Sakonnin Masu Karatu (2015) (3)

Ci gaban sakonninku. A ci gaba da kasancewa damu, kuma a sha karatu lafiya.

112

Assalaamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana nan lafiya da iyalanka, ameen. Don Allah inaso ne amin bayani ne akan kalmar “Internet Protocol” a harshen hausa, mene ne aikinsa?  –  Abubakar Muhammad Garba

Wa alaikumus salam. Idan aka ce “Internet Protocol” ana nufin ka’idar fasahar da Intanet ke gudanuwa a kanta ne. Akwai ka’idoji da yawa. Misali, akwai “Internet Protocol” (IP) wacce ke lura da sadarwa tsakanin kwamfuta da wata kwamfuta a Gajeren Zangon Sadarwa (Local Area Network).  Akwai “Transmission Control Protocol” (TCP), wadda ita ma aikinta daya ne da ka’idar “IP.”  Sannan akwai “Hypertext Transfer Protocol” (HTTP) wanda ke lura da budo shafukan gidan yanar sadarwa ta amfani da rariyar likau. mai launi. Wadannam kadan ne cikin misalan.  Da fatan ka gamsu.


Assalam Babban Sadiq, muna godiya da irin gagarumin fadakarwa da kake a wannan dandali da shafin Jaridar Aminiya.  Allah ya kara hazaka ameen.  Ina so in yi amfani da wannan dama don neman izinin yin amfani da wani shafi ko shafuka na mukalarka a cikin feji na mai suna “Technology For Everyone.”  Kuma ko da yaushe zan ba da wa ilimi hakkinta wajen tabbatar da hakkin mallaka. Allah ya bar zumunci.  Ni ne naka Alyasa’a Hassan daga Bauchi. Nagode

Wa alaikumus salam, ba komai. na baka dama ka yada, ka dauka, ka diba kayi duk abin da kake so da rubutuna don ilmantuwa ko ilmantarwa. Allah sa mu dace, amin.


Mun gode Baban Sadiq.  Amma tambayata a nan ita ce: shin idan kana da kwamfuta mai dauke da babbar manhajar “Window 8,” za ka iya sanya mata “Window 10?”  In zai yiwu ta yaya za a yi wannan sauyi ya tabbata?  –  Muhammad Rabiu Isa Ayagi

Malam Rabiu barka ka dai.  Idan kana da kwamfuta mai dauke da Windows 8, za ka iya upgrading zuwa “Windows 10” in Allah Ya so.  Da farko, ka tabbatar cewa babbar manhajarka ta Windows 8 orijina ce, ba wai jabu (Pirated) bace.  Sai kaje bangaren “Windows Update,” ka jona kwamfutar da Intanet, sai ka matsa “Check for Update” nan take da kanta za ta nemo update har da Upgrade din baki daya.

- Adv -

Amma ka tabbata ka sa data mai yawa, musamman idan ya zama ka dade baka yi Update ba.   Idan ta dauko Windows Upgrade na Windows 10 din, za ka gani a jerin Updates din da ta nemo kafin ta loda wa kwamfutar, daga nan sai ka loda shi. Ba wahala. Allah sa a dace.  Kar ka mance, dole ne Windows 8 dinka ta zama orijina ce, ba jabu (Pirated) ba.   Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum, fatan alkairi da jinjina ga babban malami mai taimako a yau da kullum, sai dai muce Allah ya biya ka da gidan Aljanna.  Madaukaki ya kare ka da kariyarsa, ameen.  –  Hassan Sa’id

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Hassan.  Ina godiya matuka da addu’o’inku.  Allah saka da alheri ya kuma albarkace mu baki daya, amin.  Na gode. Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, da fatan kana cikin koshin lafiya.  Allah yasa haka amin. Ina da tambaya kamar haka: ina amfani da Wayar salula mai babbar manhajar Android ne wajen lilo a intanet, ta amfani da manhajar opera mini, to amma da zarar na shiga shafin BBC Hausa domin kallon bidiyo, sai ace mini: “Na’urarka na da matsala.”  Kuma na yi “Updating” din manhajar Opera ta.  –  Abubakar Muhammad Adam

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Abubakar.  Wannan matsala da kake fuskanta ba ta rasa alaka da manhajar da kake amfani da ita ko kuma nau’in bidiyo da kake son kallo.  Akwai nau’ukan bidiyo da yawa kuma ba kowace manhajar lilo ke iya bude dukkansu ba.  Wadannan nau’ukan bidiyo (Video Format) sun fi dari.  Don haka matsalar na iya zama daga wannan ce.  Ko kuma nau’in Opera Mini dinka; ta yiwu nau’in (Version) da kake amfani da ita ba ta iya bude irin bidiyon da kake son kallo a shafin.  Don haka, in da hali kayi amfani da wata nau’in browser din kawai.  Akwai nau’ukan manhajar lilo a wayar salula kala-kala.  Idan ka kasa amfani da wata nau’i, ka koma wata.  Wannan na cikin hikimar da tasa aka samu nau’uka daban-daban.  Dangane da cewa ka yi “Updating” manhajar Opera Mini dinka, wannan ba dalili bane kan cewa dole ka samu abin da kake so.  Idan dukkan dalilan da na zayyana a sama sun kubuta, to, ta yiwu kuma matsalar daga wayarka ce ta salula; sanadiyyar karancin ma’adana.

Yana da kyau ka san cewa, kallon bidiyo kai tsaye daga shafin Intanet (wato Video Streaming), yana bukatar ma’adana a cikin wayarka, duk da cewa ba saukar da bidiyon za ka yi ba.  A duk sadda ka matsa hoton bidiyo daga shafin Intanet, kafin ya fara nunawa, sai ya tattaro bayanan kai tsaye zuwa cikin wayarka, a ma’adanar wucin gadi (Temporary Folder), kafin ya fara nuna maka a shafin waya.  Don haka, idan ma’adanar wayarka babu yawa, ma’ana abin da ya rage na wuri kenan, wayar ba za ta iya taskance maka abin da kake son kallo a fuskar wayar ba.  Da fatar ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.