Sakonnin Masu Karatu (2015) (4)

Ci gaban sakonninku. A ci gaba da kasancewa damu, kuma a sha karatu lafiya.

136

Assalaamu alaikum, dan Allah Baban Sadik a taimakeni: na nemi Account dina na Facebook na rasa. Dan Allah ka taimakamin. Sunan dake Account din shi ne: “Muhammad Garba Mai Qara’i.”   Yadda abin ya faru kuwa shi ne, kawai na wayi gari zan shiga shafina sai naga: “Sorry, this page isn’t available. The link you followed may be broken, or the page may have been removed.”  Na yi kokarin dawo da shi amma ina, sai na kara bude wani Account din da sunana na farko wato “Muhammad Garba Mai Qara’i,” shi ma kwana biyu sai suka rufe shi.   Na yi, amma ina shi ne na bude wani da suna “Muhammad G. Mai Qara’i,” shi nake amfani da shi a yanzu, to amma sakamakon abubuwan da nake dashi a wancan shi yasa bana jin dadin wannan kodaya.  Dan Allah inda dama Baban Sadik a taimakamin.  –  Muhammad G Mai Qara’i.

Wa alaikumus salaam, babbar laifinka shi ne, sadda ka samu matsala da na farko, maimakon kayi kokarin gano mece ce matsalar, sai ka sake bude wani shafi da sunan irin na da. Wannan, a ka’idar Facebook, haramun ne, wato yin amfani da suna iri daya a account biyu.  Ko amfani da lambar waya (a matsayin sunan shiga – Username) a account biyu.  Ko amfani da adireshin Imel daya (a matsayin sunan shiga – Username) a account biyu.  Duk wannan, a ka’ida da dokar Facebook, haramun ne.  Abin da za ka iya maimaita shi a kowane lokaci, ko da sau dari ne, shi ne kalmar iznin shiga: Password.  Kana iya amfani da kalmar iznin shiga iri daya a account goma ma, ba biyu ba.  Amma wajen suna, dole ne kowane account da sunansa.  Shi yasa suka sake rufe wanda ka sake budewa daga baya mai suna iri daya da na farko.

Dangane da haka, baza su taba baka damar gyarawa ba.  Domin gani suke kamar kana kokarin hawa kan sunan wani ne, ba kai bane hakikanin mai sunan.  Wannan shi suke kira “Impersonation,” kuma hukumar Facebook ba su yin uzuri kan wannan laifi.  Don haka, hanya mafi sauki shi ne ka sake bude wani da wani suna daban.  Idan nace suna, ina nufin sunan da kake shiga dashi, ba wai sunanka da ka shigar wajen “First Name,” da “Second Name” ba.  Da fatan ka gamsu.


Salamun alaikum Malam, dan Allah ina da tambaya ne kan wani abin da yake daure min kai.  Tambayar kuwa ita ce: yaya ake jawo sunan mutum a tsakiyar “comment” ko kuma a tsakiyar “post,” ba farkonsa ba, ba kuma karshensa ba?  Na gode.  –  Abban Zeenat

Wa alaikumus salam, barka ka dai Abban Zeenat.  Ai wannan ba wani abu bane mai wahala.  Idan kana cikin rubutu, kuma ka bukaci ambaton sunan wanda kake son ka ambata, sai ka fara harafin sunansa na farko da babbar harafi (Capital Letter), kana gama rubutawa sai ka dan dakata, za ka ga sunayen abokananka masu suna irin wanda kake rubutawa sun bayyana nan take, sai ka zabi wanda kake so.  Da zarar ka zabi wanda kake so, nan take za ka ga sunan ya koma launin shudi, alamar rariyar likau kenan, wato: Link.  A nasa bangaren, za a sanar dashi cewa: “Wane ya ambaceka,” cikin harshen turanci.  A yadda sunansa yake kuma, da zarar ka matsa sunan, nan take za a kaika shafinsa kai tsaye.  Wannan ita ce hanyar da ake ambaton aboki a Facebook.

