Sakonnin Masu Karatu (2017) (2)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

141

Salamun alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya, Allah ya kara basira.  Don Allah ina da waya kirar “Hisense hs-T928”, na kaita wajen masu gyara a mata “Flashing” sai aka ce baza tayi ba saboda kamfanin wayar bai sake  fayil din wayar a Intanet ba.   Don Allah ina bukatar shawararka Allah Yasa ka gama da iyayenka lafiya, amin.   Daga dalibinka: Muhammad Nura: 07039091198

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Muhammad.  Shawarar da zan baka ita ce: ka nemi wani mai gyaran wayar ko mai filashin din, amma abin da ya fada ba haka bane.  Amma dole ka masa uzuri, ta yiwu ya yi iya binciken da zai iya yi ne, da ya kasa samu shi yasa ya gaya maka haka.  Amma wannan waya tana dauke da ka ambata tana dauke ne da babbar manhajar Android nau’i na 4.1.  Kuma akwai babbar manhajarta ko ince akwai manhajojin da ake iya amfani dasu wajen yi mata filashin.  Duk bayanan da nayi a baya kan abin da ya shafi filashin, sun hada da ita.

Duk da cewa ban san mece ce hakikanin matsalar wayar ba, idan ka samu wanda ya kware wajen gyara zai iya mata filashin.  Don haka nake ba da shawarar a nemi wani mai gyaran, muddin lalacewar bai wuce haddi ba, za a iya dawo da ita.  Allah sa a dace, amin.


Slamun alaikum, na san muna da duniyoyi tara (The Nine Planet), amma wani malamin fannin Biology yace mana yanzu saura guda takwas, dayar ba a san inda taje ba.   To, yanzu tana ina ne? Kuma abin da ya gaya mana haka ne? Daga Aminu A. A. Logic: 08093839553

Wa alaikumus salam, Malam Aminu barka dai.  A iya sani na ban da wani bayani tabbatacce dake nuna cewa daya daga cikin duniyoyin da malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronmers) suka gano, ta bace.  Ban taba jin wannan labari ba sai ta hanyar wannan ruwayar taka.  Ya kamata malaminku ya muku cikakken bayani, amma lallai da ace wani abu makamancin hakan ya taba faruwa, da tuni labarin ya game duniya, musamman a wannan lokaci da hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani suka cika duniya.

Duk da haka, ina kyautata zaton yana ishara ne ga duniya ta tara mai suna: “Pluto.”  Wannan duniya ta Pluta dai da yawa cikin malaman kimiyyar sararin samaniya na kiranta da suna: “Dwarf Planet,” wato ‘yar wada.  Suna mata wannan kinaya ne saboda kankantanta.  Wannan ne ma yasa wasu ke ganin cewa wadannan duniyoyi guda takwas ne, ba tara ba.  A iya gajeren tunanina, ina ganin wannan shi ne dalilin da yasa malaminku yace su takwas ne, idan ka debe bayanin cewa daya ta bace.  Babu wacce ta bace, sai wacce take da kankantar da wasu ke ganin bata cancanci a kirata “duniya” (Planet) ba.  A iya ka’idojin malaman kimiyyar sararin samaniya, “duniya” ita ce duk wani jiki na mahalli dake cin gashin kanshi, wanda ke iya zagaye rana, wanda kuma bai dogara da wata duniyar ba, sannan kuma bai hada mahalli da wata duniya dake makwabtaka dashi ba.  Ta la’akari da wadannan ka’idoji ne yasa wasu ke ganin duniyar “Pluto” bata cika duniya ba.  Amma duk da haka ana kididdige ta, kuma tara ne su, ba goma ba.

Bayan wadannan duniyoyi shahararru, akwai a kusan duk shekara sai an gano wasu nau’ukan jiki na mahalli (Heavignly Bodies) a wajen wannan sararin samaniyar tamu, wadanda suke zaman kamar duniyoyi ne masu zaman kansu.  Ya zuwa yanzu dai an tantance sama da 1,700.  Don haka, idan kaji na cewa duniyoyin nan sun wuce tara, to, ka dauka yana la’akari ne da wannan kididdiga na wadancan duniyoyin dake wajen sararin samaniyar da wannan duniya tamu ke ciki.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: ina so in bude shafin sada zumunta na “Twitter”, amma ba ni da adireshin Imel. Shin, zan iya budewa ta wayata ko kuwa sai na je mashakatar lilo (Cyber Café)? Daga S. Haruna Shitu: 09034717632

Wa alaikumus salam, Malam Haruna barka dai.  Ba dole sai da adireshin Imel ba ake iya iya rajista a shafin Twitter.  Ko da lambar wayar salula za ka iya yi, in har wayarka tana iya hawa Intanet cikin sauki.  Amma duk da haka, in har kana mu’amala da ire-iren wadannan shafuka, yana da kyau kayi rajista din Imel, don sawwake al’amura, sannan ka adana bayanan akwatin Imel din.  Domin layin waya na iya samun matsala, ko wayar na iya mutuwa ba caji a lokacin da kake da tsananin bukatar canza wani abu a cikin wadannan wurare.

