Sakonnin Masu Karatu (2016) (2)

Ci gaban sakonninku kamar yadda aka saba. A sha karatu lafiya.

100

Salaamun alaikum Baban Sadik, shin me ake nufi da ‘tag’, da ‘poke da kuma ‘pending’ dake sahen sada zumunta na Facebook?  Zan so ka turo min amsa ta imel di na dake: Sanimaster1@yahoo.com.  Mun gode.  Sani Shuaibu, Potiskum, Yobe State

Wa alaikumus salam, barka Malam Sani Master.  Wadannan kalmomi suna ishara ne ga abubuwa daban-daban da suka shafi nau’unta tsari da hanyoyin sadarwa da samar da nishadi a Dandalin Facebook.  Kalmar “Tag” na nufin dayan abubuwa biyu ne; na farko dai sunan wata karamar manhaja ce da ake amfani da ita wajen tarayya da wani aboki ko abokiyar kawance a dandalin facebook, cikin sakon rubutu ko hoto da mai shi ke son dorawa a shafinsa.  Idan ka loda hoto ko wani sako a shafinka, bayan ka gama, a kasa akwai inda za ka latsa don shigar da sunayen wadanda kake son su yi tarayya da kai wajen yada wannan hoto.

Abu na biyu da kalmar “Tag” ke nufi shi ne, lika sunan wani aboki ko abokiya a kan hoto ko sakon rubutu da kayi a shafinka.  A nan mun dauki kalmar da ma’anar aiki ne kenan.  Duk wanda ka lika sunansa ta hanyar “Tag” a sakon da ka rubuta ko hoton da ka loda, wadannan sakonni za su bayyana a shafinsa kai tsaye, kuma dukkan abokansa, ko da sun kai dubu biyar ne, za su iya ganin sakon kai tsaye.  Wadanda baza su iya gani ba sai wadanda ka toshe su daga shafinka, ko shi ya toshe su daga shafinsa, wato: “Block”, ko kuma wadanda ka killace su a kasan sakon bayan ka gama rubutawa ko lodawa.  Su kam wadannan ba za su iya ganin sakon ba.

Kalma ta biyu, wato: “Poke”.  Ita ma tana nufin sunan manhaja ce, sannan idan muka dauki kalmar da ma’anar aiki, tana nufin yin amfani da manhajar “Poke” dake dandalin Facebook.  Wannan manhaja daya ce daga cikin hanyoyin samar da raha a dandalin Facebook.  Idan aka ce: “Sadik poke you” misali, ana nufin ya tsikareka kenan.  Manhaja ce da ake amfani da ita wajen tsikara, don jawo hankalin aboki ko wanka ake kawance dashi ko ita.   Kuma da zarar ya maka nan take za a sanar da kai.  Daga nan kai ma kana iya mayar da martani.  Duk da cewa ba kowa bane ya san ma’anar wannan manhaja, wanda hakan yasa wasu ke amfani da ita fiye da kima, amma wannan shi ne dalili da ma’ana ta asali da suka samar da wannan tsari.

Kalmar karshe, wato: “Pending” na ishara ne ga aiki ko wani abin da ba a karasa shi ba, ko ake jira wani ya aiwatar da wani abu a kanshi.  Wannan ya fi shahara a zaurukan Facebook, wato Groups.  A takaice dai kalmar “Pending” na nufin jira ne, ko sauraron aiwatar da wani abu kafin direwa wani wuri ko aiwatar da wani aiki.  Da fatan ka gamsu.


Salamun alaikum, daga mai kaunarka. Bayan gaisuwa tare da fatan kana cikin koshin lafiya,  Allah yasa haka amin.   Don Allah ka amsa min tambayata; Mene ne “Email”, sannan yaya ake bude Imail, kuma mene ne amfaninsa da rashin amfaninsa?   Bayan haka, a cikin nau’ukan manhajar Imel Wanne ne yafi dadin sha’ani? Wassalam. Daga Dan uwanka: Abdullahi Aliyu Alkas, Bauchi State 09030103444

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka ka dai takwarana.  Da fatan kana cikin koshin lafiya.  Da farko dai, idan aka ce Imel ana nufin “Wasikar hanyar sadarwa ta Intanet” ce, wacce ke dauke da adireshi mai hawa biyu; da sunan mai akwatin Imel da kuma sunan kamfanin dake dauke da manhajar Imel din.  Idan aka kasa manhajar Imel dangane da hanyoyin mu’amala, sun kasu kashi biyu ne; akwai Manhajar Imel ta Intanet, wacce ake kira “Internet Email Programme” kenan.  Ire-irensu su ne: Yahoo! da Gmail da Hotmail da dai sauransu.  Sai nau’i na biyu wanda ake iya amfani da ita a gajeren zangon sadarwa, ko da kuwa babu Intanet a wurin.  Su ma akwai su da dama.  Daya daga cikinsu ita ce manhajar Imel na kamfanin Microsoft mai suna: Outlook.

