Sakonnin Masu Karatu (2014) (4)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

97

Assalamu alaikum, don Allah malam ina bukatar ayi mini cikakken bayani game da yadda ake “Boost din “Post a cikin Shafi (Facebook Page) din da mutun ya hada na kansa.  Domin idan nayi post mutane da yawa ba su gani.  Sai ace mini: “Boost this post,” idan na shiga sai a ce mini in sa lambar kati Visa da dai sauransu.  – Abdullahi Garba Shalos: abdullahigarbashaloss@hotmail.com

Wa alaikumus salam Malam Abdullahi, barka da warhaka. Kalmar “Boost Post” na ishara ne ga wani tsari da hukumar Dandalin Facebook ke amfani dashi wajen “habaka” sakonnin da masu shafin facebook (Facebook Page) ke rubutawa a shafinsu, don baiwa mutane da dama ganin sakon, da karanta shi ko bashi mahimmanci.  Wannan tsari na habaka sakonni ba kyauta suke yinsa ba.  Sai ka biyu kudi, shi yasa kake ganin bayani kan Visa Card da dai sauransu.

A ka’ida, idan ka bude shafi a Facebook, kana iya gayyatar dukkan abokanka don su “So” shafin, wato “Like” kenan.  Iya yawan wadanda suka so shafin iya yawan wadanda za su rika ganin sakonka idan ka rubuta.  Idan mutane miliyan daya ne suka so shafinka, to, wannan na nuna cewa da zarar ka yi rubutu ka cilla a shafin, akwai tabbacin mutum miliyan daya za su ga sakon kenan.  Ba su kadai ba, hatta abokansu suna iya ganin abin da su suka so, wanda kuma hakan ma wani tsari ne da ke baiwa shafinka daman samun karin “Masoya” araha babu ko kwabonka.  To amma hakan ba abu bane mai sauki a aikace.  Kafin mutane masu dimbin yawa su so shafinka cikin dan kankanen lokaci yana bukatar jajircewa a bangarenka, wanda kuma ba kowa ke da wannan hikima, da basira, da fasahar nemo mutane su so shafinsa ba.

Wannan tasa hukumar Facebook suka bullo da tsarin “Boost Post.”  Kare da kudinsa, in ji Hausawa, ya sha rubutu.  Idan kana son a rika habaka maka sakonninka cikin sauki ka biya kudi, sai ka matsa wannan alama ta “Boost Post,”  nan take za a kaika wani shafi inda za ka zabi yawan mutane, da farashin da kake son a aiwatar maka da aikin.  Kudaden ana biyansu ne a tsarin Dalar Amurka ba Nairan Najeriya ba.  Don haka, idan ka zabi iya lokaci (daga kwana daya ne zuwa shekara idan kana so), sai a kai ka inda za ka shigar da lambar katin ATM dinka, da nau’insa – VISA ne ko MASTERCARD.  Sannan a can kasa za ka zabi ko kana son idan lokacin da ka diba ya kare, a sake yanko wani lokaci irinsa ba tare da sai ka bukata ba (wato “automatic resubscription” kenan).

Da zarar ka gama cikewa, nan take za su zare kimar kudin, bankinka zai turo maka sako kan adadin kudin da wannan hidima ya hadiye.  Sauran bayani kuma sai ka saurare su.  Su suka san yadda zasu rika tallata maka shafinka, kana samun “masoya” cikin sauki, har zuwa kadadar lokacin da ka diba.  Da fatan ka gamsu da wannan dan takaitaccen bayani.


Assalamu alaikum Baban Sadik, tsawa lokacin ruwan sama a mahangar musulunci, ance tasbihin mala’iku ne. To meye dalilin tsawa a mahangar Malaman kimiyya? 

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam. Da fatan an wuni lafiya.  Ban da tabbaci kan zancenka na farko kan dalilin samuwar tsawa a mahangar musunculi, cewa tasbihin Mala’iku ne.  Amma dangane da iya binciken malaman kimiyya, sun nuna kafin samuwar tsawa, akwai haske da ke bayyana, wato walkiya kenan kamar yadda muke cewa, daga nan sai samuwar rugugi mai karfi mai girgiza da muke kira cida a harshen Hausa, bayan cida ne kuma sai sautin tsawa ya biyo baya a karshe.  Haka abin ke biye, kamar yadda muke ji ko gani.  Amma a hakika, lokaci guda duk suke samuwa.  Meye dalilin samuwar tsawa?  Yaya walkiya da rugugin cida ke rigar sautin tsawa?

