Sakonnin Masu Karatu (2014) (14)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

113

Assalaamu alaikum, Baban Sadik don Allah a aiko mini da kasidar nan ta “Tsibirin Bamuda” zuwa adireshin Imel di na da ke: abdulrahmani42@yahoo.com. Daga: 08093476575

Wa alaikumus salam, Malam AbdurRahman barka ka dai. Sai ka duba akwatin Imel dinka, tuni na cillo maka kasidar. Allah sa a amfana da abin da ke ciki, amin.  Na gode.


Salaamun alaikum, da fatan Baban Sadik yana lafiya tare da daukacin ‘yan makaranta baki daya.  Tambayata ita ce: don Allah meye ma’anar wannan kalma ko haruffa ke nufi: .ng wacce take zuwa a kashen sunan layin adireshi kamar www.glo.com.ng.  Allah ya baka ikon amsawa, amin.  Daga: Rahinat, Kano.

Wa alaikumus salam, barka da warhaka.  Wannan harafi ko haruffa da ake gani, wato .ng ana kiransa “Top Level Domain Name.”  Bangaren karshe ne na adireshin gidan yanar sadarwa, wanda ke da rajista da asali a Najeriya.  Lafazin ng na nufin Najeriya ne.  Na kasar Amurka shi ne gov.  Na kasar Ingila kuma .co.uk.  Na kasar Kanada kuma .ca.  Na kasar Afirka ta kudu kuma .za.  Kowace kasa a duniya tana da nata wanda ya kebance ta.  Da fatan an gamsu.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki kuma yaya fama da jama’a?  Allah dai ya saka maka da alheri, amin.  Wai don Allah ko akwai wata na’ura da za ta iya taskance magana ta mayar da maganar zuwa rubutu?  Ina nufin idan ana wani bayani ko hira sai ya rika zama rubutu.  Daga: Muhammad Musa, Bachirawa K/Ungogo Fasaha Communication Center.

Wa alaikumus salam, da fatan kana lafiya. Lallai akwai masarrafa ko manhaja ko na’ura wacce ake jonawa da kwamfuta, don mayar da bayanan sauti ko na bidiyo, zuwa rubutattun bayanai.  Na’urar da ke wannan aiki ana kiranta da suna “Transcription Machine.”  Manhaja ko masarrafar kwamfuta mai wannan aiki kuma sunanta: “Transcription Software.”  Wannan tsari yana da muhimmanci matuka, kuma da shi ne galibin lokuta ake amfani wajen mayar da galibin tarurruka da majalisin ilimi na manyan malaman duniya a yau, zuwa rubutattun littattafai.  Da zarar an shigar wa kwamfuta wannan masarrafa, sai a budo jakar bayanin da ke dauke da wannan bayani, ita kuma nan take kawai sai ta kama rubuce jawaban sautin ko bidiyo.  Daga magana, zuwa gyarar murya, zuwa tari, duk sai ta rubuce.  Daga baya sai a bi su daya bayan daya, a gyara abubuwan da ta rubuce su. Wanda ake bukata a barshi, wanda kuma ba a bukata sai a cire.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu alaikum, da fatan alheri. Allah ya taimaki Baban Sadik, amin.  Tambayata ita ce: na ga idan ina hirar ga-ni-ga-ka na facebook (Facebook Chat), sai na ga wani koren digo a gefen sunayen abokaina, wasu kuma in ga alamar wayar salula.  Me wannan ke nufi ne?  Daga: Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Gidan mai mangwaro. 

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Yahuza.  Duk wanda ka ga alamar kore a kusa da sunansa, to alamar ya hau manhajar facebook kai tsaye kenan.  Don haka kana iya tuntubarsa kuyi hira, in har ba a shagale yake ba.  Haka duk wanda ka ga alamar wayar salula a kusa da sunansa, shi ma yana nan kai tsaye.  Sai dai ya dakile tsarin da ke nuna wancan alama ne don kada jama’a su dame shi.  Ko kuma bai ma san tsarin a kashe yake ba.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina da wayar nau’in Blackberry, wai dole ne sai na sayi layi kafin in rika saukar da abubuwa daga Intanet (Downloads) da shiga Facebook?  Domin idan nazo shiga yanzu sai a ce mini: “Set up your wi-fi.”  Na gode. Daga: Usman Muazu Funtua, Katsina.

