Ziyarar Gidajen Yanar Sadarwa (2)

Wannan mako za mu leko gidan yanar sadarwa na Kanoonline, wanda jihar kano ta dauki nauyin ginawa da tafiyar dashi. A sha karatu lafiya.

265

KANOONLINE.COM (http://www.kanoonline.com)

A yau ga mu tsundum cikin birnin Kano; Ta-Dabo Ci-gari; gari ba Kano ba dajin Allah; Yaro ko da me ka zo an fi ka!  Cikin ziyarar da mu ka fara kaiwa wasu gidajen yanar sadarwa da ke giza-gizan sadarwa ta Intanet, a yau za mu kashe yini ne a zauren KANOONLINE.COM, shahararren gidan yanar sadarwan da aka tanada musamman, don taimaka ma dukkan mai neman sanin wani abu dangane da birnin Kano da ke arewacin Nijeriya.

Gidan Yanar, Kacokan

 

 

Wannan gidan yanar sadarwa na Kanoonline, kayataccen gida ne irin na yanar sadarwa, wanda aka gina shi da kwarewa irin ta fasahar gina gidan yanan sadawa na zamani, wato Web Progamming Techniques.  Daga cikin fasahar da aka yi amfani dasu akwai Java Script, wanda ya taimaka wajen kawata haruffa da hotunan da mai ziyara zai ta cin karo dasu.  Idan ka matsa rariyar likau (Web Link) a Kanoonline, za ka ga haruffa na wani laushi da laudi, suna canza kama, kamar sa maka Magana ko dariya.  Wannan shi ake kira Mouse Over, kuma duk da fasahar Java Script  ake tsara su.  Sai kuma fasahar Cascading Style Sheets,   ko kace CSS a takaice.  Shi ma wani gajeren dabara ne da ake amfani da shi wajen gyatta zaman bayanai a gidan yanar sadarwa, musamman wajen abin da ya shafi tsarawa da shirya launin haruffa da ajiye bayanai a irin bigiren da ake so, a ko ina ne cikin daki ko zauren gidan yanar sadarwa.

Har wa yau, maginin wannan gidan yanar sadarwa na Kanoonline yayi amfani da hanyoyin saukaka ma mai ziyara fita ko shiga wani shafi daga wani.  Duk shafi ko dakin gidan yanan da ka shiga a cikin gidan, za ka samu alamar da za ta riskar da kai zuwa wani dakin ko kuma ka dawo zauren gidan gaba daya.   Sannan, da zarar ka shigo zauren (Home Page), abin da za ka fara cin karo da shi shi ne wani kafcecen tambarin KANO, tare da taswiran jihar gaba daya (Map), daga hannun hagu a sama.  A kasan tambarin ne za ka ci karo da agogon da ke sanar da kai ko karfe nawa ne yanzu a birnin Kano!  Tirkashi!  Wani aikin sai Kanawa.  Za ka ga lokaci da kuma kwanan wata duk a nan (Date and Time).  Daga can kuryan dama kuma, za ka sake cin karo da bayanai kan layin bigiren da Kano ke kai, a taswiran duniya (Longitude and Latitude).  Daga nan sai maginin gidan ya raba gidan zuwa kashi uku, daga sama zuwa kasa.  Daga bangaren farko daga hannun hagu, sai tsakiya, da kuma bangaren karshe daga dama.  To me ke zube cikin wannan gida ne?

Me Ke Ciki?

Kamar gidan yanar sadarwa ta Gamji, Kanoonline na makare ne da bayanai da hotuna masu motsi da marasa motsi da sauti da kuma taswirori.  Bayanan sun hada da kasidu da mujallu da makaloli da littafai da kuma manhajojin da ke taimaka ma mai ziyara aiwatar da wasu ayyuka.  Akwai kuma hotunan birnin Kano, da hotunan Dogarawan Kano da kuma hotunan Badala/Ganuwa da dai sauransu.  Sai dai galibin wadannan hotuna a makale suke a matsayin tambari (banners) da ke shafuka daban-daban a dakunan gidan gaba daya.  Akwai kuma sauti na karatuttukan tafsirin Malam Isah Waziri, Marigayi Malam Lawal Kalarawi, Marigayi Malam Nasiru Kabara, Marigayi Malam Bashir Dandago, da kuma wakokin Imfiraji da wata baiwar Allah ta wake su.  Akwai kuma Marigayi Malam Bala Mai Yafe, in da yake wake Al-Burdah.  Kana shigowa zauren Kanoonline, a tsakiya za ka ci karo da: AS SALAAMU ALAIKUM!  A kasan sa kuma akwai sanarwa da ke sanar da masu ziyara cewa wannan gidan yanar sadarwa da bayanan da ke jibge ciki ba mallakin gwamnatin Jihar Kano bane.  Kana kara gangarawa kuma za ka cin ma takaitaccen bayani kan Birnin Kano.  Wannan bangaren tsakiya kenan, na gidan yanar sadarwan.

