Sakonnin Masu Karatu (2017) (14)

A yau kuma za mu fara debo sakonninku daga jakar sakon Tes da kuka aiko ta wayar salula.  Watanni biyu da suka gabata mun shagaltu da sakonnin Imel ne.  Daga cikin sakonnin akwai wadanda maimaici ne, don haka ban amsa su ba.  Sannan masu sakonnin bukatar aiko kasidu ta Imel dinsu kuma su ma za su gafarceni.  Na daina aika sakonni ta Imel saboda samuwar TASKAR BABAN SADIK inda na zuba dukkan kasidun da suka gabata a baya.  Don haka duk wanda ke bukatar wata kasida ta musamman, yana iya hawa shafin don karantawa ko ma saukar da kasidar a kan waya ko kwamfutarsa, cikin sauki.  A sha karatu lafiya.

69

Salaamun alaikum, a bugun jaridar AMINIYA na 20 ga watan Disamba na ga ka yi bayani a kan rabe-raben duniya.  Shin, mu ‘yan adam a wace duniyar muke?  Shin, a sauran duniyar akwai halittu ne daban-daban?  –  Ibrahim Yarima Abban Khaliel, Abuja: 08067228825

Wa alaikumus salam Malam Ibrahim.  Muna duniyar da muke ciki mana, wacce a turance ake kira: “Earth.”  Wannan ita ce duniyar da muke rayuwa a cikinta, kuma ita ce ta uku a jerin duniyoyin da Malaman kimiyyar sararin samaniya suka gano.  Akwai duniyoyi shida a tsakaninmu da wata, ma’ana idan aka kwatanta bigiren da muke ciki da inda rana take kenan.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya kai da abokan aikinka.  Allah yasa haka amin.  Bayan haka, tambayata ita ce, wai me yasa idan zan saukar da wani abu daga wata cibiyar “Play Store” akan wayata ta Android sai in shafe kusan awa guda abin bai sauko ba.  Wai me yake kawo wannan jinkirin ne?   – 08064942376

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Wannan dalili yana da alaka ne da karfi ko rashin karfin siginar Intanet a wayarka.  Ko dai ya zama daga bigiren da kake ne, ko kuma daga kamfanin wayarka, ko kuma, a karo na karshe, daga wayarka matsalar take.  Kana iya samun wannan matsala sanadiyyar rashin karfin siginar Intanet a kamfanin wayarka.  Wannan dalilin ba ka da wani abin yi a kai, domin ya wuce karfinka.  Sai dai in canza layin za ka yi.  Idan matsalar daga bigiren da kake ne, watakila a unguwar da kake siginar sadarwar kamfanin wayarka ba shi da karfi.  A nan kam sai dai ka canza bigire zuwa wani bigiren daban, ko ka canza wani layi na wani kamfani daban dake da karfin siginar sadarwa a inda kake.

A daya bangaren kuma, matsalar na iya zama daga wayarka, musamman idan karamar waya ce, wacce take tsohuwar yayi.  Bayan wannan duk, mizanin manhajar da kake kokarin saukarwa ma na iya haddasa hakan, amma bai kamata ya zama kowane lokaci ba.  Sai lokacin da kake kokarin saukar da manhaja mai babban mizani.

- Adv -

Shawara a nan ita ce, ka tabbata kana da isasshen “data” a wayarka, sannan ka rika lura da lokacin da kake da siginar sadarwa ta waya mai karfi kafin kokarin saukar da manhaja daga wannan cibiya.  Idan babu sigina mai inganci, kamar yadda kake gani, babu abin da za ka iya saukarwa.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, tamabayata ita ce, na canza “Password” dina na Facebook kuma na manta sabon da nasa.  Ga shi kuma layin wayar da na bude shafin dashi ya bata!  Yanzu da zarar na yi kokarin hawa, sai a jefo ni waje.  Don Allah yaya zan yi in gano sabon “Password” din da na canza?  –  Abubakar Haruna, Mile 12, Lagos: 08164048916

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abubakar, babana.  Abin da wannan ke nunawa dai shi ne, kana amfani da tsohon “Password” ne ko kuma ba ka sanya sabon da ka canza, daidai.  Wannan kuwa zai sa a hana ka hawa ma gaba daya.  A ka’idar sadarwa a shafin Facebook, dole sai ka shigar da hakikanin suna (adireshin Imel ko lambar waya, ko “Facebook ID”) na shafinka, tare da hakikanin “Password” da ka canza ko zaba a sadda kake bude shafin, sannan a baka hanya ka hau shafinka.

Idan ka gagara bayar da wadannan bayanai yadda suka kamata, akwai inda ake baka dama ka canza ‘Password’ din, in dai shafin naka ne.   Wannan ita ce kadai mafita.  Amma in ba haka ba, babu yadda za ayi ka sake samun wancan tsohon “Password” din ko kuma sabon da ka mance shi.

Yana da kyau ka san cewa, sadda kayi rajistan shafin, an tambayeka “Password” din da kake so, kuma ka zaba.  Sadda ka zaba din nan, kana shigar da “Password” din, nan take za a layance shi zuwa wasu jerin haruffa masu tsayi.  Wannan shi ake kira: “Password Hashing.”  Daga lokacin nan, duk sadda kazo hawa shafinka, da zarar ka shigar da “Password”, manhajar runbun adana bayanan Facebook za ta kalli abin da ka shigar, sai ta gwama shi da wancan “Password” din farko da ka shigar.  Idan sunyi daidai, sai a baka dama ka isa zuwa shafin.  Idan kuma basu dace da juna ba, sai ace maka: “Username or Password incorrect.  Try again.”

Tunda ka daina amfani da layin wayar da kayi rajista dashi a farko, in har akwai Imel a kan “Profile” dinka, kana iya matsa inda aka rubuta: “Forget Password?” don ka canza “Password” dinka.  Idan ka matsa wurin, za a aiko maka rariyar da za ka bi ne, don canza “Password” din a akwatin Imel dinka.  Idan kuma, sanadiyyar tsautsayi baka sanya Imel a shafin ba, to, a wannan yanayin zai yi wahala su baka damar canzawa, saboda rashin tantancewa.  Sai dai ka bude wani sabon shafi kawai.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.