- Adv -

Wannan tambaya da ka mini, irinta aka yi wa Farfesa Richard Brill da ke Kwalejin Honolulu (Honolulu Community College) a kasar Amurka, cikin shekarar 2000, wanda kuma Mujallar “The Scientific American” ta buga a shafinta a watan Disamba na shekarar 2002.  Ga nassin amsar da ya bayar nan kai tsaye na fassaro maka:

“Abin da ke haddasa samuwar tsawa shi ne walkiya, wanda asali yake dauke da  cunkoson sinadaran “Electron” dake makare a cikinsa ko a tsakanin giragizai, ko kuma tsakanin giragizai da mahallin da muke rayuwa a ciki a wannan duniya tamu.  Nau’in iskar da ke gewaye da wadannan sinadaran “Electron” kan yi zafi (sanadiyyar zafin rana), zafi mai tsananin da ya kai kimanin digiri 50,000 a ma’aunin zafi na farahait (50,000F), daidai da zafin rana ninki uku kenan.  Da zarar wannan iska mai dan karen zafi ya fara hucewa, sai ya samar da wata jakar iska a gewaye da titin da iskar ke bi.  Nan take sai iskar da ke makwabtaka da wannan jakar iska ta rika fadada tana tsukewa, tana fadada tana tsukewa (expansion and contraption), lokaci-lokaci.  Wannan ke sa jakar iskar da ke gefe ta rika girgiza cikin batsewa, hakan kuma yana haifar da sautin tsagewa.  Da zarar wannan girgiza ta fara lafawa, sai ta haifar da wani sauti mai tsakanin kara da muke kira Tsawa.

Muna iya jin masifaffen sautin tsawa da bugawarsa daga tazarar mil goma (kilomita 13) ko sama da haka daga hasken da ke haddasa tsawar.  Sannan idan walkiya ta auku a iya tazarar da ake iya ganinta, ita muke fara gani (ba sautin rugugin cida ko tsawar ba), domin gudun sauti a cikin haske bai kai gudun sinadaran “Electron” da gudanuwarsa ba. Shi yasa ma sautin tsawar ke aukuwa kamar sautin hatsarin wutar lantarki (Shockwave), ba kamar sauti irin wanda da aka sani na al’ada ba.  Shi wannan sauti mai kama da sautin hatsarin wutar lantarki yana bibiyar titin wannan sinadarin “Electron” ne (a yayin da yake aukuwa) kamar yadda dunkulen yatsu ke tasiri a jiki yayin da aka naushi mutum.

Bayan haka, gudun sauti ba komai bane idan aka kwatanta shi da gudun haske.  Hasken da ke samuwa a yayin walkiya na riskarmu ne (a wannan duniya) cikin kasa da dakika (second) guda, a yayin da sautin ke biye dashi cikin saibi da nawa, kai ka ce dodon kodi ne ke biye da jirgi nau’in roket dake shawagi a tsakanin duniyoyi.  Don haka, yanayin sauti da haske da ke samuwa a lokacin walkiya da tsawa hadaka ne na abin da ke samuwa sanadiyyar girgizan da sinadaran iska ke yi wajen hargitsa karfin sinadaran lantarki.  Wannan wani al’amari ne mai matukar ban mamaki hakika, kuma wannan ke dada tunatar damu duka cewa mu ba komai bane idan aka gwama halittarmu da na sararin samaniya.”


Salaamun alaikum, don Allah yaya zan yi in bude Mudawwana (Blog Page). Saboda ina son zama Blogger.” –  Mubarak Elanwar Kano

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Mubaarak.  Idan kana bukatar bude shafin Mudawwana ko Taska, abu ne mai sauki.  Ka je daya daga cikin gidajen yanar sadarwa da ke da manhajar shafin Mudawwana a Intanet, misali, WordPress (www.wordpress.com) ko kuma na kamfanin Google mai suna Blogger (www.blogger.com) don yin rajista.  Idan ka tashi yin rajista za a bukaci adireshin Imel.  Idan na Blogger ne dole sai kana da adireshin Imel na kamfanin Google, wato Gmail kenan.  Kana iya yin rajista a http://mail.google.com kyauta. Idan kuma na kamfanin WordPress ne, duk adireshin Imel din da ya sawwaka kana iya amfani da shi.

Bayan ka yi rajista, za a zarce da kai zuwa shafinka, daga nan sai ka tsaya shi yadda kake so, ka ci gaba da zuba dukkan ra’ayoyinka.  Dangane da zama “Blogger” kuma, wato Marubuci na musamman a Mudawwana, wannan abu ne mai sauki muddin za ka juri rubutu, da karanta ra’ayoyin wasu, da yawo cikin duniyar ilimi kan fannin da kake da sha’awar rubutu ko zama “Blogger” a kai.  Allah sa a dace, ya kuma sa a dabi’antu da juriya da hakuri, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.