Sakonnin Masu Karatu (2017) (6)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

133

Assalamu alaikum Baban Sadik, me ake ciki ne game da katange wasu wayoyin hannu daga amfani da manhajar WhatsApp: Java, da kuma wasu daga cikin android?  Ko an fasa katangewar domin wa’adin da suka diba ya cika? Nasiru Kainuwa Hadejia 08100229688: knw6339@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Lallai wannan ka’ida tana nan.  Duk da cewa sanarwar farko wa’adin zai kare ne a karshen shekarar 2016, wato Disamba 31 kenan.  To amma daga baya kamfanin WhatsApp ya sake fitar da wata sanarwar da ta tsawaita wa’adin zuwa karshen watan Yuni na wannan shekara, wato: June 30, 2017.   Sakamakon wannan sanarwa na nuna cewa sai karshen wannan wata ne wayoyin za su daina iya amfani ko hawa manhajar WhatsApp.  To amma duk da haka, akwai wasu nau’ukan wayoyin da tuni sun daina aiki tun karshen shekarar da ta gabata.  Musamman wayoyin salula na kamfanin BlackBerry masu dauke da babbar manhajar BB 7 OS.

Wannan ke nuna cewa wa’adin da aka kara ba dukkan wayoyin ya shafa ba, wasu ne daga ciki.  Don haka, zuwa karshen watan Yuni dai dukkan wayoyin da aka ayyana za su daina hawa WhatsApp, sai in sabunta babbar manhajar wayar suka yi ko canza wata wayar sabuwa.  A karshe dai, wannan sanarwa bai da alaka da kamfanonin da suka kera wayoyin, daga kamfanin WhatsApp ne kai tsaye.  Don haka, ko ka ga sanarwa a jikin wayarka a sadda kayi yunkurin hawa manhajar, to, daga kamfanin WhatsApp ne ba daga kamfanin wayarka ba.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, a kara hakuri damu har wa yau dai ina neman kasidar Tsibirin Bamuda cikakkiya daga gareka. Inason ka turo min ita zuwa  ga akwatim Imail dina wato ibniarzika@gmail.com da kuma aarzika@yahoo.com. Na gode ina jiran sakonka.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Arzika.  Na cilla maka kasidar kamar yadda ka bukata.  Sai ka duba akwatin Imel dinka don tabbatarwa.  Allah amfanar damu baki daya, amin.  Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadik da fatan ka wuni lafiya.  Ubangiji Allah yasa haka amin. Dangane da kasidun da kuke sanyawa ne a Blog dinku, a duk sadda na duba sai in ga bayanan dake ciki tun shekarar 2013 ne, ko me yasa?  Sannan zanso ace nine na gina muku wannan dandali don zama zakara da ba da tawa gudunmawar.  Na gode.  Nura Yusif Aliyu (Nura Mafia) unguwan central mosque, Dutse, Jigawa State. Ka huta
lafiya: nuramafia@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Nura Mafia, barka dai.  Muna godiya da wannan kuduri naka, Allah saka da alheri.  Tabbas duk wanda ya shiga shafin da na tanada don taskance kasidun zai ga tun shekarar 2013 rabon da in kara dora wasu bayanai ko kasidun.  Hakan ya faru ne sanadiyyar shagulgula.  Wannan yasa na yanke shawarar kirkiran gidan yanar sadarwa (Web Site) na musamman don taskance dukkan kasidun gaba dayansu.  Wannan zai baiwa masu karatu damar isa gare su cikin sauki kuma kai tsaye;  a duk inda suke a duniya.  Na yi sanarwa watanni uku da suka gabata kan haka, kuma aikin ya kankama.  Da zarar na dora kasidun gaba daya zan sanar da masu karatu.  Wannan zai taimaka wajen dauke nauyin jiran sai na turo wa mutum kasidar da yake bukata ta Imel.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik yaya gida ya aiki?  Kasancewata dallibin fannin “Geography”, don Allah a cikin manyan Jami’o’in duniya ko akwai wacce za ta bani damar yin  amfani da e-library dinta don yin karatu kyauta?  Kuma don Allah a taimaka mini da wani adireshin wani gidan yanar sadarwa inda zan samu manyan littattafan wannan fanni na “Geography” kyauta.  Na gode. Ina sauraro: ramnaz06@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam, da fatan kana lafiya.  Eh, tabbas akwai dakunan karatu da galibin jami’o’i suka tanada don baiwa dalibai damar amfana da dimbin littattafan da suke ciki.  Galibinsu na dalibai ne, wasu kuma kana iya amfana dasu ko ba dalibin jami’ar bane kai amma da sharadin ka yi rajista a shafin yanar nasu.  A halin yanzu bazan iya ce maka ga wanda yake kyauta ba, sai dai in baka shawarar ka bincika a Intanet don tantance wanda zai dace da yanayinka.  Dangane da bayanin littattafan fannin Geography kyauta a Intanet kuma, shi ma abu ne mai yiwuwa sosai.  Sai dai dole ne kayi amfani da kalmomi ko haruffan da za su taimaka maka wajen iya tatso bayanai masu inganci sosai, don samun abin da kake nema ko bukata.

