Sakonnin Masu Karatu (2009) (5)

Ga kadan cikin wasikun masu karatu nan kamar yadda muka saba kawowa lokaci-lokaci.  Wasu na riga na amsa su tun sadda aka aiko su, wasu kuma nayi alkawarin amsa su ne a wannan shafi; wasu sakonnin kuma ta hanyar wayar tarho aka yi su, na bayar da amsarsu nan take. Don haka wadanda aka bugo don yabo, sai dai muce Allah saka da alheri, don ba zan iya kawo dukkansu ba.  Wadannan sakonni dai na text ne ko wadanda aka rubuto ta hanyar Imel, muna kuma kara nuna godiyarmu ga dukkan masu bugowa ko aiko da sako ta dukkan hanyoyin, Allah saka da alheri, ya kuma bar zumunci, amin summa amin.  A halin yanzu ga sakonnin nan:

82

Malam Assalamu Alaikum, ina son cikakken bayani kan fai-fai guda biyu; na GARMAHO da na CD. A duniyar kimiyya da fasaha ya abin yake ne Malam?  Na kasance ina da karancin shekaru.  Allah ya taimaki Malam da almajiransa amin.  – Aliyu Muktar Sa’idu, Kano: 08034332200, 07025815073

Hakika shafin Kimiyya da Fasaha na matukar godiya gareka saboda irin himmarka wajen bibiyar darussan da ake zubowa a wannan aji, ta hanyar bugo waya ko text da dai sauransu.  Lallai fasahar faya-fayan Garmaho da na CD suna da alaka da juna, alaka ta asali kuwa, kuma na tabbata cikin masu karatu da karancin shekaru irinka basu san fai-fan garmaho ba, sai na CD. Na kuma tabbata akwai masu sha’awan son jin yadda wannan fasaha yake.  In Allah Ya yarda muna nan tafe da jerin kasidu kan haka nan ba da dadewa ba.  Mun gode.  – Baban Sadiq


Assalamu Alaikum Baban Sadiq, godiya muke yi da binciken da kake yi. Kuma gudunmuwar ilimi da kake bayarwa sun amfanar.  Da fatan za ka ci  gaba da binciko mana abubuwan al’ajabi kana sanar da mu.  Allah biya, ya jikan mahaifa, ya kara maka da mu ilimi mai amfani. Na gode.  – Baban Auwal, Abdullahi A., Keffi, Nassarawa State: 08035974923

Baban Auwal, mu ke da godiya kwarai kan haka.  Allah kara mana juriya da hakurin bin darussa.  Allah taimake mu baki daya kan haka, amin.  – Baban Sadiq


Assalamu Alaikum, don Allah ka daure ka buga  mana littafi game da kwamfuta da Hausa.  – Hon. Isa Tilde: 08023185801

Hon Isa mun gode da wannan shawara.  Akwai littafin koyon kwamfuta da aka kaddamar a Kano makonni biyu da suka gabata.  Na kuma tabbata zai fara yaduwa nan ba da dadewa ba. Sai a nema, kafin wanda na rubuta kan Fasahar Intanet ya bayyana in Allah Ya yarda.  Mun gode.  – Baban Sadiq


Assalamu Alaikum Baban Sadiq, fatan alheri.  A bayaninka na Etisalat a cikin Jaridar AMINIYA ta ranar Jumu’a 28/11/2008, akwai abubuwan dubawa kamar biyu: na farko kyautar 300secs a wata ne ba a kullum ba.  Na biyu, “Home Zone” yana nufin wuraren da za a yi ma saukin  caji in ka kira kana wurin ne, ba wai in ka kira wuraren ba.  Na gode.  – Shehu Dahiru Fagge, Kano: 08060651115

Malam Shehu na gode da wannan  fadakarwa da kayi min, kuma Allah saka da alherinsa, amin.  Kamar yadda na sanar da kai ne a jawabin sakon Imel da na aika maka, cewa aiyuka sun ruda ni, sai na mance, shi yasa baka ga na fitar da gyarar a shafin AMINIYA ba.  A yanzu ga shi nan, kuma Allah saka da alherinsa amin.  – Baban Sadiq


Assalam na ga sakonka kuma na ji dadin kasancewar ka mai amsar gyara, da fatan Allah ya yi maka jagora ya kuma tallafawa wannan kamfani namu MEDIA TRUST. Ya kuma kara  ma sa kwararrun ma’aikata irinka.  Nagode.  Naka a kodayaushe  –  Shehu Dahiru Fagge (Baba), shehudahir@yahoo.com.

Af, ashe ma ka samu sakon nawa kenan!  To Allah sa mu dace baki daya, amin.  – Baban Sadiq


- Adv -

Salaam, na rubuto ne domin in mika gaisuwa na, da fatan an yi sallah lafiya, allahumma amin.  Abbas Amin: 07032997200

Lallai mun yi sallah lafiya Malam Abbas, mun kuma gode, Allah saka da allherinsa, amin summa amin.  – Baban Sadiq


Baban Sadik, ka manta littafin “Mu Koyi gyaran Rediyo” na Musa Isa, da kuma “Ikon Allah (1-5).”  Muna yaba kokarinka a wannan shafi.  Allah Ya taimake mu.   – Nasir G. Ahmad: 08065496902

Wannan haka yake Malam Nasiru, kuma na shigar da bayanin kamar yadda na tabbata ka karanta a kasidar karshe kan wannan maudu’i. Mun gode da tunantarwa, Allah bar zumunci.  – Baban Sadiq 


Baban Sadiq akwai wani bawan Allah ana kiransa Alhaji Isa Musa Gumel, ya rubuta littafi (mai suna) “Mu Koyi Gyaran Rediyo” (1-2), ma’aikacin NEPA ne, kuma mazaunin Kano. – Shazali Lawan Gumel, Gumel, Jigawa: 08060103506

Malam Shazali kai ma mun gode da wannan tunatarwa.  Na kuma tabbata ka ga tunatarwarka mun shigar cikin kasida ta karshe kan wannan maudu’i.  Mun gode.  – Baban Sadiq


Assalamu Alaikum, Baban Sadiq shin zan iya samun littattafan Farfesa Muhammad Hambali Jinju a Kano?  Kuma a wani waje? – Ahmad Muhammad Amoeva: 08066038946, 07028456188

Kamar yadda na sanar da kai, idan kaje “Bata” za ka samu in Allah ya yarda.  Ko kuma kaje shagon sayar da littafai da ke Jami’ar Bayero, ko ka aika ABU Zaria.  Allah sa a dace, amin.  – Baban Sadiq


Baban Sadiq, kasancewar wannan shafi namu mai albarka na Kimiyya da Fasaha yana yin waiwaye, to ni ma ina son ai min fashin-baki a kan “Asusu” (Bank), da wasu nau’uka na cikinsa; kofar shiga, da kofar fita (bullet-proof security door), na’urar kirga kudi (counting machine),motar daukar kudi (bullion van).  – Aliyu Mutkar Sa’id Kano: 08034332200

Malam Aliyu, idan na fahimci tambayarka, kana son bayanai ne kan nau’ukan fasahar da aka yi amfani dasu wajen kera wannan abubuwa da  a yanzu ake amfani dasu wajen tafiyar da harkokin kudi.  Insha’Allahu a hankali duk za a samu bayanai daya-bayan-daya.  Komai a hankali ake binsa, saboda yanayin shafi da kuma lokaci.  Allah sa mu dace, amin. – Baban Sadiq

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.