Sakonnin Masu Karatu (2017) (3)

90

Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah ya kara basira amin.   Don Allah ka turo mini kasidarka kan tsibirin “Bamuda Triangle” ta imel dina dake: ibrahimali056@naij.com. Daga Yahya (Abban Humairah), Gombe: 08035767045

 

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Yahya.  Ina godiya da addu’o’inku.  Ka duba akwatin Imel dinka, na cillo maka kasidar, kamar yadda ka bukata.  Allah amfanar damu baki daya, amin.  Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadik. Yaya gida kuma yaya iyali? Allah ubangiji yasa kowa lafiya amin. Na kasance mai bibiyar shafinka na kimiyya da kire-kire a jaridar Aminiya mai albarka. Ina son in bude wata manhaja wadda za ta kawo ci gaba a yankinmu baki daya. Shi ne nake son kayi mani karin bayani ta yadda zan fara bullo wa lamarin da kuma wani kalubale ne zan fuskanta?  Idan na samu bayani kan tambayata ina son a turo mini ta Imel dina mai taken: sfulani10@gmail.com.  Na gode. Sako daga Zayyanu Tsafe

 

Wa alaikumus salam, Malam Zayyanu barka dai.  Na yi sha’awar wannan buri naka.  Haka ya kamata kowannenmu ya zama mai son ci gaban al’ummar da yake rayuwa cikinta.  Duk da cewa baka yi cikakken bayani kan bukatarka ba, ina tunanin kana nufin wata manhaja ce ta kwamfuta ko wayar salula ko ma duka biyun, da za ka gina, don baiwa jama’a damar amfana da ita, kyauta.  Abu na farko dai shi ne, sai ka dubi meye al’ummarka suka fi bukata, ko meye kake ganin al’umma na wahala wajen aiwatar dashi?  Wannan shi zai baka damar nemo hanyar warware musu matsalar.  Abu na biyu, shin, matsala ce da za ka iya warwarewa don saukaka musu rayuwarsu? In eh, sai kaje mataki na gaba.  Amma idan amsar a a ce, to, sai ka dubi wata matsalar daban.

 

Abu na uku, yaya za ka samar da hanya mafi sauki gare su don warware wannan matsala?  Amsa wannan tambaya na bukatar tunani mai tsawo, iya gwargwadon kwarewarka kan abin da kake son aiwatarsa.  Tunda muna magana ne a bangaren manhajar kwamfuta ko wayar salula, sai ka dubi mahallin, shin, akwai wata manhaja dake iya sawwake musu wannan matsala?  In eh, to, suna amfana da wannan manhaja?  In a a, to me yasa?  Ta yiwu watakila manhajar da turanci take ko larabaci, su kuma galibi basu kware a wadannan yaruka ba.  Wannan zai baka damar gina manhaja irinta, ko ma wacce tafi ta wajen kwarko da inganci, amma cikin harshen Hausa.  Idan kuma babu wata manhaja gaba da ke iya aiwatar musu da wannan aiki, to, ta yaya za ka iya samar musu da ita?

 

Amsa wannan tambaya na bukatar tunani shi ma sosai.  Misali, zai iya yiwuwa rashin kwarewa a fannin turanci ne mafi girman damuwarsu.  Kai kuma kana son ganin sun kware, musamman ganin cewa hatta mu’amala da kwamfuta ko wayar salula duk suna bukatar ya zama kana jin turanci.  Wannan zai sa ka gina musu manhaja ta musamman don koyon harshen turanci, cikin harshen Hausa.  Ko kuma, a daya bangaren, al’ummarka na fama da matsalar wanda zai iya raba musu gado a duk sadda aka yi rasuwa.

 

Ko kuma akwai masu iya rabon gadon, amma kana son ka kayatar tare da sawwake hanyar yin hakan, musamman kan abin da ya shafi sarkakiyar lissafin da rabon gado ke dauke dashi.  Duk, ta hanyar manhajar kwamfuta kana iya samar da wannan sauki.  Sai ka gina musu manhaja cikin harshen Hausa, wacce da zarar an saukar da ita a kan kwamfuta ko wayar salula, za a shigar da adadin kudi ko kimar kayan da mamaci ya bari ne, sannan a shigar da bayanin mamacin (Uba ne, ko Uwa, ko Mata, ko Da, ko ‘Ya ko Kaka da sauransu).  A karshe kuma a shigar da sunayen magada, a matsa maballin lissafi, nan take sai manhajar ta aiko da sako mai dauke da rabon gaba daya, da kason kowa cikin magada.  Idan ma akwai wanda bai cancanci gado ba, za ta fitar dashi gefe, a matsayin wanda aka katange ko shamakance.  Wannan misali kawai na kawo maka.

