Fasahar “Digital Currency”: Manyan Fa’idojin “Cryptocurrency”

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 21 ga watan Mayu, 2021.

385

Manyan Fa’idoji da Matsalolin “Cryptocurrency”

A makonnin jiya da shekaranjiya mai karatu ya samu bayani kan nau’ukan kudaden zamani dake Intanet, da kuma takaitaccen bayani kan wasu shahararru daga cikinsu, wanda ya hada da asalinsu, da wadanda suka samar dasu, da fasahar tantancewar da suke amfani da ita wajen gudanar da cinikayya, sannan da farashin kowanne daga cikinsu.  Daga wannan mako zuwa makon gobe da jibi in Allah Yaso, makalarmu za ta dubi fa’idoji da kuma matsalolin dake tattare da wadannan nau’ukan kudade ne na zamani da ake amfani dasu a Intanet da sauran kafafen sadarwa na zamani.  Domin duk wani abu na mu’amala, dole yana da amfani ko dauke da wasu matsaloli.  Ana la’akari ne da bangaren da yafi rinjaye don masa hukuncin karshe.

Manyan Fa’idojin “Cryptocurrency”

Fasahar “Cyrptocurrency” na dauke da fa’idoji masu yawa, kamar yadda masu hulda da ita ke zuzutawa.  Shahararru daga cikin wadannan fa’idoji dai sun hada da:

Kariya Daga Faduwar Darajar Kudi

A baya galibin jama’a kan sayi dalar amurka ne, musamman a kasashe masu tasowa, ko gwalagwalai, don adana su, saboda tabbatar da kimar kudin da suka mallaka, maimakon zuwa banki kawai su zuba kudin, kimarsa na zagwanyewa sanadiyyar tabarbarewar tattalin arziki.  To amma yanzu masu yin haka galibi sun koma bangaren na’ukan kudaden zamani dake Intanet, musamman Bitcoin.  Hakan ya faru ne saboda a duniya babu kudin da farashinsa ke haurawa a kowace rana, kuma yake da kimar da Bitcoin ke dashi.  A halin yanzu kwandalar Bitcoin guda daya ta kai naira miliyan ashirin da daya da ‘yan kai.  Wannan kimar dai ta samo asali ne saboda karancin adadin kudin a duniya.  Domin a yadda aka tsara magudanar Bitcoin, za ta samar da kwandaloli miliya 21 ne kacal.  A halin yanzu ana da kwandaloli miliyan 18.  Wannan karanci yasa farashin ke haurawa a kullum, saboda yawaitar mabukata.

Idan ka sayi na kowane adadin kudi ne, a duk sadda kimar kwandalar Bitcoin ta daga, kimar kudinka zai daga.  Idan da kashi 50 ne farashin ya tashi, kaima kudinka zai kiru da kashi 50.  Shi yasa ma, kashi kusan 90 cikin 100 na masu sayan Bitcoin suna saye ne don idan farashinsa ya daga sai su sayar su samu riba.  Wannan shi ake kira: “Capital Gain” a fannin zuba jari.  A takaice dai, a duk duniyar yanzu ba hajar da ta kai Bitcoin saurin hauhawa wajen farashi.

Cikakkiyar ‘Yanci

Sabanin tsarin hada-hadar kudi na zahiri da muke amfani dashi a kasashenmu, wanda hukuma ce da bankuna ke lura da gudanar da komai, tsarin kudaden zamani na Intanet ba haka suke ba; ana gudanar dasu ne cikin cikakkiyar ‘yan ci.  Da zarar ka sayi kudin na wani adadi, kana iya sayar da abin da ka saya tsakaninka da mai saye kai tsaye, ba sai wani ya sani ba.

- Adv -

Cikakkiyar Kariya da Sirri

A tsarin gudanarwa na Banki, komai naka a hannun bankinka yake.  Sun ma fi ka sanin me ke faruwa a taskar taka.  Amma a wannan tsari na zamani, kana da cikakiyyar kariya da sirri a taskarka.  Hatta kamfanin dake ajiyar kudaden ma bai sanin nawa ka mallaka kuma wa da wa kake hulda dasu a lalitarka (Wallet).  Amma a tsarin bankuna kuwa bankinka yafi kowa sanin abokan huldarka da kuma abubuwan da kake gudanarwa.  Shi yasa ma ake da sauki ya kulle taskarka kai tsaye ba tare da saninka ba.

Saukin Canjin Kudade

Idan kana da kwandalolin kudaden zamani na “Cryptocurrency”, cikin sauki kana iya mallakar nau’ukan kudaden wasu kasashen.  Haka idan kana son sayan kwandalar Bitcoin misali, da kowane irin kudi za ka iya amfani wajen saya.  Abin da baza ka iya yi ba kai tsaye a ko ina, shi ne ciro nau’in kudin a matsayin takarda, don canja shi da wani kudin na daban.  A tare da cewa an fara samun na’urar ATM na Bitcoin (Bitcoin ATM) a wasu kasashe sai dai ba abu bane da ya shahara a ko ina.  Kana iya amfani da wannan na’urar ma wajen saya ko sayar da kwandalolin da kake dasu na Bitcoin, cikin sauki.  Duk da za a cajeka wani adadi na kason kudin da ka saya ko sayar.  A takaice dai, akwai sauki wajen juya nau’ukan kudi wajen hada-hadar kasuwancin kudaden zamani.

Caji Mai Rahusa

Kasancewar babu wani shamaki mai yawa tsakaninka da abokin huldarka wajen saya ko sayar da kwandalar kudaden zamani na Intanet, cajin da ake karba wajenka kadan ne, a wasu lokuta ma babu.  Sabanin tsarin banki na zahirin rayuwa.  Bankinka zai cira, gwamnatin Najeriya ta cira, sannan kamfanin da ya bayar da katin da kake amfani dashi, shi ma yana da nashi kason.  Kuma duk a cikin kudinka za a cire.  Amma a tsarin hada-hadar kudaden zamani na Intanet, babu irin wannan dan karen caji mai yawa.

Saukin Aikawa da Karban Kudade

Duk da tsarin aikawa da karbar kudade na zamani (Payment System) da muke amfani dashi a Najeriya (wanda mun riga kasar Amurka fara amfani dashi) mai sawwake tsarin aikawa da karban kudade ta hanyar wayar salula da na’urorin sadarwa na zamani, said ai idan aka gwama shi da tsarin aikawa da kudaden zamani na Intanet, za a ga bambanci mai girman gaske.  A tsarin da muke amfani dashi a zahirin rayuwa, akwai shamaki mai kawo tsaiko.  Domin idan ka aika, sai bankinka ya tabbatar da abin da za ka aika.  Idan ta hanyar ATM ne, sai kamfanin katinka ya tabbatar da hanyar, da adadin kudin, da bankin da za ka aika kudin, sannan kudaden su tafi.  Haka idan za ka karba.  Amma a tsarin hada-hadar kudaden zamani ta Intanet, duk babu wannan tsaiko.  Da zarar ka nufaci wanda kake aika ma kudi, kai tsaye kudaden za su tafi, daga lalitarka zuwa tasa, cikin sauki.

Wadannan, a takaice, su ne kadan cikin fa’idojin dake dauke cikin wannan tsari na kudaden zamani ta Intanet.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.