Idan ka yi bangaren hagu kuma, za ka fara cin karo ne da Tools, manhajoji ne a wajen.  Idan kana son aikawa da adireshin Imel dinka, don a rika aiko maka bayanai kai tsaye, sai ka mika a Join Our Mailing List. A wannan bangare za ka samu bayanai kan wasu garuruwa ko ince takwarorin Kano, a kasashe irin su Rasha, Congo Democratic Republic, Japan, Nijer, Hungari, Chadi.  Akwai garuruwa masu suna “Kano” a dukkan wadannan kasashe.  Daga nan za ka samu manhajar da za ta taimaka maka wajen auna mizani ko kimar kudade tsakanin Nairan Nijeriya da sauran kudade (Currency Converter).  Kasa da shi kuma sai tambarin Kungiyar Inuwar Jama’ar Kano (Kano Forum), wacce ke daukan nauyin tafiyar da gidan yananDaga nan kuma sai bayanai kan Gidan Makama, wato gidan tarihi da ke Kano, sai bayanai kan Ganuwar Kano.  Daga nan sai aka jero rariyar likau na wasu gidajen yanar sadarwan, irinsu Gamji, Dandali, Gwamnatin Jihar Jigawa, Arewaonline, Association of Nigerian Authors (ANA) da kuma British Council.  Wadannan su ne ababen da ke bangaren hagu a zauren gidan yanan.

- Adv -

A bangare na karshe kuma, wanda ke hannun dama, nau’ukan bayanan da ke ciki sun hada da kasidu (articles), littafai, mujallu, zauren hira da tattaunawa (Discussion Forum), wakoki na kafiya (poems) da kuma jakunkunan sauti na tafisiri da wakokin Imfiraji (kamar yadda bayani ya gabata a sama).  Har wa yau, a wannan bangare ne ake da cikakken bayani kan adadin jama’ar da ke Kano, da adadin Bankunan da ke Kano, da adadin asibitocin da ke Kano, da adadin hadarurrukan jirgin sama da aka yi a Kano, da kuma adadin wadanda suka shugabanci Kano a matsayin Gwamnoni, da kuma adadin Kananan Hukumomin da ke Jihar gaba daya.  A kasa da wadannan kuma akwai kasidu da aka tara, wadanda kuma galibinsu sun ta’allaka ne da jihar Kano gaba daya, kan abin da ya shafi hanyoyin sadarwa, ilimi da sauransu. Dukkan wadannan bayanai za ka same su a bangaren hannun dama, da zarar ka shigo zauren. To wa ke tafiyar da wannan gidan ne?

Uban Gidan Gaba Daya

Wannan gidan yanar sadarwa an gina shi ne a shekarar 2001, ranar 23 ga watan Agusta.  Kuma duk da cewa wasu mutane hudu ne suka hada kai wajen wannan aiki na alheri, daya daga cikin su ne ya gina gidan gaba daya, a aikace nake nufi.  Wadannan mutane kuwa su ne: Farfesa Abdallah Uba Adamu (Jami’ar Bayero, Kano), Malam Salisu Danyaro Soron-Dinki (Amurka), Malam Ibrahim Ado Kurawa (Cibiyar Binciken Ilimi, Kano), da kuma Malam Adamu Yusuf.  Wadannan mutane shahararru ne, ba a Nijeriya ko arewancinta kadai ba, har a sauran kasashen duniya.

