Sakonnin Masu Karatu (2014) (5)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

62

Zuwa ga Baban Sadik, da fatan kana lafiya Allah ya kara maka basira.  A gaskiya na kasance ma’abocin sauraron gidanjen rediyo ne.  Hakan ya sanya nake kokari wajen tura sakonnina domin in bayyana ra’ayi na amma abin takaici ba su karanta sakonni na, duk cewa suna nuna sun isa wato “Delivered”; duk da kokarin da nakeyi wajen kyautata rubutu na. Don haka nake son ka bani shawara, na gode. – Bello Isiyaku, Birnin-Fulani

Barka ka dai Malam Bello.  In na fahimci sakonka da kyau, kana nufin a duk sadda ka tura sakonninka, wayarka na sanar da kai cewa sakon ya isa.  Amma kuma ba a karanta sakonninka.  Eh to, tunda har waya ta sanar da kai cewa sako ya isa lafiya, ba na tunanin akwai matsalar yanayin sadarwa, wato Network Problem, ta yiwu tambayoyin naka ne basu gamsar dasu ba, ko basu zo kan sakon naka ba, saboda yawaitan sakonnin da suke karba, ko kuma a kalla basu cika ka’idar da suka gindaya ga sakon da ya cancanci a karanta shi ba, kafin amsa shi. Ko kuma, a karo na karshe, watakila sun sha amsa tambayoyi makamantansu a baya.

Ala ayyi halin, dole ne ya zama akwai dalili mai karfi wanda kuma kamar yadda ka sani, ba abu bane mai yiwuwa su iya sanar da dukkan masu turo sakonni dalilin rashin karanta sakonninsu ba.  Sai dai ince ka ci gaba da kokari da kuma juriyar aikawa, watakila nan gaba za a dace su karanta.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, da fatan alheri gare ka kuma ka yi sallah lafiya, amin.  Allah ya raya mana iyali su zama masu albarka.  Bayan haka, don Allah Baban Sadik ina so a min karin haske; ina so na koyi sana’ar abin da ya shafi gyara babbar manhajar wayar salula (Mobile Operating System Formatting) da filashin manhajar, da kuma yadda ake bude babbar manhajar idan ta kulle, ta hanyar kwamfuta.  Wace hanya zan bi?  Sannan dole ne sai na shiga makarantar koyon kwamfuta?  A cikin bayanin takaitaccen tarihin rayuwarka, na ji ka ce da jangwale-jangwale ka koyo ta, wato kwamfuta kenan.  Sannan ina so in sani, ko ban je makarantar kwamfuta ba, zan iya sarrafa ta a aikace?  Da fatan za ka daure ka ban amsa.  –  Yahuza Idris Hotoron Arewa.

Wa alaikumus salam, Malam Yahuza Idris barka ka dai.  Ina godiya matuka da addu’o’inku, Allah saka da alheri, amin.  Koyon wannan sana’a abu ne mai kyau matuka, musamman ganin cewa babu abin da yafi yaduwa a al’ummarmu yanzu daga cikin kayayyaki ko na’urorin sadarwa irin wayar salula.  Don haka, koyon yadda ake gyara su, da gano matsalolin da ke addabarsu, abu ne mai matukar mahimmanci, bayan samar da aikin yi ga matasa.  Wannan kenan.

A daya bangaren, koyon wannan sana’a ko fannin ilimi ba wani abu bane mai wahala, matukar mai koyo ya sa hankali da ransa a kan lamarin.  Akwai wurare da dama da ake koyar da gyaran wayoyin salula.  Akwai cibiyoyin koyar da sana’o’i da gwamnatocin arewacin kasar nan da dama suka samar, karkashin shirin gwamnati na samar wa matasa abin dogaro da kai.  Idan baka samu damar shiga wadanann cibiyoyi ba, akwai masu gyaran wayoyin salula kamar yadda muke da masu gyara rediyo da talabijin, birjik.  Daga cikinsu akwai masu gyara babbar manhajar wayar salula ta amfani da masarrafan filashin din wayar salula, wato “Mobile Phone Flashing Software.”  Kana iya shiryawa dasu, ka biya su kudin hidimar karantar da kai da za su yi, sannan su karantar da kai.

Da zarar ka gama wannan karatu, dole ne ka mallaki kayayyakin aiki, wanda na san malaminka zai sanar da kai.  Za ka bukaci kwamfuta, musamman dai ta tafi-da-gidanka, wato Laptop kenan, da dukkan abin da zai sawwake maka mu’amala da ita.  Sannan za ka mallaki masarrafa ko manhajar da ake yin filashin din babbar manhajar wayar salula, kamar yadda bayani ya gabata a sama.  Wannan masarrafa na zuwa ne da wayoyin USB da ake makala su a jikin wayar da za a mata filashin don riskar babbar manhajar.  Dole ne su karantar da kai cewa kowane kamfanin wayar salula yana da nasa nau’ukan wayoyin USB.  Nokia da nasu.  Samsung da nasu.  Sony da nasu, har dai zuwa karshe.