- Adv -

Sharuddan yin hakan kuwa su ne: ya zama wanda kake son ambato ya zama daya ne daga cikin abokanka.  Idan ba abokinka bane ko sunayen sun bayyana ba za ka ga nashi ba.  Na biyu, dole ne harafin farkon sunan da kake son ambato ya zama da babban harafi ne.  Rubuta harafin farko da karamin harafi bazai bayyana maka sauran sunaye makamantan nasa ba.  Sharadi na karshe, shi ne ya zama siginar Intanet dake waya ko kwamfutarka ta zama mai karfi.  Wannan zai taimaka wajen gaggauta bayyana sunaye makamantan wanda kake son ambato.  Amma idan siginar Intanet din ba ta da karfi, ko ka rubuta harafin farko da babban harafi, kuma yana cikin abokanka, sai an dauki lokaci mai tsawo kafin sunaye makamantan wannan su bayyana.  Idan ba ka da  hakuri, sai ka zabi wanda kake so, amma kuma illar ita ce, ba za a ambace shi ba balle sanarwa taje gare shi.  Da fatan ka gamsu.


Salaamun alaikum Baban Sadiq, yaya aiki?  Da fatan an wuni lafiya.  Don Allah tambaya nake kan: “Windows Linux,” shin, tsada gareta yasa ba’a samunta, ko bata shigo Nigeria bane?  A huta lafia.  –  Shamsuddeen Kabir

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Shamsuddeen.  Da farko dai, babu wata babbar manhajar kwamfuta mai suna: “Windows Linux,” ina kyautata zaton kuskure ne.  Abin da kake nufi shi ne: “Linux Operating System,” wato babbar manhajar Linux kenan.  Wannan babbar manhajar kwamfuta ce da galibi bata shahara a nan ba, amma ba wai wani tsada take dashi ba.  Tana da nau’uka daban-daban; wasu kan zo cikin kwamfuta sabuwa, kamar yadda babbar manhajar kwamfuta ta Windows ke zuwa a cikin sabuwar kwamfuta.  Shahararru daga cikinsu su ne: “Free BSD,” da “Fedora,” da “OpenSUSE,” da “CentOS.” Amma galibinsu sai dai ka saukar dasu kyauta daga shafukan intanet, irin su: “Ubuntu” wanda kamfanin Canonical ya samar, da “Kali Linux” (sabuwar nau’in Backtrack 5), da “Debian” da “Linux Mint,” da irin su “Puppy Linux.”   Wadannan duk kyauta ne.

Babbar manhajar kwamfuta ta Linux ta sha bamban da Windows ta fuskoki da dama.  Abin da yasa dai a takaice ba ka ganinsu ko ina a Najeriya shi ne, na farko dai kamar yadda na fada a baya, ba a cika sayar dasu cikin sabuwar kwamfuta ba kamar Windows.  Na biyu, galibinsu an fi amfani dasu a matsayin Uwar Gwarken (Server) gidan yanar sadarwa ne.  Kashi 90 cikin 100 na gidajen yanar sadarwar dake Intanet duk a kan kwamfutoci masu dauke da babbar manhajar Linux suke dore.  Hakan ya faru ne saboda ingancinsu, da nagartarsu, sannan suna iya jure aiki na tsawon lokaci.  Kana iya kunna kwamfuta mai dauke da babbar manhajar Linux ta kasance a kunne na tsawon watanni shida ko sama da haka.


Assalumu alaikum, da fatan kana lafiya, amin.  Ina matukar godiya bisa ga kokarin da kake yi na ilimintar da al’umarmu kan ilimin kimiyyar kwamfuta musamman.  Allah ya saka da alkhairi amin.   Bayan haka, ina bukatar idan da hali a duba yiwuwar dora mana yadda za a sarrafa manhajar PHOTOSHOP (CS6).  Na gode.  –  Hamisu Umar

Wa alaikumus salam Malam Hamisu.  Barka ka dai.  Wannan shawara ce mai kyau.  Kuma zan duba yiwuwar hakan kam.  Ba ma manhajar Photoshop kadai ba, al’ummarmu na bukatar sanin yadda ake amfani da sauran kannenta, irin su: Adobe Indesign (CS6), da Adobe After Effects, da Adobe Audition, da kuma Adobe Illustrator, musamman.  Wadannan manhajoji idan mutum ya karance su da yadda ake sarrafa su, ya samu sana’a mai karfi.  Domin yana iya aiki a gidajen wallafa littattafai, da kamfanonin jarida, da gidajen talabijin, da rediyo da duk inda ake sarrafa hotuna masu motsi ko daskararru.  In Allah yaso zan yi kokarin samar da bidiyo na musamman da kasidu dake karantar da yadda hakan zai iya samuwa.  Na gode matuka.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.