Facebook Gidan Rudu: Magudi Cikin “Comments” Da “Likes”

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook, a shekarar 2015.

183

Magudi Cikin “Comments” da “Likes”

Daga cikin manyan rudu dake dandalin Facebook akwai rashin hakika dake tattare da galibin abubuwan dake faruwa a dandalin; daga rubutun da ake yi a shafuka zuwa ta’alikin masu karantawa (Comments); daga yawan “Like” zuwa karancinsa; daga hotuna zuwa labaru; kashi 60 cikin 100 duk babu hakika tare da su.  Me nake nufi da rashin hakika?

Akwai samari da ‘yan mata a Groups ko shafukansu, masu yin rubutu don ganin wasu sunyi kan maudu’in, ba tare da cewa suna da kudurar ilimi kan maudu’i ko ra’ayin yi ba a farkon lamari.  Akwai samari da ‘yan mata masu matsa alamar “Like” a rubutun wasu abokai ko yan mata ko samarinsu, ba don suna so ba, sai don kada rashin hakan ya zama matsala wajen alakarsu da mai rubutun.  Akwai samari da ‘yan mata, maza da mata, yan birni da yan kauye masu shafuka a Facebook, wadanda bayan sun yi rubutu, sai su yi ta bibiyar abokansu, da kawayensu, da ‘yan matansu, da samarinsu, cewa su je suyi “Like” ko su yi ta’aliki (Comments) kan rubutun da suka yi.  Wannan ya fi yawa a galibin Zaurukan Facebook (Facebook Groups).

Akwai da yawa cikin mutane da ransu ke baci idan suka yi rubutu ko suka makala wani hoto a shafinsu, amma ba a yi ta’aliki (Comments) ba ko babu “Likes” a kan rubutun.  Akwai wadanda masoya ne, amma sun bata saboda yayi rubutu a shafinsa budurwarsa bata ce komai kan rubutun ba.  A tare da cewa wasu sun yi ta’aliki.  Akwai wacce na ga sun bata da kawarta saboda bata yi “Like” a kan abin da ta rubuta a wani Zaure nasu ba.  Wannan jahilci ne da son zuciya.

Daga cikin rashin hakika dake Dandalin Facebook, akwai rudu cikin ta’alikin masu ta’aliki a shafuka.  Da yawa cikin masu ta’aliki (Comments) akan rubutu, ba su wakiltar kansu.  Wasu na ta’aliki ne idan sun ga abokansu sunyi.  Wasu ma ba su karanta rubutun, da zarar sun ga galibin masu ta’aliki na cewa: “Amin” sai su ma kawai su rubuta “Amin.”  Ba wannan kadai ba ma, da yawa cikin masu matsa alamar “Like” basu san hakikan manufar samar da wannan manhaja ko tsari ba.  A ka’ida, abin da ya birge ka shi kake latsa masa “Like”.  Shi yasa hukumar Facebook ma ke kokarin samar da kishiyarta, wato: “Dislike.”  Kuma ma shi yasa ko a yanzu ne, idan cikin kuskure ka matsa alamar “Like” sai daga baya kaga wannan zance bai dace ace ka kaunace shi ba (wanda abin da manufar “Like” ke isarwa kenan), kana iya sake matsa alamar, za ka ga ance: “Unlike.”

- Adv -

Darasi:

  1. Kada ranka ya baci don ka yi rubutu babu wanda yace komai a kan rubutunka. Me zai sa ka damu, in dai ka yi don Allah ne?  Me zai sa ka damu, in har ka san abin da ka  rubuta mai fa’ida ne?  Rashin ta’aliki ko “Like” ba shi ne alamar ba a gani ko karanta ba;
  2. Idan kana da abokai 5,000 misali, kuma kayi rubutu a shafinka amma babu wanda yace komai, kada ranka ya baci. A kalla kashi 30 cikin 100 za su gani ko su karanta ko kuma su amfana.  Duba ka gani, nawa ne kashi 30 na 5,000?  Ga lissafin: 5,000 x 0.30 = 1,500.  Mutum 1,500 zasu amfana, a kalla.  Me zai sa ranka ya baci don ba a ce komai ba?;
  3. Neman jama’a su zo su ce “wani abu” kan rubutunka ko su yi “Like”, alama ce dake nuna ba don Allah kayi ba. Sannan kai kanka baka gamsu da ingancin abin da ka rubuta ba.  Idan don Allah kayi, kuma ka gamsu da ingancin abin da ka rubuta, don me za ke je yawon neman jama’a su zo suyi zance?  Ai ME MADI KE TALLE, AMMA MAI ZUMA FA…?

Jama’a, muyi don Allah, sai mu samu albarkar Allah, da kuma kyakkyawar sakamako daga Allah!

BABAN SADIK

03.02.2016 – 11:17am

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.