Tsarin Amfani da Wayar Salula (7)

Kashi na 32 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

362

Taskance Bayanan Sirri

Wayar salula ma’adanar sirri ce, amma ga wanda ya iya adana, ya kuma san tsarin adanawa da taskancewa.  Kowace wayar salula na iya baka damar taskancewa (ta hanyar rubutu), da kuma adanawa (ta hanyar masarrafai) ga duk abin da kake ganin sirri ne a gare ka.  Da farko dai, akwai tsarin kariya (Security Features) da kowace wayar salula ke zuwa da shi. Kana iya kulle maballan wayarka, ya zama ba za a iya yin kira ba ko ganin dukkan bayanan da ke cikin wayar ba sai da yardarka.  Wannan na samuwa ta tsarin Keypad Lock, wanda kowace wayar salula ke da shi; komai kankanta da rashin tsadarta kuwa.

Bayan haka, akwai masarrafai na musamman da ake taskance bayanai da su, irin su Notes, da kuma Active Notes wadanda suka shahara a wayoyin Nokia.  Sannan akwai Diary kamar yadda wasu wayoyin salula kan kira shi.  A wayoyi nau’in BlackBerry akwai Memo Pad, da Tasks, wadanda za a iya samunsu a jakar Applications; duk kana iya taskance bayanan sirri da su.  Bayan wadannan, akwai tsarin kariya da kowace waya ke bayarwa don kulle ma’adanar waya (Phone Memory) da katin ma’adanar waya (Memory Card) ta yadda babu wanda zai iya isa ga bayanan da ke cikinsu sai da kalmomin izinin shiga, wato Password. 

Nau’ukan bayanan da za a iya taskancewa da adanawa dai sun hada da adireshin Imel, da kalmomin izinin shiga, da lambobin ajiyar banki (Bank Account Details), da adireshin wurare, da duk wani bayani mai muhimmanci ga mai waya.  Nau’ukan bayanan ba su da iyaka; ya dangancin irin muhimmancin da suke da shi ga mai wayar, ko irin muhimmancin da ya basu.  Har wa yau kana iya taskance hotuna, da bidiyo, da sakonnin tes da lambobi ta yadda ba mai isa gare su sai da izininka.  Don haka, wayar salula kamar lalita ce.  Sai dai kuma, yana da kyau mu san cewa, kowace lalita fa, wasu lokuta tana lalata.

Don kariya daga rasa dukkan bayanan da ka taskance sanadiyyar matsalolin da ka iya samun wayarka ba da sani ko so ba, yana da kyau kayi tanadi.  Duk abin da ka san ka taskance shi a wayarka, to yana da kyau ka samu makwafinsa a wani wuri.  Na farko dai idan zai yiwu, ka sake taskance su a katin SIM dinka, musamman idan lambobi ne ko sakonnin tes.  Da zarar waya ta samu matsala, kana iya zare katin SIM dinka ka dora a wata wayar don samun makwafinsu.  Idan a katin ma’adanar waya ne sai ka samu wani katin daban, ka taskance su a ciki.  Idan kuma a masarrafar waya ne sakonnin suke taskance, irin su Notes, ko Active Notes da dai sauransu, sai ka saukar da manhajar mu’amala da wayar, wato Phone Suite ko Nokia Suite idan Nokia ce.  Idan sabuwa ce wayar ka saya, duk kana iya zuwa gidan yanar sadarwar kamfanin da ya kera wayar, ka saukar da manhajar da ake mu’amala da wayar da ita.

Da zarar ka yi haka, sai ka loda manhajar a kwamfuta, sannan ka jona wayarka da kwamfutar, ka bude manhajar, ka je masarrafar makwafin bayanai, wato Phone Backup, ko Data Backup, ko duk wani suna da yayi kama da haka, don taskance dukkan bayanan da ke cikin masarrafan wayarka, cikin sauki.

