Rayuwata a Duniyar Sadarwa (2)

Takaitaccen tarihina ne wannan kan irin gwagwarmayar da na sha a fannin bincike kan kimiyya da fasahar sadarwa na zamani. Wannan kashi na biyu kenan. A sha karatu lafiya.

563

Shiga na wadannan majalisu na Intanet ne ya zaburar da jajircewata kan harkar sadarwa.  Na hadu da mutane da dama a fannoni masu yawa da bazan iya tuna sunayensu ba.  Wannan yasa na zama a makale da dukkan majalisun da nake cikinsu; dare da rana safe da yamma.  Bayan su ma akwai majalisar “Hausa Net” ko “Zauren Hausa,” – https://networks.h-net.org/h-hausa –  wanda gamammen shafi ne mai dauke da zaurukan harsunan duniya, wanda wani bature ya bude.   Farfesa Abdallah Uba Adamu ne ya shigar da ni wannan zaure.  Wannan zaure ba karamin zaure bane; akwai fa’idoji da dama a cikinsa.  Sanadiyyar zama na a ciki na fara sha’awar fannin fassara daga wani harshe zuwa wani.

Dame a Kala…

A halin yanzu fassara sana’ata ce, wacce nake cin abinci da ita.  Bayan wasu ‘yan kananan littattafai da kasidu da na fassara ma wasu kamfanoni, ciki har da hukumar majalisar dinkin duniya mai lura da harkar lafiya, na kuma fassara shahararren littafin nan mai suna “LAA TAHZAN” (Don’t Be Sad) na babban Malami, Aa’id ibn Abdallah Al-Qarnee.  Yanzu haka ana gab da fitar dashi.  Kamfanin buga littattafan musulunci mai suna “International Islamic Publishing House” (IIPH) da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya ne ya dauki nauyin aikin gaba daya.

Fasahar Intanet

Na yi mummunar sabo da fasahar Intanet a daidai lokacin da nake cikin wadannan majalisu na Hausa.   Bayan zaman ofis da nake yi daga safiya zuwa magriba wasu lokuta, idan na koma gida ma sai naje mashakatar lilo da tsallake-tsallake, wato Cyber Cafe.  Wasu lokuta nakan kai karshe 11 na dare a can, sadda nake gwauro ba nauyin kowa a kaina.  Haka idan ranakun asabar da lahadi ne; duk inda wurin lilo yake sai na leka.   Wasu lokuta nakan rasa komai a aljihuna sai kudin lilo, wallahi haka zan hakura da cin makulashe, inje in shiga shagon lilo.  Wasu lokuta nakan taka a kasa daga unguwarmu zuwa Area 10 (ga wanda ya san birnin Abuja) – ya kai kusan kilomita 5 –  don yin lilo kawai.  Galibin lokuta idan ina da kudi, sai inyi kusan awanni 3 zuwa 4 ina lilawa, musamman idan yanayin sadarwar Intanet a wajen yana da kyau.

- Adv -

A lokacin babu wayar salula, ko akwai ma, babu tsarin Intanet mai inganci a ciki.  Wadannan shaguna na lilo su ne birjik.  Duk inda wani wurin lilo yake a birnin Abuja na sani.  Haka idan nayi tafiya zuwa wata jiha, abin mamaki, wurin farko da nake fara nema shi ne shagon lilo.  A kullum idan ban leka akwatin Imel di na ba, ba zaman lafiya.

Sarrafa Kwamfuta

Daga cikin abin da ke taimaka wa duk wani dalibi musamman mai bincike a fannin sadarwar zamani shi ne, iya rubutu da tsara shi, ta hanyar amfani da kwamfuta.  Ko a takaice kace: iya sarrafa kwamfuta wajen rubutu da kintsa rubutun.  Wannan shi ne abu na farko da ya kamata kowane dalibi ya koya a sadda yake koyon kowane irin ilimi, musamman na kwamfuta.  Idan ka iya sarrafa kwamfuta yadda kake so, ka samu matakin farko.  Na samu wannan alhamdulillahi a ma’aikatan da nake aiki.  Duk sadda babu sakatarenmu ni nake jigila da kwamfutar.  Tun ina yi ana mini gyara har aka wayi gari sai dai inyi wa wasu.  Ina godiya ga Allah kan wannan.  A halin yanzu, da ka bani kasida rubutacciya shafi goma, gwamma ka min lacca kan abin da kasidar ke kunshe dashi, kace in rubuta maka kasida mai shafi 30!  Duk wani abin da na fahimce shi na ilimi, idan na zauna a gaban kwamfuta ba na bukatar wata rubutacciyar takarda a gaba na.

Daga cikin kasidu sama da 300 da na rubuta kuma aka buga a shafin AMINIYA, kashi 85 daga cikinsu duk daga kwakwalwata nake hararo bayanan ina rubutawa.  Na samu wannan kwarewa ne ta sanadiyyar abubuwa biyu.  Na farko shi ne tsananin sha’awar da nake wa fannin.  Gani nake kamar duk duniya babu wanda ya kaini son kwamfuta (a lura, ban ce “sanin kwamfuta” ba, “son kwamfuta” nace).  Abu na biyu shi ne dacewar mahallin da nake aiki a ciki.  Yanzu shekaru na 13 da fara mu’amala da kwamfuta.  Cikin shekarun nan, na kwashe shekaru 8 daga cikinsu ina mu’amala da kwamfuta daga safiya zuwa yammaci (8am – 7pm) a kalla.

Zan ci gaba a kashi na uku.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.