Sakonnin Masu Karatu (2017) (4)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

84

Assalamu alaikum Baban Sadik, baka da warhaka.  Yaya ake goge duk wani virus a jikin waya mai dauke da “Memory”?  Daga Abbagana Kallah Machina: 08085835191.

Wa alaikumus salam, Malam barka dai.  Idan wayarka mai dauke da babbar manhajar Android ce, kana iya hawa Play Store ka nemo manhajar goge kwayar cutar kwamfuta.  Akwai na kudi da kuma kyauta.  Da zarar ka saukar a kan wayarka, amfani da manhajar ba shi da wahala ko kadan.  Sannan, manhajar na iya tantance dukkan bayanan dake wayar; da wadanda ke kan ma’adanar waya da wadanda ke kan ma’adanar “Memory”, kai tsaye.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban sadik, tambayata ita ce: ko akwai wata duniya mai halittu kamar wannan duniyar tamu?  Daga Abubakar Garba Sokoto: 08036339139

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abubakar.  Babu wata duniya mai dauke da halittu irin wannan duniyar da muke rayuwa a ciki.  Idan kana tare da wannan shafi shekaru bakwai da suka gabata, a cikin kasidarmu mai take: “Makamashi da Dukkan Nau’ukansa,” mun kawo bayanai dake tabbatar da cewa, daga cikin dukkan duniyoyin da Malaman sararin samaniya suka gano, babu wata duniyar da dana dam zai iya rayuwa irin wannan rayuwar da muke yi, a yanzu dai, sai a wannan duniyar tamu.

Daga cikin dalilan da suka bayar sun nuna cewa, kusan dukkan wani yanayi dake wannan duniya (na zafi, ko sanyi, ko iska, ko dumi, ko damina, ko bazara da dai sauransu), madaidaita ne wajen mizani da awonsu.  Kuma ya zuwa yanzu dai, suka ce babu wata duniya mai dauke da yanayi irin tamu.  In kuwa haka ne, ashe babu inda za a iya rayuwa irin wannan, sai nan.  Tabbas cikin ‘yan shekarun da suka gabata an gano wasu duniyoyi guda hudu da ake ganin rai za ta iya rayuwa a cikinsu, amma ba a yanayi irin na wannan duniya ba.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum barka da warhaka, ina fata kana cikin koshin lafiya da kai da iyalinka baki daya, amin summa amin.  Don Allah ina so ka turo mini da kasidarka mai taken: “BAMUDA TRIANGLE”, ta hanyar adireshin Imel dina kamar haka: abubakarsadiq13731@gmail.com.  Don Allah ka taimaka domin na yi ta tura maka sako a facebook amma ba labari.  Na gode sai na ji daga gareka.  Daga Abubakar sadiq. 09063559076

Wa alaikumus salam, da fatan kana lafiya.  Sai ka duba akwatin Imel dinka, tuni na cilla maka kasidar.  Allah amfanar damu baki daya, amin.  Na gode.


- Adv -

Assalamu alaikum Malam Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik).  Don Allah ina son ka taimaka mini da bayani ko da a takaice ne kan yadda zan iya amfani da manhajar “Google+”.  08064942376

