Sakonnin Masu Karatu (2019) (8)

Hanyoyin "Upgrading" Wayar Salula Nau'in Lumia 1350

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Maris, 2019.

194

Assalamu alaikum, Baban Sadik Allah ya kara basira. Don Allah tambaya nake akan “Nokia Lumia 1350”; ana iya Upgrading dinta ta koma Android? Muna godiya. Yakub Z.

Wa alaikumus salam Malam Yakubu, barka dai.  Ina godiya da addu’a.  Ita wayar salula nau’in Nokia Lumia tana dauke ne da babbar manhajar “Windows Phone”, wanda kamfanin Microsoft ya gina kuma yake dora wa kwamfutocinsa.  Duk tsare-tsarenta na babbar manhajar “Windows Phone” ce, don haka a al’adance babbar manhajar “Android” bazai mata ba.  Amma duk da haka an samu wadanda suka yi yunkurin mayar da wayar salula nau’in Lumia zuwa Android, kuma sun dace, amma tare da wasu matsaloli masu yawa, wanda gwamma ma rashin yin hakan.  A tare da dacewar ma, ba dukkan nau’ukan Lumia bane ake iya dora musu babbar manhajar Android.  Nau’ukan Lumia da aka gwada kuma aka dace suka dauki babbar manhajar Android dai su ne tsofaffin nau’ukan Lumia, irin su: Lumia 520 da Lumia  521, da Lumia  525, da Lumia  526, sai kuma Lumia 720.

Bayan gwajin da aka gudanar kuma aka dace suka dauki babbar manhajar Android, wayoyin sun tashi, dauke da manhajar Android din, amma kuma fasahar Bluetooth ba ta yi.  Haka ma na’urar sauraron sauti (Earpiece) ba ta yi.  Haka ma manhajar daukar hoto (Camera) ita ma ba ta yi.  Mafi girman matsalar ma ita ce, bayan an dora musu babbar manhajar Android, an lura wayoyin duk basu iya kamo siginar rediyo, wanda dashi ne kowace wayar salula ke amfani wajen karba da amsa kira, tare da shiga Intanet.  Wannan ya faru ne saboda ka’idojin da aka gina asalin wayar sun sha bamban da tsarin da aka kintsa cikin babbar manhajar Android.  Kenan, akwai-ya-babu-ne.

Idan kana bukatar mayar da wannan wayar zuwa nau’in Android, zai dace ka kai wa masu gyara, wadanda suka kware wajen iya gyaran wayar salula.  Su zasu duba su gani, idan har zai yiwu a farke ta don dora mata babbar manhajar Android din, zasu sanar da kai.  Amma kamar yadda ka gani, wannan wayar da kake tambaya a kanta ba ta cikin wayoyin da aka yi ittifakin zasu iya karbar babbar manhajar Android.  In kuwa bai zai dole ba sai ka yi, shawarata ta karshe ita ce, ka sayar da ita sayi sabuwar wayar salula mai dauke da babbar manhajar Android.  Akwai su da yawa kuma masu inganci, wadanda zasu iya gudanar maka da duk abin da kake son wayar salula ta maka.

- Adv -

A takaice dai, su wayoyin salula kamar motocin hawa ne; muddin ba asalin injinsu bane ka dora musu, to, sai an samu matsala.  Da fatan ka gamsu da dan takaitaccen bayani na.  Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik.  Ni mutum ne mai sha’awan harkar intanet.  Amman ba ni da ilmi mai zurfi na zamani, sai harshen Hausa. Ta yaya zan yi burina ya cika?  Nuhu Adamu Nyalun, Wase, Jihar Filato.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nuhu.  Ta’ammali da fasahar Intanet bay a bukatar dole sai ka iya turanci.  A takaicen takaitawa ma dai, harshen turancin Ingilishi daya ne daga cikin harsunan da ake amfani dasu a Intanet duk duniya.  Bayan shi akwai harshen Mandarin (Chinese), da harshen Spanish da dai sauransu.  Tabbas wadannan harsuna sun fi shahara ne saboda galibin bangarorin Intanet da giza-gizan sadarwa na duniya tare da manhajojin dake tafiyar da fasahar, an tsara su ne cikin harsunan.  Wanda wannan ya sha bamban da harshen Hausa.

Duk da baka yi bayanin me kake nufi da cikan burinka ba, ina zaton kana nufin samun daman iya mu’amala da fasahar ne ko dai wajen sadarwa ko wajen kasuwanci da sauransu.  In don wannan ne, abin da kake bukata shi ne wanda zai dora ka a hanya.  Ka samu wanda zai karantar da kai a aikace, hanyoyin da za ka rika bibiya wajen yin abin da kake son yi.  Cikin kankanin lokaci zaka samu cikan burinka.  Idan kuma ban fahimci tambayarka bane sosai, to kana iya aiko mini sako na musamman sai in kira ka mu tattauna.

Ina maka fatan alheri a ko yaushe.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Mohammed Baba Idriss says

    Muna godiya da wannan gagarumin aiki naka na ilmantar da al’umma dangane da Kimiya da ma fasahar sadarwa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.