace-tallace.  Saboda shafin “Google Search” ne shafin da aka fi ziyarta a duniya a kowace rana.  Kuma duk kalma ko  jimlar da kayi amfani da ita wajen nemo bayani, kamfanin da sanya tallace-tallace masu alaka da kasar da kake, da hajar da kake neman bayani, idan haja ce, ko da ma’anar abin da kake nema.  Sannan a galibin lokuta ma, amsoshin da ake aiko maka a shafin farko, za ka samu duk kamfanin na amfani ne da manufar kasuwanci wajen tunkudo maka su.  Wannan shi ne abin da yake kira: “Page Ranking”.  Ma’ana, wasu masu gidajen yanar sadarwa kan biya kamfanin Google kudi don ya rika nuna shafinsu a sama, a duk sadda aka tambaya wata kalma dake da alaka da abin da kamfanin yake tallatawa.  Cikin dalar Amurka biliyan 123 ($123.8 bil) da kamfanin ya samu ta hanyar tallace-tallace a shekarar 2020 da ta gabata, dala biliyan 104 ($104 bil) duk ta hanyar manhajar “Google Search” suka shigo.  Kwatankwacin naira tiriliyon 42 (N42.00 tr) kenan nudin Najeriya.  Tirkashi!

Sai hanya ta biyu, wato shafin sada zumunta na bidiyo mai suna “YouTube”, wanda mutane ke dora hotunan bidiyo da sauti a yanayin bidiyo, don amfanin masu ziyara.  Kamfanin Google na dora wadannan tallace-tallace a dukkan bidiyon da mutane suke dorawa a shafinsu.  Idan masu kallo suka matsa tallar dake kan bidiyon, za a zarce dasu ne shafin kamfanin da ya bayar da tallar.  A shekarar 2020, kamfanin Google ya samu dalar Amurka biliyan 19.76 ($19.76 bil) a matsayin kudaden shiga daga tallace-tallace a shafinsa na YouTube mai adadin maziyarta ko masu rajista biliyan 1.86 a duniya.  Kwatankwacin naira tiriliyon 8 (N8.12 tr) kenan a nairar Najeriya.

Daga bayanan da suka gabata, zai bayyana wa mai karatu irin mahimmancin da adadin jama’a ke dashi ga wadannan kamfanoni na kafafen sada zumunta a duniya.  A yayin da kake tinkahon an baka damar rajistar shafi kyauta kana zuba bidiyo, a daya bangaren kuma, kai ne hajar da kamfanin Google tallatawa a kaikaice. Tsari ne na “bani-gishiri-in-baka-manda”.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.