Amfanin Imel yana da dimbin yawa, ya danganci iya sanayyarka da manhajar.  A takaice dai, ana amfani da ita wajen aiwatar da sadarwa cikin gaggawa, cikin sauki.  Kana iya aika hotuna da sauti da bidiyo duk ta amfani da Imel.  Sannan kana iya amfani da adireshin Imel wajen karban sakonni.  Kana iya amfani da ita wajen bude shafin Facebook, da MySpace, da Twitter da galibin wuraren nishadi a Intanet.  Daga cikin matsaloli ko kalubalen dake tattare da mallakan Imel akwai kamuwa sakonnin bogi, da sakonnin ‘yan zamba cikin aminci (Yahoo Boys) masu amfani da wannan hanya don yaudarar mutane da karbu musu kudade.

Dangane da abin da ya shafi inganci ko nagarta tsakanin wadannan nau’uka na manhajar Imel kuwa, ya danganci dandanonka, da abin da ka saba dashi.  Amma wadanda suka fi shahara dai su ne Yahoo Mail, da Google Mail ko Gmail da kuma Hotmail ko Windows Live Mail.  Daga cikin wadannan ukun kuma manhajar Imel na Gmail ta fi shahara, musamman ganin cewa dukkan wayoyin salula na zamani masu dauke da babbar manhajar Android suna tilasta mallakar akwatin Imel na Gmail kafin fara amfani dasu, musamman ganin cewa babbar manhajar Android din daman ta kamfanin Google ce, wadda kuma ita ce take mallakar manhajar Gmail din.  Abin ya zama tuwo-na-mai-na kenan.

Shawarata a nan ita ce, idan kana da wayar salula mai amfani da babbar manhajar Android ce, kana iya zabar Gmail, sabo da saukin mu’amala, da samun manhajar Imel na wayar salula mai saukin mu’amala a kan wayar salularka, don sarrafa sakonninka cikin sauki.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum. Malam barka da ibada.  Ina karanta wani littafi ne mai suna “The Final Divine Religion Islam”, sai naci karo da wadannan kalmomi: “Hydrogen,” da “Helium,” da “Tons of gas,” da kuma “Tons of Substance and Mass.”   Ina neman bayani kansu. 

Wa alaikumus salam, barka da warhaka.  Wadannan kalmomi suna ishara ne ga nau’ukan sinadaran da Allah ya samar a ciki da wajen wannan duniya da muke rayuwa a cikinta.  Kalmar “Hydrogen” na nufin wani nau’in iska ne mara launi, wanda ba shi da dandano wajen shaka – wato babu wani wari ko kamshi da makamantansu – kuma tana da saurin daukan wuta da zarar an gitto shi kusa da ita.  Ma’ana idan aka bijiro da iskar Hidirojin kusa da wuta, nan take take kamawa.  Sinadari ne mai matukar mahimmanci wajen hada abubuwan amfani daban-daban – daga amfanin rayuwa zuwa kera makamai.   Akwai nau’in makamashin nukiliya da ake kerawa da wannan nau’in iska na Hidirojin (Hydrogen).

Kalmar “Helium” ita ma na ishara ne ga wani nau’in sinadarin iska, wadda ita ce mafi kankanta wajen rashin nauyi daga cikin jerin sinadaran da take da dangantaka dasu.  Kalmar “Tons of Gas” kuma na nufin tarin dandazon sinadarin iska ne.  Asalin kalmar “Ton” (wanda jam’inta shi ne: Tons) na nufin tarin abu ne mai yawa; dandazonsa.  Amma a fannin kimiyyar lissafi har wa yau ana amfani da ita wajen auna nauyin abu.  Ton guda na nauyi daidai yake da kiligiram 1,016.  Haka ma kalmar “Tons of Substance and Mass”, tana ishara ne ga tari ko dandazon wani irin nau’in sinadari wanda ke dauke da makamashi masu kamaiceceniya da juna, masu yawa.  Asalin kalmar “Substance” na nufin hakikanin abu ne; wajen siffa ko kama ko samuwa.  Kalmar “Mass” kuma a ilimin fannin kimiyya na nufin yawan abu ne, musamman sinadarai ko makamashi, misali.  Da fatan gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.