Sakonnin Masu Karatu (2015) (5)

Ci gaban sakonninku. A ci gaba da kasancewa damu, kuma a sha karatu lafiya.

201

Assalaamu alaikum Baban Sadik, na lura idan aka sa duwarwatsu da ruwa kamar kofuna uku a cikin tayar mota, ko kuma tif (tube), aka kuma tayar da motar aka fara tafiya da ita, tayar za ta rika jujjuyawa ne kamar yadda duniyarmu take zagaya rana, sannan wadannan duwarwatsun za su rika yawo ne a hargitse; wannan ya hau wannan, wancan ya hau wancan – babu kan-gado.  Tambayata a nan ita ce: me yasa duniyarmu da karikitan dake cikinta – kamar su tekuna, da gidaje, da motoci ba su irin wannan garwayar?   Kuma me yasa ba mu ganin kanmu ya koma kasa kafafunmu sun koma sama; sai ka ga komai a natse?  Alhali kuma idan ka jera gwangwanayen madara komar guda goma, in dai ba iska bace ta bige su, za su iya kai shekaru goma daram (a wuri daya).  Ni kam a kodayaushe na hada uku da uku sai in ga biyar.  Don Allah a taimaka mini da amsar.  –  Junaidu Sokoto: 09035907765

Wa alaikumus salam, Malam Junaidu.  Wannan tambaye ce mai matukar mahimmanci, wanda na san da yawa cikin mutane za su so sanin dalilan hakan, saboda samun kansu cikin irin halin da zuciyarka ta samu kanta kafin wannan tambaya.  Wannan yasa na killace mako guda don fadada bayani.  Domin amsar wannan tambaya, in har gamsuwa ake son samu iya gwargwado, dole tana bukatar fadada bayani don komai ya fito fili filla-filla, ta hanyar fayyace bayanai sanka-sanka.

Wannan misali da ka kawo a zahirin rayuwa ta yau, don yin kiyasi a kan irin dabi’ar da duniyarmu ke gudanuwa a kai, misali ne mai kyau, amma wanda zai sawwake wa mai tambaya neman dalili.  Amma idan ta bangaren asali ne, babu alaka ko kadan tsakanin bangarorin biyu.  Kana bayani a kan yadda idan aka cakuda tsakuwa da ruwa a cikin tayar mota – kamar yadda muke cakude a cikin wannan duniya a yau –  akan samu hargitsi ne mai girman gaske, da zarar motar ta fara tafiya, sanadiyyar juyawar tayar.  Amma ga shi mu da muke cakude cikin wannan duniya, wacce tafi girma da fadi, sai dai kuma komai a natse.  Babu hargitsi. Babu cakude irin wanda ke tayar motar da daka cike da ruwa da tsakuwa (ko tsakwarkwani, kamar yadda ka kira su).  Mece ce dalili?  Dunkulalliyar amsar dai kwaya daya ce:  ka’idojin da wannan duniya tamu ke gudanuwa a kansu, sun sha bamban da wanda tayar mota ke gudanuwa a kai.  Shi yasa da ka hada uku da uku, sai ka samu biyar, maimakon shida.

Dr. Andrew Fraknoi shi ne Shugaban Sashin ilimin Sararin Samaniya a Jami’ar Foothill dake kasar Amurka.  A cikin doguwar kasidarsa mai take: “How Fast Are You Moving When You Are Sitting Still?” ya tattauna kan wannan batu, tattaunawa irin ta ilimi da binciken kwakwaf.  Inda yayi kokarin gamsar da masu tunani irin wannan (wanda tunani ne da galibin jama’a ke yi kan haka).

Da farko dai ya kamata mu san wai shin, wannan duniya tamu tana juyawa ma kuwa?  In eh, to me yasa, kamar yadda ka kasa fahimta, ba a ganin alamar juyawarta a zahiri?  Sannan me yasa ba a ganin sakamakon juyarta ta hanyar samuwar hargitsi da cakuduwar abubuwa, a zahiri?  Sannan, me ye iya kadarin saurin juyawarta?

