Sakonnin Masu Karatu (2017) (1)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

76

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina maka fatan alheri. Tambayata ita ce: shin, yaya duniyar wata take? Kuma ka turom cikakken bayani ta wannan adireshin Imel: abdulmalikhassan994@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdulmalik, da fatan kana lafiya.  Shi Wata, ko Moon a turance, shi ne Tauraron Asali (Natural Satellite) da wannan duniya tamu ta mallaka, kuma yake gewaye ta, tare da halittar rana.  Malaman Sararin Samaniya sun yi hasashen cewa a kalla halittar Wata ta yi shekaru biliyan hudu ko sama da haka, tun samuwarta.  Wata kan kare gewaye wannan duniya tamu ne cikin kwanaki ashirin da biyar da rabin rana (25.5days), amma idan aka hada da gibin kwanakin da yake kashewa a halin shawaginsa a falakin rana, sai ya yi kwanaki ashirin da tara da rabin kwana (29.5days) yake gama gewaye daya.

Kamar yadda bayanai suka gabata, wannan duniya tamu ba ta da wani Tauraro na Asali (Natural Satellite) da ya wuce Wata, kuma idan aka kwatanta shi da girman duniyar, kusan shi ne Tauraron Asali da yafi girma a dukkan Taurarin Asali da ke gewaye da sauran duniyoyin da ke makwabtaka damu.  Shi Wata ba shi da hasken da yake kyallarowa na kansa, sai dai ya lakato haske daga rana a yayin da take nata shawagin, idan ta juya mana baya kuma muka shiga dare ko duhu, sai ya hasko mana wannan haske, kamar dai yadda bayanai suka gabata a kasidun baya.

Kamar wannan duniya tamu da sauran duniyoyi ko halittun da ke sama, Wata a cure yake, ko ince a mulmule.  Bangaren dake fuskanto mu a lokacin da yake shawagi, shi ake kira The Near Side, a turancin Kimiyyar Sararin Samaniya.  Wannan bangare ne ke darsano hasken rana don haskaka duniyarmu, kuma an kiyasta cewa darajar zafin dake wannan bangare ya wuce digiri dari da talatin da bakwai a ma’aunin zafi na santigireti (wato 1370C).  Dayan bangaren da ke shiga duhu kuma daga baya, shi ake kira The Far Side.  Amma kuma sabanin bangaren farko, wannan bangare bai da zafi sai sanyi mai tsanani.  An kiyasta sanyin wannan bangare na Wata cewa ya kai dari da hamsin da shida a kasa da mizanin zafi (wato -1560C). 

Binciken baya-bayan nan da aka yi ya tabbatar da cewa halittar Wata na dauke ne da duwatsu nau’uka daban-daban, da sinadaran kimiyya masu inganci irin wadanda ba mu dasu a wannan duniya tamu.  Kari a kan haka, jikin Wata, inji masu wannan bincike, kamar gilashi yake wajen mu’amala da haske; duk ta inda ka cillo haske, zai dauka, ya kuma cilla hasken zuwa inda yake fuskanta.  Kamar dai yadda gilashi ke yi idan ka cilla masa haske.  Wannan tasa idan rana ta cillo haskenta, sai Wata ya dauka, ya kuma cillo hasken zuwa wannan duniya tamu, kasancewar shi ne tauraronmu.  Allah Buwayi gagara misali!   Ba nan aka tsaya ba, babu iska balle guguwa a duniyar Wata.  Wannan tasa duk inda ka taka a saman Wata, gurabun sawunka zasu ci gaba da kasancewa a wurin, tsawon zamani.  Har zuwa yau akwai gurabun takun wadanda suka ziyarci duniyar Wata tun shekarar 1969 a Kumbon Apollo 11. 

- Adv -

A karshe, akwai buraguzan taurarin da rayuwarsu ta kare (wato Meteorite) masu shawagi a saman Sararin Samaniya, wadanda kuma ke shigowa wannan duniya tamu lokaci-lokaci.  Ire-iren wadannan buraguzai ne ke afkawa cikin Wata a lokuta dabam-daban, iya gwargwadon girmansu.  Don haka Malaman Kimiyyar Sararin Samaniya suka ce galibin ramuka da tsagan da ke jikin Wata sun samo asali ne sanadiyyar illolin da wadannan buraguzai masu shawagi a can sama ke yi a saman Wata.  Wannan shi ne dan abin da zai samu na bayanai kan yanayin da Wata ke rayuwa a ciki.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da aiki.  Ko akwai hanyar da ake bi wajen kara wa kwamfuta sauri wajen kwafo bayanai ko kuma wajen aikawa da bayanai daga cikinta zuwa ma’adanar “Memory Card” da sauransu? Nasiru Kainuwa Hadejia: 08100229688, naseeryaaky@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Sauri wajen aikawa ko karban sakonni tsakanin na’urorin sadarwa irin su kwamfuta, ko ma’adanar wayar salula ko ma’adanar kwamfuta da sai sauran ire-iren su, ya danganci yanayin mahallin da ke karba ne ko aikawa.  Misali, idan tsakanin kwamfuta da kwamfuta ne, a nan ma ya danganci ingancin babbar manhajar dake aikawa da na wacce ke karba.  Haka idan tsakanin kwamfuta ne zuwa wayar salula ko ma’adanar wucin-gadi na wayar salula, wato: “Memory Card.”

A takaice dai, idan za ka aika sakonni daga kwamfuta zuwa ma’adanar “Memory Card,” dole za ka samu tsaiko, domin mahallin na’urorin ba daya bane.  Sakonnin za su yi saurin fita ko sauka daga kwamfuta, amma wajen karbarsu za a samu tsaiko, domin ma’adanar dake karba kuntatacciya ce.  Bayan karancin girma, fasahar da aka kera ma’adanan ba daya bane.  Fasahar ma’adanar kwamfuta ta fi inganci sama da fasahar ma’adanar wayar salula.  Abu na karshe shi ne yawan sakon da ake aikawa ko karba.  Idan sakon na da yawa, za a kara samun wani tsaikon kuma.

Domin kafin aikawa ko karban sakonni daga wata ma’adana zuwa wata ma’adana, sai na’urar ta kacalcala sakon zuwa tsibi-tsibi, don aikawa dasu a lokaci daya, daban-daban.  Da zarar sun isa masaukinsu, sai su hade wuri guda, kamar yadda suke a wancan ma’adanar da ta aiko su.  In kuwa haka ne, ba maganar ta yaya za a iya kara wa kwamfuta gudu wajen aikawa da sakonni daga gareta zuwa wata ma’adana daban, musamman ma’adanar wucin-gadi.  In akwai wacce za a kara wa sauri ita ce ma’adanar “Memory Card” din, wanda kuma ba abu bane mai yiwuwa.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Nasiru Kainuwa Hadejia says

    Baban Sadik Allah Ya Kara Basira.

Leave A Reply

Your email address will not be published.