Sakonnin Masu Karatu (2010) (9)

Yau ma zamu dan waiwaiya kwandon wasikunku don amsa wasu daga cikin sakonninku. A sha karatu lafiya.

85

Karshen Zango

Bayan tsawon lokaci muna ta kwasan darussa iya gwargwado, a yau za mu karkare wannan marhala a daidai lokacin da ake bikin karamar sallar wannan shekara.  Hakan na da muhimmanci don sake tsara wata alkibla kuma a marhalar da ke tafe.  Kafin mu yi nisa, shafin Kimiyya da Kere-kere na taya dimbin dalibansa murnar bikin salla.  Allah Ya sa ayyukan da muka gabatar cikin watan Ramadana karbabbu ne, ya kuma isar da mu wannan wata mai albarka cikin shekarar da ke tafe lafiya, amin.

Kada a mance, a caja wayoyin salula sosai, a zuba kudi a ciki, a sadar da zumunci (kada a mance a aiko sakonnin zumunci zuwa shafin Kimiyya da Kere-kere), sannan kuma, kowa ya lura da wayarsa. Domin masu satar wayoyin salula sun fi zage damtse lokacin bukukuwa, don sun san mutane a shagalce suke a lokacin.  A kira ‘yan uwa da abokan arziki, a aiko sakonnin text masu dauke da dadadan kalmomin zumunci da kaunar juna.

Da zarar mun dawo hutun salla, za mu ci gaba da gabatar da jawabai kan fannonin kimiyya iya gwargwadon hali.  Muna mika sakon gaisuwa da godiya ga dimbin masu karatun da ke bugo waya a lokuta daban-daban don tambaya ko neman Karin bayani ko nuna gamsuwa.  Dangane da masu aiko sakonnin text kuma, muna mika godiya garesu, musamman masu aiko sakonnin godiya da gamsuwa.  A halin yanzu ga sauran sakonnin text da suka saura a jakar wayar salula ta zan amsa.  Wadannan sakonni da zan amsa dai sakonnin ne da ba su dauke da maimaici.  Duk wadanda suka rubuto sakonnin neman Karin bayani kan abin da muka sha tattauna shi a shafin, sai dai su yi hakuri.  Domin kamar yadda na sanar ne a shekarar da ta gabata, cewa idan muka ce za mu yi ta amsa ire-iren wadannan tambayoyi – musamman kan tsarin amfani da Intanet a wayar salula ko yadda ake shiga Facebook – to za mu wayi gari muna ta gewaye ne a waje daya.  Duk wanda bai ji sakonsa ba, to ya yi hakuri. A halin yanzu ga wadannan sakonnin neman Karin bayani nan.


Assalaamu Alaikum, yaya kokari?  Ina son Karin bayani a kan EMS, MMS, da kuma SMS.  – Khaleel Nasir Kuriwa Kiru: 07069191677

Malam Khaleel barka da war haka kuma da fatan an yi salla lafiya. Abin da jerin haruffan “EMS” ke nufi shi ne “Enhanced Message Service”, watau kayatacciyar hanyar aikawa da sakonnin text a wayar salula.  A wannan tsari, kana iya aikawa da sakonni ta amfani da haruffa masu launi, da kuma amon kira (watau Ringing Tone).  Wannan tsari na amfani a tsarin sadarwar wayar salula ne irin ta da. Jerin haruffan “MMS” kuma na nufin “Multimedia Messaging Service”, kuma hanya ce ta musamman da ake aika sakonni a wayar salula da suka shafi haruffa, da sauti, da bidiyo, da hotuna da dai sauransu. 

- Adv -

Wannan tsari na amfani ne da tsarin sadarwa ta Intanet na kamfanin waya wajen aikawa da wadannan nau’ukan sakonni.  A daya bangaren kuma, jerin haruffan “SMS” na ishara ne ga “Short Message Service”, kuma na tabbata duk mun san wannan tsari; wanda yana amfani ne da tsarin sadarwar kamfanin waya (Network Service) wajen aikawa da sakonni.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu Alaikum, ina son a min bayani a kan “Settings” din “GPRS” wanda ba a daukan kudi a wayar mai amfani da shi, sabanin wanda ake daukan kudi a wayarsu.  Da fatan an gane tambaya ta.  –  Nine Malam Malam Mai Zanen Hula Gololo: 08032822433

Malam Mai Zanen Hula barka da warhaka.  Tun ina sakanadare nake ta jin sunanka a gidajen rediyon kasar nan.  Ashe da taimako da nufin Allah za a hadu ta nan.  To Allah sa a dace.  Bayani kan tsarin amfani da Intanet a wayar salula wanda ba a iya daukar kudi a wayar mai amfani, a kashin gaskiya, ba halattaccen tsari ba ne sam ko kadan.  ‘Yan Dandatsa ne ke hankado kofar kwamfutocin kamfanonin waya, ta hanyar amfani da masarrafar “OperaMini” na musamman, don jonuwa da kwamfutocin kai tsaye.

Wannan ke bayar da damar shiga ko mu’amala da tsarin Intanet kyauta ta hanyar kwamfutocin, ba tare da manhajar kamfanin ta kalli wayar salularka ba a lokacin da kake lilo a saman giza-gizan sadarwa ta duniya ta hanyar kwamfutocinsu, balle har ta cire kudi.  Ba kai kadai ba, da dama cikin masu karatu sun sha bugowa suna neman Karin bayani kan wannan tsari.  Akwai ma wanda ya bugo mini cewa ya dade yana amfani da tsarin, amma daga baya abin ya yanke; har yake tambayar wai ko da gaske ne cewa wayarka na iya kamuwa da kwayar cutar kwamfuta, watau Virus a lokacin da kake mu’amala da wannan tsari?

Tabbas wannan tsari ba ya dawwama, nan take kamfanin zai gano wannan badakala har ya toshe hanyar da ake bi ana shiga.  Wannan tasa da zarar an fara amfani da shi na tsawon mako ko makonni biyu, sai ka neme shi ka rasa.  Har wa yau, akwai hadari wajen amfani da wannan tsari, domin wayar salula na iya kamuwa da kwayoyin cutar kwamfuta, watau Virus.  Domin wayar tana mu’amala da giza-gizan sadarwa ne kai tsaye, ta hanyar da babu tsaro, watau “Unsecured Connection”.  Don haka sai a hakura da wanda za a iya cire kudi, domin ya fi natsuwa.  Da fatan an gamsu.


Assalamu Alaikum Baban Sadik, shin, wace kasa ce ta kirkiri kwayar cutar kwamfuta, watau “Computer Virus”? – Hambali Azare: 08036966225

A gaskiya babu wata kasa da za a ce ita ce ta kirkiro wannan matsala.  Domin wani abu ne da ke ta’allake da kwarewa, wanda kuma kowa na iya samunsa a ko ina yake a duniya.  A takaice ma dai, ba za a iya cewa ga wanda asali ya fara kirkiran wannan matsala ta kwayar cutar kwamfuta ba.  Dalili kuwa shi ne: wannan matsala ta kwayar cutar kwamfuta ta fara samo asali ne ta sanadiyyar kurakuran da masu gina masarrafar kwamfuta ke yi cikin aikinsu, wanda sanadiyyar haka sai a samu matsala wajen aikin manhaja ko masarrafar.  Daga baya da magina suka gano tasirin ire-iren wadannan kurakurai, sai wasu suka ribaci wannan dama wajen kirkirar nau’uka daban-daban.  Wannan ke tabbatar da cewa babu wata kasa ko wani mutum musamman da za a ce shi ne ko ita ce ta fara kirkirar wannan matsala.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.