Duniyarmu Tana Juyawa

Galibin lokuta idan ka shiga mota kana tafiya, ko jirgin kasa, da zarar ka kalli bishiyoyi ko gidajen dake gefen hanya, sai ka ga kamar su ne suke tafiya da baya da baya, ba wai motar da kake tafiya a cikinta ba.  Har wasu kabilun Najeriya kan yi wa wasu kabilun raha, cewa wani ya shiga mota ana cikin tafiya sai ya ga kamar bishiyoyi ne kawai suke tafiya amma motar a wuri daya take.  Sai nan take yace a sauke shi a bashi kudinsa, zai je ya hau bishiya, wacce kyuata ce, tunda su ne ke tafiya.  Wannan dabi’a ce ta kiyasi da dan adam ke da ita a kwakwalwarsa.  A duk sadda ka kalli Wata da Taurari cikin dare, sai ka ga kamar wannan duniyar a tsaye take, su ne ke juyawa.  Idan ka kalli Rana ma haka za ka gani.  A idonmu take bullowa a duk safiya, sannan a idonmu take faduwa a duk yammaci.  Ga alama, a tunani gajartacce, sai a ga kamar ita ce kadai ke juyawa, mu a tsaye muke cak.  Haka lamarin yake idan kana zaune a kan kujera kana hutawa, idan wani yace maka a hakan ma duniyar na juyawa, sai abin ya maka wani bambarakwai, wai namiji da sunan Rakiya.  Amma a hakikanin gaskiya duniyarmu tana juyawa a duk yini.

Malaman ilimin Sararin samaniya suka ce duniyarmu na juyawa sau daya daga turkenta (“Axis”), a duk cikin sa’o’i ashirin da hudu.  Haka kayayyakin dake cikinta, suna juyawa ne tare da ita duniyar baki daya.  Sannan wannan juyawa na samuwa ne cikin saurin ko tazarar mil 1000 a duk sa’a guda.  Wannan yayi daidai da tazarar tafiyar kilomita 1600.  Wannan tazarar da saurin tafiya kan ragu idan ta doshi arewacin duniya, a duk juyawarta.  Wannan juyi ko zagayen yini kenan da duniyarmu keyi, daga turkenta, wato “Axis.”

A daya bangaren kuma, akwai juyin shekara-shekara da duniya ke.  Wannan juyi na shekara na samuwa ne ta la’akari da tazarar lokaci da saurin tafiyar da duniyarmu ke yi kafin zagaye rana.  Duniyarmu kan dauki tsawon kwanaki 365 kafin ta gama zagaye Rana sau daya, wato shekara guda kenan.  To me yasa?  Hakan ya faru ne saboda nisan tazarar tafiya dake tsakanin duniyarmu, da Ranar dake hasko mu  a duk yini.  Malamai sun kiyasta cewa akwai tazarar tafiyar mil miliyan 93 (daidai da kilomita miliyan 150) tsakanin duniyarmu da Rana.  Bayan haka, titin da duniyarmu ke bi a yayin zagaye Rana cikin kwanakin shekara, da aka kiyasta nisansa, ta la’akari da nisan dake tsakanin duniyarmu da ita kanta Ranar, bincike ya tabbatar da tazarar nisan mil miliyan 600 (daidai da kilomita miliyan 970) kafin gama zagaye guda cikin shekara.

Wannan, a cewar masana, na nuna cewa a duk cikin sa’a guda, duniyarmu na tafiya a saurin da ya kai mil 66,000 (daidai da kilomita 107,000).  Tafiya a wannan tazara da sauri, a cewar masana, na iya kai matafiyi daga birnin San Franciso zuwa babban birnin Washington DC (a duk a kasar Amurka), cikin minti uku, rak.  Wannan a tafiyar mota ana kaiwa ne cikin sa’o’i biyar; kamar daga Abuja zuwa Birnin Kano, ko daga Abuja zuwa Bauchi.

