Sakonnin Masu Karatu (2016) (1)

A wannan mako dai mun leka jakar wasikarmu ne don amsa wasu daga cikin sakonninku da kuka aiko mana ta Imel da Tes da kuma Facebook.  Kashi na biyu na tafe a mako mai zuwa in Allah yaso. A ci gaba da kasancewa tare damu.

73

Assalamu alaikum malam, kasancer kai ne wanda mafi yawan jama’ar kasar nan suka sani cewar Allah ya maka baiwa ta yadda kake bayani, kake karantar da mutane abin da ya shafi ilimin kwamfuta da fasahar Intanet ake fahimta cikin sauki, musamman cikin harshen Hausa.  To, kasancewar kuma akwai mutane masu kokarin amfani da wadannan kafafe da hanyoyin sadarwa amma ba su fahimtar harshen turanci,  wannan yasa muke rokon Baban Sadik ko zai yiwu ya rubuta wani littafi mai koyar da darasin kwamfuta cikin harshen hausa?  Ko hakan zai kara taimaka wa jama’armu su kara fahimta.  –  Yakub I. Yakub

Wa alaikums salam, barka ka dai.  Dangane da abin da ya shafi rubutawa da kuma buga littafi mai dauke da darussa kan kwamfuta da hanyoyin sadarwa na zamani, wannan abu ne mai kyau.  Kuma zai kara wa da dama cikin jama’armu himma wajen koyon wannan ilimi a matakin gaba da sakandare.  A baya na rubuta littafi mai bayani dalla-dalla kan ilimin fasahar Intanet, mai take:  “Fasahar Intanet a Sawwake,” amma har yanzu ba a buga littafin ko ba.  Ina kan masa gyare-gyare ne sanadiyyar tsawon lokaci da ya dauka bayan rubutun farko da bitar da aka masa a shekarar 2009.

Dangane da abin da ya shafi buga littafi na musamman kan ilimin kwamfuta tsantsa kuwa, na san a baya akwai wadanda suka yi kokarin hakan.   Akwai Malam Sagir Muhammad dake Kano, wanda masani ne kan fannin gina shafin yanar sadarwa (Web Designer), ya rubuta littafi kan wannan fage a shekarun baya.  Duk da cewa ban taba ganin littafin ba a fili, amma ina da tabbaci kan haka.  A nawa bangaren kuwa, ina kudurin yin wani abu makamancin hakan, duk da cewa na tsara wasu ‘yan darussa ne da zan rika gabatarwa lokaci-lokaci, masu saukin fahimta kan ilimin kwamfuta.  Bayan wadannan darussa ne nake sa ran in da hali, sai a fitar dasu a matsayin littafi.   Don haka, wannan shawara taka tana kan hanya.  Na gode matuka.


Assalamu alaikum Baban sadik, ina matukar godiya da ka amince min kulla abotar musulunci da na kimiyya da kere-kere, da kuma kimiyya da fasahar sadarwa,  Allah ya kara basirar ci gaba da bamu karatu mai gwabi.  Ina matukar godiya domin kai malamina ne a jaridar Aminiya; tsawon shekaru shida ina bibiyar karatun da kake bamu in shaa Allahu.  –  Manu Abdullahi Dutsinma

Wa alaikumus salam, Malam Abdullahi (takwarana) ina godiya matuka musamman ta la’akari da tsawon lokacin da ka dauka kana karanta wannan shafi a Jaridar AMINIYA.  Wannan ke nuna kana cikin tsofaffin daliban wannan shafi wadanda suka lazimci jaridar tsawon lokaci.  Ina fatan ka karu da abubuwan da ake gabatarwa wannan tsawon lokaci har wa yau.  Ina rokon Allah ya amfanar damu abin da aka koya baki daya, amin.  Na gode.  Na gode.


- Adv -

Assalaamu alaikum Baban Sadik.  Gaskiya ina jin dadin irin tarihin abubuwan da kake bayarwa.   Allah ya kara basira.  –  Garzali Ghali

Wa alaikumus salaam Malam Garzali.  Ina godiya matuka da wannan yabo da kuma addu’ar da ka mini.  Allah ya saka da alheri, ya kuma sa abin da ake karantawa ya amfane mu baki daya, amin.  Na gode.  Na gode.  Na gode.


Assalam alaikum. Da fatan kana lafiya. Allah yasa haka amin.  Don Allah ina so ka taimaka min da kasidar bincike a Internet.  Kuma me yasa kamfanonin Layin waya na Nigeria ba sa yiwa ‘yan Nigeria kyautuka manya kamar yanda kamfanonin kasashen duniya  suke yi?   Misali akwai wani abokina da ya ci nasarar gasa, inda ya samu Fam dubu sittin na kasar Ingila (£60,000.00).   Kuma ba chacha bace. Me yasa su na Nigeria ko yaushe sai chacha?  Akwai wani abokin na wa kuma da ya samu dala dubu arba’in ($40,000.00) daga wani kamfanin layin waya a kasar Malesiya.  Duk ina da kwafi na certificate din kyautar.  Prince Jameelu – jamilu.abdulkarim1@yahoo.com

Wa alaikumus salaam.  Barka ka dai Malam Jameelu.  Bukatarka ta farko dai na aika maka, sai ka duba akwatin Imel dinka.  Dangane da tambayarka ta biyu, ban san dalilin hakan ba, domin kowane kamfani da irin tsarinsa na kasuwanci.  Idan da hali kana aika musu kokenka a shafinsu na Intanet ko ta hanyar sakon tes, don tuntubarsu kan dalili.  Na tabbata suna karban koken kwastomominsu.  Ta yiwu sanadiyyar kokenka su fara koyi da ire-iren wadancan kamfanoni.  Da fatan ka gamsu.


Salamun alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya da kai da iyalanka duka.  Allah ya kara basira, amin.   Duk mako ina biye da kai a shafinka.   Amma ina ganin sau daya na taba aiko sako, sai kuma yau. Ina so don Allah ka taimaka ka turo mini kasidar nan mai take:  “Tsibirin Bamuda.”  Sai kuma tarihin mutumin nan dan kasar Rasha makerin bindigar AK47 (Janar Clashincov).  Sannan ina bukatar tarihin mutumin nan dan kasar Iraki wanda ya kawo ilimin lissafi da sauransu. Sai kuma yanda zan yi add dinka a Facebook saboda in rika karuwa da iliminka.   Na gode. Daga Babangida Musa Shinkafi.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Babangida.  Da fatan kana lafiya.  Danagane da bukatarka kan kasidu, akwai su, kuma kamar yadda na tabbata ka gani a baya, ana aiko mini adireshin Imel ne sai in tura wa mai bukata.  Ba kasidu ne da za a iya aika su ta hanyar sakon tes ba.  Don haka ka aiko mini da adireshinka na Imel sai in aika maka su. Sai na ji daga gare ka.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.