- Adv -

A takaice dai, kana iya rajista da lambar waya, amma bayan ka gama, sai ka bude Imel, sannan kaje bangaren “Profile” dinka a Twitter din, don shigar da adireshin Imel din.  Duk sadda ka mance “Password” dinka na hawa Twitter, kai tsaye za ka iya sa a turo maka hanyar da za ka warware matsalar ta Imel, wanda kana iya shiga don canzawa ko da a mashakatar lilo ne.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu  alaikum  Baban  Sadik,  don  Allah  ina  son  ka  turo  mini  da  bayanai  dangane  da  hanyoyin  da  zan  fara  koyon  ilimin  kwamfuta.  Ga addireshin Imel dina: hassanabdul2019@yahoo.com

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah nima ga Imel di na ina bukatar bayanai akan yadda zan kware a kan kwamfuta: kingabdulaziz409.ai@gmail.com

Wa alaikumus salam, barkanku dai, Malam Hassan da Malam Abdulaziz.  A kyakkyawan zatona ina ganin kuna ishara ne ga bayanan da nayi a makon jiya, sadda nake amsa tambayar masu son koyon ilimin gina manhajar kwamfuta.  A karshe na sanar da cewa akwai darussa da na fara a Facebook, kan ilimin gina manhajar kwamfuta, wato: “Programming.”  Wadannan kasidu ban fara tura wa jama’a ba, sai in kuna da shafuka a Facebook kuna iya ziyartar shafin Kimiyyar Sadarwa dake: www.facebook.com/zaurenbabansadik, don rika cin karo da wadannan kasidu da nake rubutawa a yadawa lokac-lokaci.   Wannan dangane da koyon ilimin gina manhajar kwamfuta kenan.

Amma idan koyon yadda ake amfani ko mu’amala da kwamfuta ne wajen kunnawa da kashewa da rubutu da taskance rubutun da kuma dabba’a shi, wannan kuma sai dai ince a nemi bayanai kan hakan a Intanet ko kuma aje makarantar da ake koyon hakan a aikace.  Kamar yadda na sanar a wancan mako, shi ilimin mu’amala da kwamfuta ilimi ne da ke tattare da kwatantawa.  Ni kuma a nan ina aiko da shawarwari ne ko bayanan da za su taimaka wajen kaiwa ga hakan, ba wai hakikanin abin nake karantarwa kai tsaye ba.  Kamar fannoni ne irin na likitanci, ba ka iya koyonsa a shafukan takarda ko littattafai, sai da malami.  Ina muku fatan alheri, kuma Allah yasa a dace, amin.  Da fatan kun gamsu.


Assalamu alaikum, da fatan kana lafiya, Baban Sadik don Allah ina so ka turo mini da bayanai kan yadda ake aiwatar da “Video Call”, a kuma aiko mini da kasidar nan kan tsibirin “Bermuda Triangle” ta Imel dina: khaleed121997@gmail.com, da fatan Allah ya kara basira.  Daga Khaleed Khan, Ban Zazzau, Zaria:  09039066203

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Khaleed.  Da farko dai, aiwatar da kira ta hanyar hoto mai motsi shi ake kira “Video Call.”  Wannan tsari yana gine ne cikin galibin manyan wayoyin salula na zamani da ake kira “Smartphones.”  Wadannan wayoyin salula suna dauke ne da na’urar daukan hoto (camera) guda biyu; da wacce ke baya, ta asali kenan.  Wannan da ita ake daukan hotunan da ake bukata.  Sai wacce keg aba, wacce ake kira: “Front Camera.”  Ita kuma da ita mai wayar ke iya daukan kansa da kansa, wato: “Selfie” kenan.  Galibin wayoyin salula masu kemara guda biyu za ka samu ana iya aiwatar da “Video Call” dasu, cikin sauki.

Idan wayarka ta cika wannan ka’ida, dole ne kuma wanda za ka kira ya zama shi wayarsa tana cika wannan ka’ida. Idan wayarsa irin tawa ce wacce ba ta iya aiwatar da wannan tsari, in ka kira zai iya ganin kiranka har ya daga, amma kai a naka bangaren ba za ka iya ganinsa ba, sai kaga duhu a shafin kemarar taka, ko wani sako da wayar za ta cillo maka, mai nuna cewa abokin zancenka ba ya iya aiwatar da wannan tsari.  Ba wani abu bane mai wahala.  Idan ka zabi lambar wanda kake son kira, da zarar wayar ta fara kira, akwai alamomi a jikin fuskar da wayar za ta budo maka su, musamman idan “Android” ce ko “Windows Phone” ko kuma “iOS”.  Da zarar abokin magananka ya daga kiran, za ka wani tambari mai dauke da hoto ko tambarin bidiyo, sai ka matsa; nan take za ka ganshi kai tsaye, kamar yadda shi ma nan take zai ganka.  Domin da zarar wayarsa ta fara kara sadda kake kira, a fuskarta zai ga sako dake nuna masa cewa wannan nau’in kira ne na bidiyo.  Yana dagawa shikenan, sai a budo masa fuskarka ko yana ganinka kai tsaye.  Wannan, a gajarce, shi yanda ake aiwatar da “Video Call.”  Da fatan ka gamsu.

Dangane da bukatarka ta biyu kuma, sai ka duba akwatin Imel dinka, na cillo maka kasidar.  Allah amfanar damu baki daya, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.