Bayan juyi da zagayen da duniyarmu keyi, kafin mu kai ga bayanin dalilan dake sa ba a iya gane tafiyar, da dalilan dake sa har wa yau ba a samun hargitsi a wannan duniya tamu, zai dace mu kalli sauran halittun da duniyarmu ke gudanuwa a sarari daya dasu, irin su Rana da Wata da Taurari; wai shin su ma suna juyawa ne, ko dai a tsaye suke cak, duniyarmu ce kadai ke juyawa?

Rana Da Wata Na Juyawa

Kafin kwarewar turawan Turai yayi nisa cikin binciken kimiyya, akidarsu dangane da rana ita ce, a tsaye take cak!  Duk sauran halittun da ke makwabtaka da ita kuma suna jujjuyawa ne a cikin falakinsu, don kewaye ta.  Har a karni na biyu haka ake tafiya a yammacin duniya.  Wannan ita ce ka’idar da ake kira: “Heliocentric Theory of Planetory Motion.”  A cikin shekarar 1512 ne wani malamin kimiyya mai suna Nicholas Copernicus ya samar da wannan ka’ida ta ilimi mai suna Heliocentric Theory of Planetory Motion, wanda ke nuna cewa dukkan sauran halittun da ke sararin samaniyar duniya baki daya suna jujjuyawa ne a cikin falakinsu da ke gewaye da rana. Amma ita rana a tsaye take cak, ba ta motsawa.  Haka ma binciken da Yohannus Keppler ya tabbatar, cikin shekarar 1609.  Sakamakon wadannan bincike ne ya fara wayar wa turawa da kai, suka dada samun fahimta kan yadda manyan halittun da ke sararin samaniya ke juyawa, suka kuma basu damar fahimtar “juyin-wainar” da dare da yini ke yi a cikin falakinsu.

Na tabbata idan ba yanzu ba, da dama cikinmu (wadanda suka yi sakandare shekarun baya), an karantar da mu wannan ka’ida ta ilmin kimiyya da ke nuna cewa “dukkan sauran halittun da ke sararin samaniya na kewaye da rana ne, a halin zagayen da suke yi.”  Amma a yanzu kam, malaman kimiyyar sararin samaniya, wato Astronomers, sun warware wancan ka’ida ta Nicholas da Keppler, inda suka tabbatar da cewa lallai rana ma na jujjuyawa a nata falakin, ba a tsaye cak take ba guri guda.

- Adv -

Wata Mahangar

Idan muka koma Al-kur’ani mai girma cikin Suratul Ambiya’, za mu samu tabbaci da ke nuna cewa da rana da wata, duk kowanne daga cikinsu na da nashi falaki (ko hanya, ko magudana) da yake bi, da yanayin gudu ko saurinsa.  Ga abin da Allah yace:

“Kuma Shi ne wanda Ya halitta dare da rana (yini), da rana da wata, dukkansu a cikin wani sarari suke iyo.” (Ambiya’:33)

Wannan ke nuna cewa lallai akwai falaki ko tafarki da kowannensu ke bi a halin iyonsa.  An ambaci dare da yini a nan don nasaba da ke tsakaninsu da rana da kuma wata.  Har wa yau, tsarin tafiya ko juyawa da suke yi a cikin wannan falaki nasu ya sha bamban.  Kowanne da irin saurin da ya kamace shi yake tafiya.  Dangane da haka Allah Ya sake cewa:

“Rana ba ya kamata a gareta, ta riski wata. Kuma dare ba ya kamata a gareshi ya zama mai tsere wa yini.  Kuma dukkansu a cikin sarari (falaki) guda suke iyo.” (Yasin:40)

