Jawabin Steve Jobs (2005) – Kashi na Biyu

Wannan shi ne kashi na biyu na jawabin Steve Jobs. A sha karatu lafiya.

475

A makon da ya gabata ne muka gabatar da kashi na daya na jawabin Steve Jobs, tsohon Shugaban kamfanin Apple Inc, a yau ga kashi na biyun, wanda shi ne karishen jawabin.  Idan ba a mance ba a makon da ya gabata dai mun yanke jawabin ne inda yake gab da gama labari na biyu.  A yau mun kawo cikon, tare da labari na uku. Zuwa mako mai zuwa in Allah ya so za mu kawo wasikun masu karatu da amsoshinsu.  A ci gaba da kasancewa tare da mu.


“Rayuwarku ‘Yan Kwanaki Ne Takaitattu…”

“Bayan shekaru biyar da wannan kora ne na kafa kamfani mai suna NeXT, da wani kamfanin mai suna Pixar, kuma ana cikin haka na hadu da wata baiwar Allah mai ban al’ajabi da a karshe na aure ta.  Ta hanyar kamfanin Pixar ne aka fitar da wani fim da aka yi, ta amfani da Fasahar Zanen Kwamfuta (Computer Animation) mai take: Toy Story, wanda shi ne na farkon irinsa a duniya.  Kuma wannan kamfani na Pixar ne ya tsere sa’o’insa wajen shahara da cin nasara a wannan fanni a duniya.  Abin mamaki, ana cikin haka kuma sai kamfanin Apple ya sayi wannan kamfani na NeXT da na kafa.  Wannan shi ne abin da ya dawo da ni kamfanin a karo na biyu, kuma fasahar da muka samar a kamfanin NeXT ta zama ita ce kashin bayan ci gaban kamfanin Apple kamar yadda kuke gani a yau.  Daga nan kuma na auri Laurene, muka ci gaba da rayuwa mai armashi.

Na tabbata da ba a kore ni daga kamfanin Apple ba a farkon lamari, da babu ko daya daga cikin wadannan ci gaba da za su riske ni.  Dandanon magani bai da dadi ko kadan, amma na tabbata shi ne abin da mara lafiya ya fi bukata.  Wasu lokuta rayuwa kan dake ka da guduma. Idan haka ya faru, duk kada ka yanke kauna da rayuwa.  Na gamsu cewa lallai abin da ya taimaka mini wajen tafiyar da rayuwa shi ne, ina sha’awar abin da nake yi (na aiki).  Don haka, wajibi ne ku lazimci abin da kuka fi sha’awan yi a rayuwa.  Kuma wannan shi ne abin da ya kamata ta bangaren aikin yi, da alakarku da masoyanku. Domin aiki shi ne abin da zai ci kaso mafi yawa na rayuwarku, kuma hanyar da za ku bi kadai don samun gamsuwa a rayuwa ita ce ta yin abin da kuka fi sha’awa.  In har baku samu abin da kuka fi sha’awan yi ba a rayuwarku yanzu, to, ku ci gaba da nema.  Kuma, kamar alaka ce tsakanin masoya, duk sadda shekaru suka yi nisa, tana kara armashi ne. Don haka ku ci gaba da bincike har sai kun samu abin da kuka fi sha’awan yi.  Kada ku yarda da wani abin da ba wannan ba.

Labarina na uku a kan mutuwa ne.

Lokacin da nake dan shekaru 17, na taba karanta wani zance mai kamar haka: “In har a kullum kana riya cewa ba za ka kai karshen yinin da  ka samu kanka a ciki ba, to, da sannu watarana tunaninka zai zama gaskiya.” Wannan zance yayi tasiri matuka a ruhi na, kuma sama da shekaru 33 da suka shige, duk safiya idan na kalli fuskata a madubi nakan tambayi kaina: “A kaddara wannan shi ne yinina na karshe a duniya, shin, zan so in ci gaba da yin abin da na kuduri aniyar yi a yau?” Daga sadda na ci gaba da baiwa kaina amsar wannan tambaya da cewa, “A a,” iya tsawon kwanakin da na yi ta yi wa kaina tambayar, daga nan na fahimci lallai ya kamata in canja wani abu a rayuwata.

Tunanin cewa lallai nan ba da dadewa ba zan iya mutuwa, shi ne muhimmin abin da na taba cin karo da shi, wanda kuma ya taimaka mini wajen tantace duk wani abin da zan yi a rayuwata.  Duk wani abu mara kima a rayuwa – kamar burace-buracen zuci, da girman kai, da tsoron abin kunya, ko tsoron rashin cin nasara – da zarar an ambaci mutuwa, nan take duk sai su gushe. Ba abin da zai saura sai muhimman al’amuran rayuwa.  Yawan tuna cewa nan gaba za ka mutu, a iya tunanina, shi ne kadai abin da zai sa ka kauce daga fadawa tarkon yawan damuwa da wata hasara ta dukiya da kake tsoro. Ba ka da wata mafaka.  In kuwa haka ne, ba ka da wani dalilin da zai hana ka bin shawara kan abin da zai fisshe ka.