Misali, kana iya amfani da kalmar: “free geography ebooks” a shafin Google.  Wannan zai budo maka amsoshin da suka dace da kalmar tambayarka.  Ko kuma kayi amfani da kalmar: “filetype:pdf geography” a Google, shi kuma zai zakulo maka littattafai ne ko kasidu masu alaka da kalmar Geography ko maudu’in da ka rubuta, a tsarin “pdf”, wanda shi ne tsarin da ake taskance galibin kasidun binciken ilimi da littattafai a Intanet.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, a gaskiya ina matukar karuwa da jin dadin yadda kake wayar mana da kai ta fannin Fasaha. Allah ya saka maka da alheri amin. Ni dalibinka ne kuma ina da tambaya kamar haka: Yaya ake tsarin tallata haja a dandalin facebook?  Kuma ina so ka yi mini bayanin yadda ake mallakar katin Bosting din posting a Facebook?  Na gode kwarai da gaske da fatar zan samu amsa ta wannan adireshin Imel din nawa: irabilu8@gmail.com.  Daga Ibrahim Rabilu Tsafe Jahar Zamfara.

Wa alaikumus salam Malam Rabilu, ina godiya matuka da addu’o’inku.  Dangane da abin da ya shafi biyan kamfanin Facebook kudi don su tallata maka shafinka ko sakonnin da kake rubutawa a shafinka, ba wai wani kati suke sayarwa ba.  Illa dai a duk sadda ka rubuta sako a “Page” dinka za su sanar dakai cewa kana iya biyan kudi don a tallata maka shafinka, idan ka matsa wannan alama ko sako za a zarce da kai ne kai tsaye zuwa inda za ka zabi irin nau’ukan mutane da kake son su ga sakon, da bangare ko nahiyar da suke.  Sannan ka ayyana iya kadadar shekarunsu, da ayyukansu, sai kuma a kaika inda za ka shigar da bayanan katinka na ATM.  A wannan marhala ne za ka ga yawan kudin da za a cajeka. Wannan, a takaice shi ne tsari da yadda abin yake.  Allah sa a dace, amin.


Salaamun Baban Sadik barka da warhaka, ina fatan kana lafiya amin.  Dan Allah ka turo mini da kasidar mai taken “Binciken Malaman Kimiyya kan Tsibirin Bamuda.”: hafsatsadik2020@yahoo.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malama Hafsat.  Na cilla miki kasidar zuwa akwatin Imel dinki, kamar yadda kika bukata.  Allah amfanar damu baki daya, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Sani samaila yakubu says

    Yayi kyau
    ko tayaya zansamu magana da kai

  2. Lawal says

    Thank u

Leave A Reply

Your email address will not be published.