Sakonnin Masu Karatu (2017) (7)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

91

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da aiki. Muna tambaya ne wai da wutar lantarki na hukumar NEPA da kuma ta na’urar Generator wacce ce idan aka caja wayar salula cajin yafi yin karko da ita? Nasiru Kainuwa Hadejia: 08100229688

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nasiru.  Wannan zance ne da galibin jama’a ke yi a kan titi tun bayyanar na’urorin sadarwa na zamani.  Wasu kan ce wai caji da wutar lantarki ya fi caji da wutar lantarkin da na’urar bayar da wuta (Generator) ke bayarwa.  Wasu kuma suce babu bambanci a tsakani.  Abin ya bayyana mini shi ne, idan akwai bambanci, to, yana samuwa ne sanadiyyar girman Janareto din.  Misali, idan karama ce irin wacce ake kira: “I pass my neighbour,” wasu na ganin cewa karfin sinadarin lantarkin da take harbawa bai kai wanda na’urar harba wutar lantarki na hukumar PHCN karfi ba, wannan kuma ke nuna ko da ka yi cajin wayar a wannan yanayi a karshe wayar ta nuna maka caji ya cika, a karshe cajin na iya karewa nan take, saboda rashin tagomashi.  Wannan kenan.

A daya bangaren kuma, idan janareton babba ce, ko madaidaiciya, to, babu wani bambanci tsakanin caji da wutar lantarki daga hukumar PHCN da cajin da aka yi da janareto.  Amma masana sun ba da shawarar cewa idan za ka yi cajin wayarka a kowane lokaci ne, ta amfani da kowanne daga cikin hanyoyin nan biyu, to, zai dace ka kiyaye wasu ka’idoji.  Na farko, idan da janareto ne, kada ka jona wayarka nan take bayan ka kunna ta; ka bari sai ta dan dauki lokaci da fara aiki.  Abu na biyu, da zarar cajin ya cika, ka cire wayar nan take.  Abu na uku, kada ka kashe janareton sai ka cire wayar daga caji.  Abu na hudu kuma na karshe, zai dace ka tanadi na’urar daidaita wutar lantarki a gida, wato: “Stabilizer” ko “UPS”, don daidaita harbawar sinadarin lantarki dake shigowa cikin wayar a yayin da take caji.  Wannan zai taimaka wajen karfafawa ko daidaita sinadarin lantarkin dake shiga wayar ko da kuwa da karamar janareto kake cajin.

- Adv -

Wadannan su ne abubuwan da ake bukata a kiyaye yayin da ake cajin waya ta kowace hanya ce.  Wadannan shawarwari ne da suka dace da hankali da kuma ka’idojin kimiyyar lantarki, amma sauran jita-jita da jama’a ke yadawa marasa dalili, a kawar da kai daga gare su.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, Baban sadik da fatan kana lafiya.  Don Allah ina so kayi mani bayani a kan yadda ake kirkirar blog, misali: http://labarai.blogspot.com.  Nagode.  Muntari Bello Sambo.

Wa alaikumus salam Malam Muntari, barka dai.  A baya mun yi darasi mai tsawo kan wannan maudu’i.  A takaicen takaitawa, akwai manyan madaukai guda biyu da ke bayar da damar bude shafi na Blog a Intanet.  Na farko shi ne kamfanin Google, wanda ke: http://blog.google.com, kamar yadda ka bayar da misali a sama.  Na biyu kuma shi ne shafin WordPress, wanda ake kididdige shi a matsayin na farko kuma na gaba-gaba cikin sahun shafukan dake bayar da damar yin hakan.  Za ka iya samun shafin WordPress a: http://www.wordpress.com.  Yin rajista ba wani abu bane mai wahala, amma ga wanda ya saba mu’amala da Intanet.  Idan zai maka tsauri, kana iya karanta kasidar da na rubuta a bayan dake shafinmu a: http://fasahar-intanet.blogspot.com.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa mu dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.