Mu’amala da Manhajar Tunatarwa/Farkarwa

Wayar salula bata zo don ba ka daman kira da amsa kira ko rubuta sakonnin tes kadai ba, har da taimaka maka wajen samar da tsari a rayuwarka.  A matsayinka na musulmi, kana iya amfani da wayar salula wajen tunatar da kanka duk abin da kake son yi a rayuwa; daga lokacin sallah zuwa lokacin tashi a barci cikin dare, ko rana, ko yamma.  Akwai manhajar tunatarwa na musamman da dukkan wayoyin salula ke zuwa da ita. Sai dai abin bakin ciki bamu cika damuwa da ire-iren wadannan abubuwa ba.  Abin mamaki, da yawa daga cikinmu na amfani da kashi 30 cikin 100 ne na alfanun da ke tattare da wayoyinmu.  Amma duk da haka da mun ga wata sabuwa, sai muyi caraf muna neman sake saya.  Shin, kafin ka sayi wata, ka gama kure karfi da kudurar wacce kake tare da ita ne?  Shin, mai karatu ma ya taba yi wa kansa wannan tambayar kuwa kafin  ya canza waya?

Akwai manhaja ta musamman mai suna Reminder, ko Alarm.  Ba su kadai ba, kana iya ayyana abin da za ka yi nan da kwanaki ko watanni, ka sa wayar ta tunatar da kai ta hanyar sauti ko bayyana rubutacciyar tunatarwa a shafin wayarka.  Da zarar lokacin ya yi za ta tunatar da kai babu jinkiri.  Kana iya sa duk irin sautin da kake son wayar ta tunatar da kai.  Har wa yau kana iya amfani da Kalandar wayar, wato Calendar, ko kayi amfani da manhajar farkarwa, wato Alarm, don nusar da kai abin da kake son yi; cikin dare ne ko rana, ko duk lokacin da kake so.

- Adv -

Idan kana bukatar tunatarwa cikin dare, sai ka je cikin Menu, ka shiga manhajar agogo (Clock) ko manhajar tunatarwa/farkarwa (Alarm), ka shigar da lokacin da kake son a farkar da kai.  Idan da karfe biyu kake son a farkar da kai, sai ka sa lokacin.  Daga nan za a tambayeka yanayin tunatarwa; shin, da sauti za a tunantar da kai ko da gunji (Vibration)?  Sai ka zaba. In da sauti ne, za a bukaci ka zabi sautin da kake son a tunatar da kai da shi.  Sannan za a tambayeka; shin, kana son a rika maimaita maka tunatarwar, ko a a?  In kace eh, za a tambayeka tazarar lokacin da kake son idan aka maimaita, a sake maimaitawa.

Wannan shi ake kira Snoozing.  Idan aka farkar da kai da karfe biyu, sai bacci ya rinjayeka, za a sake farkar da kai da karshe biyu da minti biyar misali, nan ma idan baka farka ba, sai a sake farkar da kai da karfe biyu da minti goma, har dai zuwa lokacin da ka farka.

Idan kuma tunatarwa ce kake son a maka, don yin wani abu a wata rana ko lokaci, kana iya sa tunatarwar ta zama da minti biyar ko goma ko ashirin, kafin lokacin abin, don ka samu shiryawa ba tare da ka makara ba.  Duk wadannan hanyoyin tsari ne na rayuwa.  Sannan kana iya hada dukkan bayanan da ke da alaka da yin wani abu, wadanda ka taskance su a manhajar Notes ko Active Notes misali, wadanda kuma suka danganci wani sha’ani, misali biki, ko tafiya, ko ziyara, su zama kamar tunatarwa.  Idan kayi haka, da zarar lokacin yayi, nan take bayanan za su bayyana a shafin wayarka, tare da sautin tunatarwa idan ka sa.  Abin da za ka kiyaye shi ne, idan ka san kana da saurin firgita, to, kada ka sa wayarka ta rika tunatar da kai ko farkar da kai ta hanyar gunjin waya, wato Vibrating.