Wa alaikumus salam, Malam barka ka dai.  Abu na farko shi ne kayi rajista din adireshin Imel na Google mai suna Gmail.  Da zarar ka mallaki wannan adireshi, to, kusan dukkan shafukan Google kana iya mu’amala dasu, daga ciki har da dandalin sada zumunta na Google +.  Bayan ka mallaki wannan adireshi, sai kaje shafin dake: www.googleplus.com, za a budo maka shafin.  Daga bangaren hannun dama za ka tambari da aka rubuta: “Sign In” a kai, idan ka matsa za a budo maka inda za ka shigar da adireshinka na Gmail, daga nan sai shafin.  Babu wahala.  Sauran tsare-tsare kuma da kanka za ka yi.  Domin kusan duk wani wanda ka taba aika masa sakon Imel da adireshin, zai iya ganinka kai ma za ka iya ganin bayanansa.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik yaya aiki kuma ya iyali?  Tare da fatan kana lafiya amin.  Don Allah a taimaka a amsa mini tambayata.  Wai yaya ake gudanar da bincike a kan wani abu da mutun yake so ya kera ne?   Kamar yadda za ka ga manya-manyan suna bincike a kan wani abu da suke so su kera kuma kaga binciken nasu ya yi daidai sun samu galaba.  Misali, kwanaki na ji labarin wani matashi da ya kera wani dan karamin jirgi mai saukar ungulu wanda yake tashi sama.  Sannan kuma ya kera wani dan karamin (rocket) wanda shi ma yake tashi sama.  Da sauran ire-iren wannan yaro dayawa da nake jin labara.  To shi ne abin yake bani matukar mamaki yadda a keyi mutun yayi tunanin abu kuma kaga ya kera shi, don ni dalibi ne kuma mutun mai sha’awar kere-kere.  Don Allah, don Allah a taimaka a amsa mini tambayata cikin gamsasshshen bayani.  Daga Sadik Katsina: 08069611572

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Sadik.  Na fahimci abin da ke baka mamaki, duk da cewa ba wani abin mamaki bane.  A rayuwa idan ka sa ranka cewa za ka yi wani abu na alheri, kuma jajirce a kai, to, tabbas Allah zai agaza maka.  Tabbas akwai wadanda suke ‘yan baiwa ne, amma ko su dinmu, sai sun hada da dagewa da kuma jajircewa.  Da farko dai dole ne ya zama kana da mahanga da kuma manufa.  Me kake son ka cin ma wa, na buri?  Wannan ne zai zaburar dakai, tare da haska maka kwakwalwarka wajen gano hanyoyi da fasahahohin da za kayi amfani dasu wajen cinma burinka.

Mu kaddara kana son kirkirar wata na’ura ko fasaha.  Abu na farko shi ne kayi bincike kan abin da kake son kerawa.  Wajen bincike ne zaka samu bayani kan ire-iren abin da wasu suka kera makamancinsa a baya, da irin hanyoyin da suka bi wajen yin hakan, da kuma kurakuran da suka tafka ko matsalolin dake tattare da abin da suka kera.  Wannan zai taimaka maka wajen kauce wa ire-iren wadannan matsaloli ko kurakurai.  Daga nan sai yi taswirar abin da kake son kerawa cikin zane, ka kuma taskance bayanin abin da kake son kerawa, wajen siffa, da tsarin aiki, da gudanuwa, da wadanda za su yi amfani dashi, da abubuwan da kake bukata na kayan aiki wajen kerawa ko samar da fasahar.  Da zarar ka gama wannan, sai kaje marhala ta kusa da karshe, ita ce hakikanin aikin samar da fasahar.

Idan ka kuma aikin gwaji, wanda shi ne zai fito maka da kura-kuran dake cikin fasahar.  Kana iya yin gwajin da kanka, ko kuma bayan kayi, ka samu wasu mutane na musamman, wadanda ke amfani da fasaha makamanciyarta ko irinta, don su baka shawara.  Wannan, a takaicen takaitawa, shi ne abin da zan iya cewa.  Ina maka fatan alheri, Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum, ina maka fatan alkhairi tare da duk ahalinka.  Allah ya kara maka martaba da basirai iri-iri har irin basirar da a yanzu ba fannin rayuwarka bane.  Allah ya kare ka daga sharrin rayuwa. “Ina so nai gamo da kai ne kawai a dandalin facebook, kuma na ganka har na aiko da neman izinin zama aboki a gareka wato “Friend Request” za ka gan shi  “Real Prince Umar” ka karbe ni don Allah! – 08034977956

Wa alaikumus salam, barka dai Prince.  Na jima ban hau Facebook ba saboda shagulgula.  A kalla na yi makonni za su kai 4 ko 5.  Amma zan duba in Allah yaso kuma zan amince da bukatar abotarka.  Allah sa mu dace, amin.  Na gode da zumunci.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.