Sakonnin Masu Karatu (2017) (13)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

98

Baban Sadik barka da wannan lokaci. Da gaske ne a duniyar wata da jan-kafa ake tafiya ba a daga kafa? Kuma da gaske ne cikin watan ake shiga idan aka je duniyar watan?  nasirukainuwahadejia1@gmail.com

Malam Nasiru barka ka dai.  Da farko dai yana da kyau kasan cewa wannan duniya tamu ba ta da wani tauraro na asali (Natural Satellite) da ya wuce Wata, kuma idan aka kwatanta shi da girman duniyar, kusan shi ne tauraron asali da yafi girma a dukkan Taurarin Asali da ke gewaye da sauran duniyoyin da ke makwabtaka damu.  Shi Wata ba shi da hasken da yake kyallarowa na kansa, sai dai ya lakato haske daga rana a yayin da take nata shawagin, idan ta juya mana baya kuma muka shiga dare ko duhu, sai ya hasko mana wannan haske.

Kamar wannan duniya tamu da sauran duniyoyi ko halittun da ke sama, Wata a cure yake, ko ince a mulmule.  Bangaren dake fuskanto mu a lokacin da yake shawagi, shi ake kira The Near Side”, a turancin Kimiyyar Sararin Samaniya.  Wannan bangare ne ke darsano hasken rana don haskaka duniyarmu.  Kuma an kiyasta cewa darajar zafin dake wannan bangare ya wuce digiri dari da talatin da bakwai a ma’aunin zafi na santigireti (wato 1370C).  Dayan bangaren dake shiga duhu kuma daga baya, shi ake kira The Far Side”.  Amma kuma sabanin bangaren farko, wannan bangare bai da zafi sai sanyi mai tsanani.  An kiyasta sanyin wannan bangare na Wata cewa ya kai dari da hamsin da shida a kasa da mizanin zafi (wato -1560C). 

Binciken baya-bayan nan da aka yi ya tabbatar da cewa halittar Wata na dauke ne da duwatsu nau’uka daban-daban, da sinadaran kimiyya masu inganci irin wadanda ba mu dasu a wannan duniya tamu.  Kari a kan haka, jikin Wata, inji masu wannan bincike, kamar gilashi yake wajen mu’amala da haske; duk ta inda ka cillo haske, zai dauka, ya kuma cilla hasken zuwa inda yake fuskanta.  Kamar dai yadda gilashi ke yi idan ka cilla masa haske.  Wannan yasa idan rana ta cillo haskenta, sai Wata ya dauka, ya kuma cillo hasken zuwa wannan duniya tamu, kasancewar shi ne tauraron mu.  Allah Buwayi gagara misali!

Ba nan aka tsaya ba, babu iska balle guguwa a duniyar Wata.  Wannan yasa duk inda ka taka a saman Wata, gurabun sawunka zasu ci gaba da kasancewa a wurin, tsawon zamani.  Har zuwa yau akwai gurabun takun wadanda suka ziyarci duniyar Wata tun shekarar 1969 a Kumbon Apollo 11.  A karshe, akwai buraguzan taurarin da rayuwarsu ta kare (wato Meteorite) masu shawagi a saman Sararin Samaniya, wadanda kuma ke shigowa wannan duniya tamu lokaci-lokaci.  Ire-iren wadannan buraguzai ne ke afkawa cikin Wata a lokuta daban-daban, iya gwargwadon girmansu.  Don haka Malaman Kimiyyar Sararin Samaniya suka ce galibin ramuka da tsagan da ke jikin Wata sun samo asali ne sanadiyyar illolin da wadannan buraguzai masu shawagi a can sama ke yi a saman Wata.

Bayanan da suka gabata na tabbatar da cewa wannan mahalli da Wata yake, mahalli ne da yanayinsa da dabi’unsa suka sha bamban  da wanda muka saba dashi a wannan duniya tamu.  Don haka yanayin tafiya ya sha bamban da yadda muke tafiya a wannan duniya.  Domin a wannan duniyar akwai iska dake kadawa iya gwargwadon yadda ya dace da rayuwarmu.  Shi yasa ma malaman kimiyya suka ce, bayan sun gudanar da bincike na kwakwaf kan ko za a iya samun wata duniya wacce dabi’u da yanayinta suke daidai da wannan duniyar tamu, amsar ita ce a a.  kuma wannan ke tabbatar maka da cikakkiyar hikimar Ubangiji da kudurarsa da gamewar iliminsa wajen halitta da tafiyar da ita. Inda ya zaunar damu a wannan duniya, wadda ita ce ta dace damu, ta la’akari da rayuwarmu.  Yadda bature yak ware wajen binciken kimiyya da fasahar kere-kere, ta la’akari da inkarin da yake wa samuwar Ubangiji, da ace akwai wata duniyar da dan adam zai iya rayuwa cikinta kamar yadda wannan duniyar take, komai da komai iri daya, da tuni bature ya fara tunanin komawa wata duniyar don sake gudanar da rayuwa.

Amsar tambayarka ta cewa ko idan suka je suna shiga cikin watan ne, a a.  Bayanan da suka gabata kadai sun isa su tabbatar maka cewa halittar Wata curarriyar halitta ce, ba wai kogo bane; babu koguna a jikin Wata, sai dai alamun buraguzan dake fadowa cikinsa lokaci-lokaci daga sararin samaniya.