 

- Adv -

Bayan ka gama tantance amsoshin wadancan tambayoyi, sai ka tanadi kayan aiki.  Abu na farko ita ce kwamfuta, wacce dukkan ayyukan suka ta’allaka gare ta.  Dole ne ka tanadi kwamfuta, ko karama ko matsakaiciya; ba sai lalai babba ba.  Sai kuma ka tanadi manhajojin da za su taimaka maka wajen gina manhajar.  Abu na uku shi ne kwarewarka;  idan kana da kwarewa a fannin ilimin kwamfuta, tuni na san ka san inda za ka dosa.  Idan kuma ba ka da kwarewa a wannan fanni, to, aiki na gaba shi ne tanadar kwarewar da za ta taimaka maka wajen aiwatar da ayyukan.  Ka sani, shi ilimin gina manhajar kwamfuta ba wai dabo bane, ba kuma maita bane; ilimi ne mai zaman kansa.  Duk abubuwan mamaki da kake gani ake aiwatarwa ta hanyar manhajar kwamfuta da ilimi aka gina su.  Abin da wannan ke nufi shi ne, ita kwamfuta kawai kayan aiki ce, ba wai ita ce za ta maka aikin ba.  Irin bayanin da ka shigar mata shi za ta sarrafa ta aiko maka da amsa.

 

Abin da nake son cewa a takaice dai shi ne, zama za kayi ka tsara yadda manhajar za tayi aiki, da yadda mai amfani da ita zai iya sarrafa ta.  Sannan sai ka rubuta wadannan bayanai cikin umarnin da kwamfuta ke iya fahimta, ta amfani da yaren gina manhajar kwamfuta, don ba ta damar yin abin da kake son tayi.  Kana iya neman karin bayani wajen masa ko ta hanyar Intanet, don samun karin haske.  Wannan ‘yar takaitacciyar shawara ce.  Ina maka fatan alheri, kuma Allah sa a dace, amin.  Da fatan ka gamsu.


Salamun alaikum Baban Sadik, suna na Comrade Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina.  Ina son ka turo mini da wata makala da ka gabatar a Makera motel, Katsina a wasu ‘yan shekaru da suka wuce, ta Imel dina kamar haka: unshakablecomrade@yahoo.com.  Na gode. 08165270879

 

Wa alaikumus salam, barka dai Comrade Bishir. Sai ka duba akwatin Imel dinka don daukar kasidar; tuni na cillo maka ita.  Allah amfanar damu baki daya, amin.  Na gode.


Salamun alaikum Baban Sadik, ina fatan kana lafiya.  Mene ne mahimmancin amfanin Wi-Fi na waya, kuma a wasu kasashe kamar Dubai sai kaga idan mutum zai yi amfani da da fasahar Intanet na waya, manhajar WI-FI na wayarsa ake bukatar kawai ya bude; zai yi duk irin abin da zaiyi, har da hawa shafin youtube.  To mu nan Najeriya me yasa sai ka sayi DATA ta kamfanin layin da kake amfani dashi sannan za ka samu damar hawa youtube?  Mene ne banbancinmu dasu kenan? Daga Ibrahim garba Tukuntawa: 08036432793

 

Wa alaikumus salam, Malam Ibrahim barka dai.  Na farko dai, bayani kan ma’anar “Wi-Fi” ya sha maimaituwa a nan.  Abin da zan iya cewa kawai shi ne, “Wi-Fi” dai wata fasaha ce da ake amfani da ita wajen jonuwa da siginar Intanet ta wayar iska, a wayar salula.  Galibin wayoyin salula na zamanin yau suna da hanyoyi biyu da ake iya mu’amala da fasahar Intanet dasu.  Hanyar farko ita ce amfani da tsarin kamfanin wayar salula, irin su MTN da Etisalat da Glo, misali.  Wannan tsari shi ake kira: “Mobile Data Network.”  Hanya ta biyu ita ce ta amfani da tsarin fasahar “Wi-Fi”, wanda tsari ne na wayar iska, wato: “Wireless.”  Amfani da wannan tsari na bukatar samuwar marhalar da siginar Intanet ke gudanuwa, wato: “Access Point” kenan a harshen turancin kimiyyar sadarwa ta zamani.

 

A nan Najeriya ma muna da wannan tsari.  Ta yiwu a can ka je inda suke da budadden tsari ne, inda kowa ke iya jonuwa yayi amfani da tsarin kyauta.  Wannan shi ne abin da ka gani ko ka sani a can.  Kuma watakila baka taba cin karo da wannan tsari ba a Najeriya ko inda kake zaune.  Amma akwai kamfanoni da dama dake sayar da na’ura mai suna: “Router” ko “Mi-Fi” ko “Wireless Modem” misali, wanda idan ka saya, za ka jona wayarka kai tsaye kayi amfani da tsarin ba matsala.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.