Sakonnin Masu Karatu (2016) (20)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

88

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina maka barka da war haka da fatan kana lafiya. Don Allah ina so a mini karin haske game da manhajar Windows; meye muhimmacinta ga kwamfuta? Daga Hamisu Salihu: salihukhamis2@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Manhajar “Windows” daya ne daga cikin nau’ukan babbar manhajar kwamfuta da ake amfani dasu yanzu a duniya.  Kamfanin Microsoft ne ya gina kuma yake lura da wannan babbar manhaja.  Abin da babbar manhaja (wanda ake harshen Turanci ake kira: “Operating System”) dai ke nufi shi ne, manhajar dake gangar-jikin kwamfutar gaba daya, sannan da zarar ka kunna kwamfuta da wannan babbar manhaja kake mu’amala.  Mahimmancin Windows a kwamfuta shi ne irin mahimmancin da rai yake dashi wajen tafiyar da gangar-jikin dan adam.  Muddin babu wannan babbar manhaja, to, ba abin da za a iya yi da gwarangwal din kwamfuta; ma’ana ba ta da wani amfani ga mai mu’amala.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, ina amfani da wayar Blackberry Z10 amma duk lokacin da na bude manhajar Whatsapp sai a turo min sako cewa: “Daga 31st December 2016 wannan wayar za ta daina amfani da manhajar Whatsapp.”  Tambayata ita ce: shin akwai wani karin tagomashi na bayanai ne da zan iya loda mata (Upgrade) don ta ci gaba da amfani da manhajar, ko kuma shikenan saidai na canja wata? Ka huta lafiya. Bashir Soja: bashir_soja@yahoo.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Lallai wannan sako da ake aiko maka ko kake gani a duk sadda kayi yunkurin hawa manhajar Whatsapp, gaskiya ne.  Hukumar Whatsapp sun fitar da wannan sako ne a ranar 6 ga watan Fabrairu na shekarar 2016, inda sanarwar ta ayya wasu nau’ukan wayoyin salula da aka dade da kera su da cewa zuwa ranar 31 ga watan Disamba baza su iya amfani da wannan manhaja ba a kan wayoyin.  Wadannan wayoyin salula da kamfanin ya zayyana dai su ne: “BlackBerry 7” da “BlackBerry 10.”  Sai “Nokia S40,” da “Nokia Symbian S60,” da nau’in “Android 2.1” da “Android 2.2,” da “Windows Phone 7,” mai dauke da wasu nau’ukan “wayoyin salula masu suna: “Window Lumia.”  Sai kuma nau’in “iPhone 3GS/iOS 6.”

Sai dai kuma, cikin makonni biyu da suka gabata kamfanin ya sake fitar da sanarwa dake nuna karin lokaci ga masu wadannan wayoyin salula, daga karshen wannan shekara zuwa ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2017.  Amma ba dukkan wayoyin bane wannan karin lokaci ya shafa.  Wayyoyin da sanarwar ta shafa dai su ne: nau’ukan “BlackBerry 7 da 10,” da nau’in “Nokia S40” da kuma “Nokia Symbian S60.”  Amma nau’ukan “Android 2.1” da “Android 2.2” da “Windows Phone 7” da kuma “iPhone 3GS/iOS 6” duk zuwa karshen watan Disamba za su daina hawa Whatsapp.

Babban dalilin da kamfanin ya bayar na hana wadannan nau’ukan wayoyin salula amfani da manhajar Whatsapp dai shi ne don dalilai na tsawo.  Da kuma cewa wadannan wayoyin salula sun tsufa, duk da cewa su ne wayoyin farko da suka fara amfani da wannan manhaja a farkon bayyanarta, sai dai kuma dole a dauki matakai na tsaron bayanan jama’a.  Wannan zance ne dunkulalle.  Abin da yake nufi a warware shi ne, wadannan wayoyin salula sun tsufa, ma’ana an dade da kera su, hakan yasa baza su iya daukan tsare-tsare da bayanan da ake turowa don tabbatar da tsaro a wayoyin salula masu amfani da wannan manhaja ba.

- Adv -

Don haka dole ne duk wanda yasan yana amfani da daya daga cikin wayoyin da kamfanin ya zayyana ya nemi sabuwa ko kuma ya nemo karin tagomashi (Update) daga kamfanin da ya kera wayar, don dacewa da babbar manhajar da kamfanin wayar ke amfani dashi a yanzu.  Wannan zabi na karshe abu ne mai wuya ga musamman wadanda ke amfani da wayoyin Symbian, don tuni an rufe kamfanin tun shekarar 2014.


Assalamu alaikum Baban Sadik, akwai shafukan da idan na bukaci shiga sai su ce in shigar da adireshin Imel dina da password. Ni kuma sai na hakura da shiga. Ko ba matsala na rika shigarwa? Ina tsoron kar a sace mini adireshin Imel di na ne da “password” din. Sunusi Musa Chairman Kulkul: 08020800420, sunusimusa595@yahoo.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Idan kaga haka, to, shafi ne dake da tsarin rajista ga masu ziyara don samun fadakarwa ko sakonni gajeru lokaci zuwa lokaci.  A yanayi irin wannan, dole ne ya zama kana da rajista a karon farko, kafin ka shigar da adireshinka na Imel, don tantance kanka.  Amma in har wannan shi ne karon farko da ka fara hawa shafin, ko ka sanya adireshinka na Imel za a ce maka babu adireshinka cikin jerin wadanda ke da rajista a shafin.  Sai dai kayi rajista.  Ya danganci me ya kaika.

Misali, a shafin BBC na turanci misali, akwai inda za kayi rajista don rika samun sakonni da suke aikowa lokaci zuwa lokaci don fadakar da kai sauye-sauyen da suke yi na shirye-shiryensu.  Ka ga wannan abu ne amfani gare ka idan kai mai yawan sauraren shirye-shiryensu ne.  Don haka, muddin ba wani abu mahimmi bane ya kaika shafin, babu bukatar sai ka shigar da adireshinka na Imel, balle maganar “Password” ma.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, dafatan kana lafiya. Muna ganin sakonninka a shafin Kimiyya da Kere-kere na AMINIYA masu wayar mana da kai kan kwamfuta. Allah ya saka da alheri ya karo maka ilimi mai amfani. Nasiru Abdulkadir Tabari: nasabdultab@yahoo.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nasiru.  Ina godiya matuka da addu’o’inku.  Allah saka da alheri, ya kuma sa abin da muke gabatarwa ya zama mai amfani gare mu baki daya, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.