- Adv -

Wannan shi ne dan abin da ya samu na jawabi. Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, idan mutum ya saukar da wasu bayanai (downloding) daga shafin Intanet, abin da aka dauko sunansa sai ka ga ya koma lambobi ratata, wani abin kuma da sunan da lambobin za ka ga a hade. Haka abin da aka turo ta Whatsapp shi ma sunansa ya kan koma lambobi.  Mene ne ke jawo haka? Kuma lambobin lissafin me suke nunawa?  nasirukainuwahadejia1@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Nasiru, barka dai.  Da farko dai yana da kyau ka san cewa wannan ya kebanci manhajar Whatsapp ne, ba wai haka abin yake a ko ina a Intanet ba.  Idan ka saukar da kasida ko wata manhaja daga wani shafin Intanet, sunan da mai shafin ya bai wa manhajar ko jakar bayanin, shi ne zai bayyana a yayin da k agama saukar dashi a kwamfuta ko wayarka ta salula.  In har kaga wani canji to, watakila baka gama saukar da manhaja ko jakar bayanin bane gaba daya sai siginar Intanet ta dauke.  In haka ta faru, baza ka ga sunan jakar bayani ko manhajar ba sai dai wasu sunaye masu wahalar fahimta da ganewa.  Wannan kuwa ya faru ne sanadiyyar alakar dake samuwa tsakanin kwamfuta ko wayarka ta salula da kuma kwamfutar da kake saukar da manhajar daga gare ta.

A duk lokacin da ka bukaci saukar da wani bayani zuwa kan kwamfuta ko wayarka ta salula, da zarar an gama “gaisawa” da gane juna tsakanin kwamfutarka da dayan kwamfutar, nan take sai wacce ake bukatar bayanan daga gareta ta miko bayanan.  Tana mikowa ita kuma wacce ke bukata za ta karba.  Idan ta fara karba ba wai a ma’adanar da ka ayyana za ta fara ajiye maka ba.  Akwai wuri da ake kira: “Temporary Folder” mai suna: “tmp” ko “temp” a kwamfuta ko wayarka.  A wannan jaka ne bayanan ke fara sauka.  Da zarar kwamfutar ko wayar ta gama karban bayanan duka, babu ragowa, sai ta ajiye maka a inda ka tanada don a rika ajiye maka, watakila: “Donwload” folder misali.  A sannan ne za ka ga cikakken sunan manhajar ko jakar bayanin.  Wannan a al’adance kenan.

Amma a bangaren manhajar Whatsapp abin ya sha bamban.  A duk sadda wani ya aiko maka sakon bidiyo ta Whatsapp, ko da ya baiwa sakon suna na musamman, to, manhajar Whatsapp za ta canza komai ta goge shi, sai wanda ta baiwa sakon za ka iya gani.  Misali, idan sakon ya iso kana iya ganin lambobi da bayanai kamar haka: VID-20170710-WA0002.mp4.  mu bi su dalla-dalla.  Bangaren farko, wato: VID, yana nufin sakon na bidiyo ne.  bangare na biyu, wato: 20170710, wannan kuma kwanan wata ne, a tsarin rubuta kwanan wata na kasar Amurka.  Suna farawa da shekarara, sai wata, sai kuma ranar da sakon ya iso.  Bangare uku, wato: WA, yana nuna sakon daga manhajar Whatsapp ne. sai bangare na karshe, wato: .mp4, wannan kuma nau’in jakar bayanin ne, wanda ke nuna cewa bidiyo ne.  idan sakon sauti neko murya, zai bayyana kamar haka:  AU-20170710-WA0002.mp3.  Haruffa biyu na farko, wato: AU, na nufin “Audio” ne, wato sauti.  Idan kuma hoto ne, zai bayyana kamar haka:  IMG-20170710-WA-002.jpg.  Haruffa biyun farko, wato: IMG na nufin “Image” ne, wato hoto.  Wannan shi ne tsarin da kamfanin Whatsapp ke bi wajen aikawa da karban sakonni.

Ta bangaren sakonnin sauti akwai lokacin da idan ka shiga manhajar sauraron sauti a wayarka za ka iya ganin taken wasu bayanan sautin kai tsaye, wasu lokuta ma har da hotuna.  Mai karatu na iya cewa to yaya akayi haka kuma?  Da farko dai, wadannan bayanai su ake kira: “Metadata,” wato bayanan bayanai kenan, in ka gane.  Wannan na nuna cewa a lokacin da aka taskance sautin, anyi amfani da wata manhaja don rubuta taken darasin (ba wai sunan jakar sautin ba), wannan shi ake kira: “Genres”, da wanda yayi laccar, wato: “Artist”, da kuma jerin taken silsilar darasin ko waken, wato: “Album”.  Idan har anyi wannan, to ko da manhajar Whatsapp ta canza sunan jakar bayanin, idan kaje manhajar sauraron sauti, zaka iya ganin wadancan bayanai, amma ba sunan jakar sautin ba.

Kamfanin Whatsapp na da nasu dalilai da suka sa suke wannan canji, daga ciki akwai dalilai na tsaro.  Sai kuma maslaha ga mai waya, ta yadda za ka iya bambance sakonnin da suka shigo wayarka ta Whatsapp da wadanda aka aiko maka ta Bluetooth ko Imel ko wasu hanyoyi.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. BABAJO A BAWA SAMINAKA says

    Assalam baban sadiq ina da tambaya wai da gaske akwai wasu halitta awata duniya sunan su aliyes musan karin bayani

Leave A Reply

Your email address will not be published.