Kalmar “iyo” ko “sulmuya” da Allah yayi amfani da ita (wato “Yasbahoon”) zai sa wani yayi tunanin ko akwai ruwa ne a sararin samaniya da har rana da wata suke yin iyon a cikinsa.  A a, ba haka lamarin yake ba.  Kalma ce mai fadin sha’ani, ya kuma danganci yadda aka yi amfani da ita a jimla. Idan aka yi amfani da ita kan mutum a cikin ruwa, yana nufin yana iyo kenan.  Idan a kasa yake, ana nufin yana tafiya kenan.  Haka rana da wata, su ma tafiya suke yi, a cikin muhallinsu a sararin samaniya.  Sai dai kowanne daga cikinsu da tafarkinsa daban.  Kuma malaman kimiyyar sararin samaniya a yanzu sun tabbatar da cewa rana kan gama kewayenta ne – daga tashar farawa zuwa tashar tikewa (ko “axis”, a turance) – cikin kwanaki ashirin da biyar, a kowane wata.  Kenan, cikin kwanaki ashirin da biyar take yin kewaye daya.  Shi kuma wata yana kewaye wannan duniya tamu ne cikin kwanaki ashirin da tara da rabin kwana (29½).  Dangane da haka Allah yace:

“Kuma da wata, mun kaddara masa manziloli, har ya koma kamar tsumagiyar murlin dabino, wadda ta tsufa.” (Yasin:39)

Wadannan “manziloli” da Allah ya fada, su ne masaukai da yake sauka a cikinsu a kullum, har ya gama zagayensa cikin wadancan kwanaki da suka gabata.  Wannan ke nuna mana cewa dukkan halittun da Allah ya dora a sararin samaniya suna juyawa ko motsawa ne.  Amma a tare da haka, ba ka samun wata hatsaniya ko hargitsi cikin lamarin baki daya.  Meye dalili?

Iko da Kudurar Ubangiji

Dalili na farko dai zamu same shi ne cikin iko da kudura da iya kyautata halitta da Allah ya siffatu da su.  Babu wanda zai iya samar da ababen halittu irin wadannan sannan ya samar da natsuwa da kimtsi cikin gudanuwarsu, tsawon zamani, ba tare da samun matsala ba, sai Allah.  Don haka, ko da bamu samu wani dalili na zahiri ba dangane da abin da ke sa a kasa samun hargitsi a wannan duniya bayan juyawa da zagaye da take yi a duk yini da shekara ba, wannan kadai ya isa dalili, ga kowane dan adam mai lafiyayyen hankali.

Tsarin Janyo Nauyi Kasa (Force of Gravity)

Da suka gudanar da bincike na kwakwaf, Malaman ilimin Sararin Samaniya sun tabbatar da cewa babban dalilin da yasa ba a samun hargitsi bayan samuwar abin da a a zahiri zai iya sa a samu hargitsi da rugujewar al’amura a wannan duniya tamu, shi ne samuwar wata ka’ida da tsari da Allah ya kimtsa a duniyar.  Wannan tsari kuwa shi suke kira: “The Force of Gravity.”  Tsari ne dake janyo dukkan wani abin dake sama, zuwa kasa, iya gwargwadon nauyinsa.  Suka ce wannan tsari ne ke like mu da kasa, ta hana mu yawo cikin sararin duniyar, kamar yadda auduga ko fallen takarda ko ganyayyakin itatuwa suke yi idan iska ta kada; mai karfi ko mai rauni.  Amma a wasu duniyoyin babu wannan ka’ida.  A tare da samuwar wannan ka’ida, akwai wasu alamomi da zasu nuna mana, idan mun natsu mun yi kallo mai cike da basira, cewa duniyar na juyawa.  Wasu alamu ne wadannan?

Alamar farko suka ce ita ce hargitsin ruwan teku dake samuwa lokaci lokaci.  Sai alama ta biyu, wato iska mai karfi da ake samu a sararin wannan duniyar tamu.  Wadannan alamomi, in ji Malaman ilimin Sararin Samaniya, dalilai ne guda biyu dake nuna mana cewa lallai wannan duniya tamu tana juyawa a duk sa’a guda.  Domin asalin samuwarsu na daga karfin juyawar duniyarmu ne, sadda take zagayenta a falaki.

Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.