- Adv -

Bayan haka, za ka mallaki manhajar bude wayar salular da ta kulle kanta ko mai ita ya kulle ta cikin kuskure ko ya mance kalmomin sirrinsa ko isharar da ake bude wayar da ita, wato “Security Lock Pattern” kenan, ga nau’ukan wayoyi masu amfani da babbar manhajar Android.  A takaice dai, dukkan kayayyakin aiki za ka mallake su kafin fara aiki.

Dangane da tambayarka kan ko mutum na iya mu’amala ko sarrafawa ko kuma koyon kwamfuta ko da bai yi karatun boko ba, sai ince maka eh, mutum na iyawa.  Abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.  A wajen koyon wancan ilimi ko sana’a, dole za a koya maka yadda ake mu’amala da kwamfuta, da yadda za ka sarrafa ta wajen aiwatar da dukkan ayyukan da ake so.  Har wa yau ka fahimci wani abu daya, shi ilimin kwamfuta na da bangare biyu ne; akwai bangaren karatu da nazari.

Sannan akwai bangaren aikata karatun a aikace.  Kowannensu yana da mahimmanci, musamman bangaren aikata karatun a aikace.  Domin kana iya mu’amala da kwamfuta ko baka taba zuwa makaranta ba.  Amma ba za ka taba iya samun shedar karatu a fannin kwamfuta ba tare da kaje makaranta ba.  Kamar yadda kaji na fada a baya, ban taba zuwa makarantar koyon ilimin kwamfuta ko wayar salula ba  a rayuwata.  Duk da cewa ban fid da rai da hakan ba nan gaba, saboda wasu dalilai da suka shafe ni.  Amma a tare da haka, iya gwargwado na fahimci wannan ilimi fiye da tunanin wanda yaje jami’a ya kware a wannan fanni.  A hakan da nake ina sa ran zan iya karantar da ko da ‘yan jami’a ne, kan wannan ilimi na fannin kwamfuta.  Abin da kake bukata shi ne, ya zama kana da sha’awar lamarin, sha’awa mai karfi, ba mai rauni ba.

Na biyu, ka yawaita mu’amala da kwamfuta.  Na uku, ka yawaita tambaya da neman karin bayani wajen kwararru kan wannan fanni.  Na hudu, ka samu wanda zai rika koya maka yadda ake mu’amala da wannan na’ura ta kwamfuta a aikace.  Duk wanda zai koya maka amfani da wannan na’ura, zai koya maka ne kamar yadda ake karantar da ita a rubuce.  Don haka, duk wanda ya ga kana mu’amala da kwamfuta bayan ka kware, zai dauka makaranta kaje ka koya.  Me yasa?  Don wanda yaje makarantar ne, ko wanda ya koye ta a karance ne ya karantar da kai.  Da fatan ka gamsu wannan dan gajeren bayani.


  Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan an yi sallah lafiya.  Wai don Allah da akwai wata manhajar kwamfuta mai suna “Data Analysis?” –  Abdullahi Bashir Dawud

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Abdullahi. Da fatan kai ma ka yi sallah lafiya.  Kalmar “Data Analysis” wani fanni ne na musamman da ya kunshi neman bayanai, da tattaro shi, da kintsa shi, da tace shi, da kuma tsara shi yadda ake so don samar da natija ko bayar da damar yanke hukunci kan sakamakon da bayanan suka bayar.  Ba wai sunan wata manhaja bace.  Sai dai kuma, akwai manhajojin kwamfuta masu dimbin yawa da aka gina su don aiwatar da wannan aiki mai matukar fa’ida a wannan zamani namu.  Ire-iren wadannan manhajoji ana amfani da su a ma’aikatu, da masana’antun gwamnati, da makarantu, da kuma gama-garin mutane masu sha’awar wannan fanni, don aiwatar da wadancan ayyuka da na zayyana a baya.

Daga cikin wadannan manhajoji akwai manhaja mai suna “R”, da “SPSS” (Statistical Package for Social Sciences) wanda galibin daliban jami’a ke amfani da ita wajen nazarin bayanan da suka tara yayin gudanar da bincikensu, sannan akwai kanana irin su “Microsoft Excel” na kamfanin Microsoft, wadda shahararriya ce.  Kamar yadda nace a sama, ire-iren wadannan manhajoji suna da yawa, sun kai dari, kuma idan dalibi ya koyi mu’amala dasu wajen nazarin bayanan da ya tara a yayin gudanar da bincikensa, suna taimaka masa matuka.  Domin da zarar ka tsamo bayanai masu mahimmanci da kake son yin nazari kansu, kana aika wa manhajar ka matsa maballi guda, nan take za a tace bayanan, a turo maka amsa kai tsaye wanda zai baka haske kan abin da kake nema.  Da fatan ka gamsu da wannan gajeren amsa nawa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.