Lura da Yanayin Sadarwa (Network)

Yanayin sadarwa shi ne sinadarin sadarwa baki daya.  Idan babu shi, to ba a iya aiwatar da kira ko amsa shi.  Yana da matukar muhimmanci a jikin wayar salula.  Wayoyin salula na wannan zamani suna zuwa ne da tsarin kalato yanayin sadarwa guda biyu.  Na farko shi ne na kai tsaye, wanda wayar da kanta take kokarin nemo yanayin sadarwar, don tabbatar da mai waya ya samu damar aiwatar da kira da amsa kira ko aika sakon tes ko aiwatar da duk wani abin da ke ta’allake da yanayin sadarwar kamfanin wayar.  Wannan tsari na kai tsaye shi ake kira Automatic Network Searching.  A daya bangaren kuma akwai tsari da neman yanayin sadarwa da hannu.

Wannan shi ake kira Manual  Network Searching.  Idan kana son ganin kowannensu sai ka je Menu, ka gangara Settings, ka shiga Phone Settings, sannan ka matsa Network, nan za ka ga Automatic.  Idan ka matsa, za a bude maka shafi inda za ka iya canzawa daga tsarin kai tsaye zuwa tsarin  nemo yanayin sadarwa da hannu, wato Manual kenan.

Akwai alama da ke nuna samuwa ko bacewar yanayin sadarwa a fuskar kowace waya. Ita ce alamar doguwar sandar da ke tsaye a bangaren hagu, a galibin wayoyin salula.   A wasu wayoyin kuma alamar na siffar Dala ne, a hannun dama. Musamman a wayoyi nau’ukan BlackBerry da sauran manyan wayoyin salula na zama.  Ala ayyi halin dai, za a samu alamar ne gab da sunan kamfanin waya a shafin wayar salula.  Idan yanayin sadarwa yayi kasa, za a ga sandan ya ragu.  Idan kuma ya karu sandan zai kara tsayi har ya daki iya tsawonsa. Amma a wasu lokuta kuma za ga alamar a cike, amma kuma ka kasa samun layi don kira.  Duk wannan na daga cikin kebantattun matsalolin tsarin sadarwa ta waya-iska, wato Wireless Communication. 

Duk sadda ka bukaci yin kira amma ka kasa, alhali ga alamar yanayin sadarwa a cike, to, kana iya canza tsarin nemo yanayin sadarwa, ta hanyar shiga Menu, zuwa Settings, a gangara Phone Settings, sai a matsa Network.  Daga nan sai a canza daga Automatic zuwa Manual.  Da zarar an zabi Manual, nan take wayar za ta kama nemo yanayin sadarwa kai tsaye, sai ta samu.  Idan ta gama nema, za ta budo dukkan sunayen kamfanonin wayoyin salula da ke da yanayin sadarwa a muhallin da mai waya yake, sai ka zabi na kamfaninka.  Idan aka gwada wannan dabara amma abu yaki, to, ana iya kashe wayar, sai a sake kunnawa.  In Allah yaso za a  dace.  Idan hakan ma yaki, to, akwai alamar matsalar gamammiya ce.  Daga nan sai a hakura, a ci gaba da gwadawa lokaci zuwa lokaci, har a dace.

Manhajar Wasannin Wayar Salula

Manhajar wasanni, wato Games suna daga cikin abubuwan da wayoyin salular zamani ke zuwa da su.  Babbar dalilin samuwarsu dai ba ya wuce samar da nishadi ga mai wayar salula.  Akwai nau’ukan wasanni daban-daban a cikin wayoyin salula. Idan kai mai sha’awar ire-iren wadannan manhajoji ne, kana iya amfana da su sosai.  Daga cikin manyan alfanun da ke tattare dasu akwai wasa kwakwalwa, da kuma karin ilimi da sanin mahangar rayuwa.  Amma sai dai yana da kyau mai karatu ya sani, kada ya bata lokacinsa wajen shagala da wadannan manhajoji, musamman idan akwai wasu abubuwa masu amfani da suke bukatar hankalinsa.  Sannan bayan haka, yawan amfani da wadannan manhajoji na wasanni suna cinye batirin wayar salula cikin gaggawa, saboda tasirinsu wajen karin aikin masarrafar wayar a lokaci takaitacce.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muhammad Shehu Fagge says

    Godiya mai yawa,Allah Ya taimaka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.