Hattara, Ana Iya Satar Tunaninka Nan Gaba!

Ci gaban kimiyyar sadarwa da na halitta sai kara gaba suke. Wani bincike na nuna nan gaba ma, ana iya sace wa mutum tunanin dake kwakwalwarsa. Mai karatu, ka ji wannan batu kuwa?

273

Idan aka ambaci ‘yan Dandatsa a zamanin yau, ba abin da mai karatu ke iya tunawa a yau face ‘yan fasakwaurin bayanai ta hanyar kwamfuta da Intanet; masu ta’addanci cikin kwamfutocin mutane suna sace bayanan sirri da ke cikinsu, tare da haukatar dasu ko barnatar da duk wani abin da suka ga damar barnatarwa, kafin su fice.  Sai dai kuma, wani abin da mai karatu ba zai yarda ba idan aka fada shi ne: akwai yiwuwar sace wa dan adam tunaninsa daga kwakwalwarsa, ba tare da saninsa ba, ta amfani da na’urorin sadarwa da taskance bayanai na zamani.

A cikin shirinsa na musamman mai take: Through the Wormhole, wanda tashar kimiyya mai suna The Science Channel ke gabatarwa a duk mako, shahararren jarumin fim Morgan Freeman ya hankado yiwuwar hakan a yau da kuma nan gaba.  Dangane da tattaunarsa da shahararrun masana harkar kimiyya da kwakwalwa, a fili yake cewa nan gaba ba zai zama da wahala ba, kuma ba zai zama abin mamaki ba a sace wa mutum tunaninsa da yake yi a cikin kwakwalwarsa, ko a iya fahimtar tunanin da yake yi, sannan in so samu ne ma, a iya gurbata tunanin, ta hanyar shigar da wasu nau’ukan tunanin ko hargitsi irin na sauti ko wani abu makamancin haka, don gurbata masa tunaninsa. A takaice dai, nan gaba za a iya satar tunaninka, ko a gurbata shi, ko kuma a yi fasakwaurin bayanan ma, kamar yadda ‘yan Dandatsa (wato Compiuter Hackers) ke satar bayanai daga kwamfutoci a wata uwa duniya a yau.  Tirkashi!  Wani abin sai ilimi, ba sihiri bane, ba kuma da’awar sanin gaibi bane.

Philip Low, shahararre ne a fannin sirrin kwakwalwa da maganadisunta, wato Neurotechnologist.  A halin yanzu yana aiki ne kan wata ‘yar karamar na’ura wacce za a iya amfani da ita wajen “karanta” siginar bayanan masu kwakwalwa, masu dauke da nau’ukan tunanin da mai kwakwalwar ke yi a halin da yake tunanin.  Wannan na’ura mai suna iBrain, za ta iya taskance siginar bayanan  kwakwalwar mai kwakwalwar (Brain Siginals) da zarar am dora ta a saman kokon kai.  Nan take za ta fara karanto siginar kwakwalwar, don aikawa dasu cikin kwamfuta, inda za a iya ganinsu, tare da fassara su don gano me suke nufi. Mista Low yace amfanin wannan na’ura shi ne taimaka wa wadanda suke da matsalar shanyewar hannu sanadiyyar cutar da ta same su, musamman cutar Alzheima.  Yace masu irin wannan cuta suna dauke ne da hannun roba, wacce idan suka dora wannan na’ura a saman kokon kansu, tare da jona ta da kwamfuta, nan take siginar kwakwalwarsu za su fara bayyana a shafin kwamfutar.  Ya ce wannan zai taimaka musu wajen gyatta tunaninsu wajen sarrafa wannan hannu nasu na roba.  To amma kuma ta yaya za su iya fahimtar abin da wadannan siginar bayanai ke nufi, wanda hakan ne zai bayyana musu tunanin da suke yi?