Wa alaikumus salam, Malam Muazu, muddin kana da kudi a wayar ya kamata a ce kana iya mu’amala da fasahar Intanet ko da baka sayi layin wata ba (Subscription) daga kamfanin waya.  Amma sai dai kudin da ke katin waya ne za su rika zaftarewa babu kakkautawa.  Ta yiwuwa shi yasa ba ka iya saukar da wani abu, tunda hakan na bukatar kudi mai yawa a wayarka, ko kuma kana da tsarin mu’amala da fasahar Intanet tsakaninka da kamfanin waya.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum, Malam yaya ake hada kwamfuta da kwamfuta a zangon sadarwa (network).  Daga Zayyanu Yarima, Abuja.

Wa alaikumus salam, wannan tambaya ce mai girma wacce ke bukatar darasi mai zaman kansa, kamar yadda nayi a baya.  Hada kwamfutoci don su aiwatar da sadarwa a tsakaninsu a Gajeren Zangon Sadarwa (Local Area Network) abu ne da ke bukatar abubuwa da dama.  Wannan tsari shi ake kira “Networking” a fannin ilimin kwamfuta da sadarwar zamani.  Mafi karancin adadin kwamfutocin da ake bukata dai daga biyu ne, sannan ana bukatar na’urorin aiwatar da sadarwa tsakanin kwamfutoci, irin su “Router,” da “Switches,” da “Network Hubs,” sai kayayyakin aiki irin su wayoyin kebul nau’in “RJ45”, da na’urar gwajin lafiya da ingancin kebul, wato “Cable Tester,” da dai sauran kayayyaki.  Idan ba a bukatar kwamfutocin su jonu da Intanet, to a nan ba a bukatar na’urar “Router.”

Bayan an tanadi wadannan kayayyaki, sai ayi nazarin irin tsarin da ake so, wato “Netowork Topology.”  Daga nan sai a jojjona kwamfutocin ta amfani da wadancan kayayyaki da bayaninsu ya gabata.  Idan aka gama jojjona su a fili, sai a shiga masarrafar kwamfutar da ke kowace kwamfuta, a hada alaka a tsakaninsu ta yadda za a iya karbar bayanai daga kowacce, a kuma iya aika wa kowacce.  Amma dole ne a samu guda daya wacce ita ce uwar garke; mai dauke da masarrafar musayar bayanai a tsakanin sauran kwamfutocin, wato “Server” ko “Host”, sauran kuma sun zama “Clients” kenan.

Har wa yau, idan masu amfani da kwamfutocin dake wannan Zango sun sha bamban wajen martabar karba da tura bayanai a tsakaninsu, to dole ne kuma a kayyade kowanne a bashi matsayinsa.  Wannan shi ake kira “Priviledges.”  Za a yi haka ne bayan an samar wa kowanne daga cikinsu suna (username) da kalmar sirri (password), wadanda dasu ne zai rika amfani wajen shiga zangon daga kowace kwamfuta ce a wurin.  Babbar manhajar kwamfuta ta Windows na dauke da manhajar tsara sunaye da kalmomin iznin shigar masu mu’amala da kwamfutar da ke kowane zango mai suna “Active Directory.”  Aikin wannan masarrafa ko manhaja shi ne tsara dukkan bayanan da suka shafi kowace kwamfuta, da kowane mai mu’amala da kwamfuta da ke zangon, ba tare da matsala ba.  A nan ne za a daidai matsayin kowannensu, a canza masa kalmar sirri idan yana so, sannan idan ma ana so a goge sunan wani ko wata kwamfuta dake zangon, duk ta nan za a yi.

Wannan a takaicen takaitawa kenan.  Sauran bayanai kuma ka nemi kasidar da na rubuta a wannan shafi cikin shekarar 2010 mai take: “Tsarin Sadarwa a Tsakanin Kwamfutoci” don karin bayani.  Ko kana iya turo adireshin Imel dinka sai in ingizo maka kasidar.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.