Farfesa Abdallah Uba Adamu ne mai Majalisar Fina-finan Hausa da ke Intanet, da ma sauran majalisu.  Kusan duk wanda ya riski fasahar Intanet a arewacin Nijeriya, ina da yakinin cewa da hannunsa a ciki, hatta masu karanta wannan shafi, da shi kanshi abin da ke rubuce a wannan shafi.  Duk sanadiyyar sa ne muka samu riskuwa da wannan bakuwar hanyar sadarwa.  Malam Salisu Dan Yaro kuma mutumin Soron-Dinki  ne da ke Birnin Kano, yana kuma zaune ne a kasar Amurka.  Shi ne ya gina wannan gidan yanar sadarwa na Kanoonline, domin masanin kwamfuta ne da manhajarta, na gaske kuwa.  Shi ne mai gidan yanar sadarwan Dandali.com, mai dauke da al’adun Hausa kai kace a kasar Hausa kake.  Wadannan bayin Allah hudu ne ke tafiyar da wannan gidan yanar sadarwa, duk da yake suna samun agaji daga Inuwar Jama’ar Kano (Kano Forum), wajen hakan.  Mutane ne masu son ci gaban al’umma ta hanyar ilimi.  Duk wanda Allah Ya hada ka dashi daga cikinsu, zai yi wahala ka yi nadama, muddin agaji kake nema ta hanyar ilimi da abin da ya shafe shi.  Ina da shaida mai karfi a kan haka.

Manufa

Duk da cewa mai ziyara ba zai ga in da aka sanar dashi manufar gina wannan gidan sadarwa ba, manufar a fili take;  ilimantar da duniya kan kasar Kano da jama’arta da kuma kasan Hausa gaba daya.  Har wa yau, daga cikin manufarsu akwai karuwa da juna ta hanyar ilimi.  Sai ka shiga Majalisar Tattaunawarsu za ka fahimci hakan.  Wadannan manufofi sun isa a matsayin hujja wajen nuna damuwarsu kan halin da al’umma take ciki.  Suna ganin babu al’ummar da za ta ci gaba, muddin ta mance al’adunta da addininta, har abada.  Allah saka musu da alheri, amin.

Shawarwari

Kafin mu karkare, yana da kyau mu mika shawarwarinmu ga masu lura da wannan gida, don kamar yadda Hausawa ne ke fadi – kogi bai kin dadi.  Akwai wasu dakuna (Web Pages), da ke da ‘yan matsaloli, kasancewar suna dauke  ne da makaloli masu amfani, ya kamata a duba su, don taimaka ma masu ziyara samun saukin isa garesu.  Na samu Error 404, yayin da nayi kokarin shiga dakunan da ke dauke da wadannan kasidu: 1) Telecommunication in Kano, 2)Sharia Law and Western Reaction, 3) Sickle Cell Desease.  Bayan nan, zai dace a rika dora sabbin wakoki a sashen ANA, ganin cewa duk karshen wata suna fid da sabbin wakoki kan al’amura daban-daban masu amfani.  Domin wakokin da ke nan duk na baya ne, a iya zuba su a rumbu, a mayar da makwafinsu.  Akwai kuma matsala wajen sauraron jakunkunan sautin karatuttukan da aka sanya da wakokin Imfiraji.  Basu budowa, kuma ga alama ina ganin Broken Links ne.  zai dace a gyara musu zama don amfanin masu ziyara.  Shawara ta karshe kuma ita ce, in da hali (na san ba abu ne mai sauki ba, musamman ga mai lura da gidan yanar sadarwa irin wannan) a budo wani sashe na labaru zalla, kan Kasar Kano, in da mai ziyara zai samu sabbin labaru kan abin da ke faruwa a wannan gawurtaccen birni mai cike da dimbin albarka.  Allah kara taimakawa, Ya kuma sa wannan aiki a mizanin ayyukanmu baki daya, amin.

Sababbin Mudawwanai

Kamar yadda muka sanar, wasu sun fara aiko da adireshin Mudawwanan da suka gina, kuma har sun ma fara watsa ra’ayoyinsu tuni.  Akwai Malam Shehu Mustapha Chaji, za a same shi a http://shehuchaji.blogspot.com.  Sai kuma Malam Muntaka Abdul-Hadi, wani Bazazzagi, shima za a sameshi a http://anguwarfatikaonline.blogspot.com.  Na san akwai ‘yan uwa da ke hankoron ginawa, kada a mance, a aiko za mu sanar da yardan Allah.  Daga karshe, ina mika godiyata ga dukkan masu bugo waya ko aiko da sakon text ko Imel.  Na gode!

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Salihu Aminu Sai'd says

    Allah ya kara Basira Malam. Babu Abin da zamu ce sai dai godia tabbas muna qaruwa da wannan taskar, Allah ya saka da mafificin Alkairi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.