- Adv -

Wannan abu ne mai sauki, a cewar masanin kimiyya Mista Jack Gallant, wani shahararre kan kimiyyar kwakwalwar dan adam (Neuroscientist). Domin a halin yanzu aikin da yake yi kenan, ma’ana gina wani kamus na musamman, mai dauke da yaren siginar kwakwalwa na musamman, wato Brain Dictionary.  Wannan Kamus, a cewar Gallant, shi zai fassara dukkan wani sigina na kwalwalwa da mai kwakwalwar ke gani a shafin kwamfuta, don bashi ma’anar da siginar ke ishara gare ta, cikin hotuna da rubutattun bayanai.  Masanin ya yi hakan ne ta hanyar wani gwaji da ya fara, inda ya ajiye mutane da dama, tare da lura da siginar kwakwalwasu a lokacin da ya basu dandazon hotuna daban-daban, suna kallo, shi kuma yana nadar irin tunanin da suke yi a tsarin siginar kwakwalwa, cikin sauki.  Mista Gallant ya yi amfani ne da na’urar taskance siginar kwakwalwa na zamani mai suna functional Magnetic Resonance Imaging (fMRI).  Yace a halin yanzu sunan nan suna ta kokarin gina wasu ka’idojin hasashen tsarin tunanin mutanen kan hotunan da suke kallo.

A daya bangaren kuma, wasu masana sun tabbatar da cewa nan gaba kana iya satar fasahar kwarewa daga kwakwalwar mai kwakwalwa a sadda yake aiwatar da sana’a ko aikinsa.  Misali, idan Tela yana dinki, ga kwakwalwarsa a jone da kwamfuta ana taskance siginar kwakwalwarsa, masana suka ce abu ne mai sauki ka iya gane sadda kwakwalwarsa ta kai makura wajen tunanin yadda yake tafiyar da aikinsa, cikin kwarewa.  Wannan tsari, a cewar Chris Berka, na iya taimaka wa mai tunanin, ta hanyar nazarin fassararren siginar kwakwalwarsa a sadda yake tafiyar da aikinsa, don gane sadda nau’in tunanin da ke samar masa da kwarewa ke cika, da sadda yake raguwa, don bashi daman tabbata a marhalar cika.  Ga wanda ke son “sace” wa Tela tsarin tunaninsa kuwa, Berka yace wannan abu ne mai sauki.  Tirkashi! To amma bayan sace tunanin a sadda mai tunanin ke yinsa, ana iya gurbata shi?

Eh, inji shahararriyar masaniya a fannin ilimin dabi’a, Ilana Hairstone.  Tace ana iya hakan ma ba tare da sanin mai kwakwalwar ba.  Kamar yadda ‘yan Dandatsa (Hackers) ke amfani da “kafa mai rauni” tsakanin hanyoyin sadarwar kwamfuta, wato Cracks, to haka za a iya amfani da “kafa mai rauni” tsakanin hanyoyin sadarwar kwakwalwa, wato Brain Pathways, don shigar da wasu bayanai a tsarin sauti ko makamantan haka, zuwa cikin kwakwalwa, har ya saje da sauran nau’ukan tunanin da mai kwakwalwar ke yi.  Daga cikin kayan aikin da za a iya amfani dasu wajen fahimtar kafa mai rauni a kwakwalwar mutum, inji Hairstone, akwai dabi’ar “sinsino.”  Wannan dabi’a na sisino na iya taimakawa wajen shigar da bayanai cikin kwakwalwa.  Ilana Hairstone ta gudanar da gwaji na musamman kan wannan al’amari, tare da tabbatar da yiwuwarsa.  Abin kamar almara.  Tace an tanadi mutane ne, aka umarce su da yin bacci, sannan aka fara taskance siginar kwakwalwarsu a sadda suke baccin.  Ta amfani da dabi’ar sinsino, Ilana Hairstone ta shigar da wasu bayanai a yanayin sigina, wadanda suka bi ta hanyar sadarwar kwakwalwa, don isa cikin rumbun tunanin masu kwakwalwar.  Wannan ke nuna cewa da zarar sun farka, ana iya samun nau’in bayanan da aka shigar musu kwakwalwa, idan aka musu tambayoyi masu alaka da su.  Allah buwayi gagara misali.

Wannan ke nuna cewa nan gaba akwai yiwuwar gurbata wa masu lefi tunaninsa ba tare basu wani abu na barasa ko amfani da tasirin wutar lantarki ba, don cinma wasu manufofi.  Allah ka daidaita mana fahimtarmu, tare da bamu dacewa cikin dukkan lamuranmu baki daya, amin.    

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Yusu Salisu says

    Allah ya taimaka

  2. Yusu Salisu says

    Allah ya taimaka wajen taimakawa matasa akan ilimin zamani

Leave A Reply

Your email address will not be published.