Kimanin shekara daya da ta wuce (2004) aka tabbatar mini cewa na kamu da cutar sankara mafi muni (Pancreatic Cancer). Da misalin karfe 7:30 na safiya aka dauki hoton ciki na, inda a karshe aka gano ina da wannan cuta ta sankara.  Ban ma taba sanin me ake nufi da wannan bangaren ciki da ake kira Pancreas ba. Nan take likitoci suka sanar da ni cewa, wata irin nau’in cutar sankara ce wacce ba ta da magani, kuma nan gaba ba zan wuce tsawon watanni shida ba a duniya. Daga nan dai likita ya shawarce ni da in koma gida “in gyatta al’amura na.”  Wanda hakan, a kaikaice, hannunka mai sanda ne da likitoci ke yi wa mara lafiya cewa, ka je ka shirya wa zuwan mutuwa kawai. Abin da wannan ke nufi shi ne ka je ka sanar da iyalinka duk abin da ka san ya kamata su sani daga nan zuwa shekaru 10, a tsawon ‘yan watannin da ke tafe.  Hakan na nufi ne har wa yau, cewa ka tabbatar da cewa komai ka gama kintsa shi, don sawwake wa iyalinka duk wata matsala da ka iya tasowa bayan mutuwa. A takaice dai, ka je ka musu wasiyya da bankwana!

- Adv -

Da tunanin wannan cuta dai na yini tsawon wannan rana. Can dai zuwa yamma, sai aka zo aka tsakuro samfurin wannan cuta daga ciki na. An yi hakan ne kuwa ta hanyar tsofa na’urar hango cuta a ciki (Endoscope) wacce ke dauke da wani dan karamin allura, ta bi ta makogwaro da ciki da hanji, har ta karasa inda mikin ciki yake (Pancreas), ta tsukuro kwayoyin halitta (Cells) daga cutar da ta tsiro a jiki.  A lokacin an mini allurar bacci, amma mai dakina tana wurin, kuma tace daidai lokacin da aka fito da wannan samfurin cuta, da aka sa shi karkashin na’urar hangen nesa, sai duk likitocin suka kama kwalla saboda murna.  Domin ya bayyana musu cewa wannan nau’in cutar sankara ce ta musamman da ake iya warkar da ita ta hanyar tiyata. Tuni har an mini tiyatan, kuma a halin yanzu na samu sauki.

Wannan shi ne lokacin da na samu kaina mafi kusanci da mutuwa, kuma ina fatan wannan lamari ya kusantar da ni zuwa wasu shekaru masu yawa nan gaba.  Bayan na wuce wannan marhala ta rayuwa, a yanzu ne zan iya sanar da ku wani zancen da a baya ba zan iya gaya muku shi ba, saboda rashin fahimtar mutuwa hakikatan. (Ga sako na gare ku):

Babu mai son ya mutu.  Hatta wadanda ke ganin sun yi aikin kwarai ba su cika son su mutu ba, sai dole.  Amma kuma babu makawa, mutuwa ce masaukin da za ta tattaro mu duka.  Babu wanda ya taba guje wa mutuwa a baya.  Kuma haka lamarin ya kamata ya zama. Domin mutuwa ce abin da har zuwa yau duniya bata taba samar da irinta ba.  Ita ce abin da ke kawo canji a rayuwa.  Ita ce ke share tsohuwar al’umma don kawo sabuwa.  A halin yanzu da nake muku wannan jawabi, ku ne sabuwar al’umma, amma nan ba da dadewa ba, watarana za ku zama tsohuwar al’umma, a share ku don kawo wata sabuwar.  Ku mini afuwa idan wannan zance nawa ya firgita ku, amma wannan ita ce hakikanin gaskiya.

Rayuwarku ‘yan kwanaki ne takaitattu, don haka kada ku shagala wajen kwaikwayon rayuwar wani.  Kada ku zama ‘yan abi yarima a sha kidi.  Kada ku yarda surutan wasu su hana ku bin shawarar da za ta fisshe ku a rayuwa.  Abu mafi muhimmanci shi ne, ku zama masu juriya wajen bin abin da zai zama maslaha a rayuwarku da fahimtarku.  Domin su ne kadai suka fi kowa sanin abin da kuke son ku zama.  Duk wani abin da ba wannan ba, to, ya zo a bayanshi.

Lokacin da nake dan karami akwai wata mujalla mai kayatarwa da ake kira: Whole Earth Catalog, wadda mujalla ce da kusan kowa yayi amanna da ita.  Wanda ya fara buga wannan mujalla kuwa wani bawan Allah me mai suna Stewart Brand, wanda ke unguwar Menlo Park da ke nan kusa da ku.  Ya kuma kayatar da mujallar ne ta hanyar kwarewarsa ta adabin turanci da yake da ita.  Wannan lamari ya faru ne tun wajajen shekarun 1960, kafin bayyanar kwamfutoci da tsarin buga mujallu na zamani kenan. Don haka mujallar gaba dayanta ana buga ta ne ta hanyar amfani da keken rubutu (Typewriter) na wancan zamani, da almakashi (wajen rage tsawon shafukan), da kuma na’urar daukan hoto irin ta da (Polaroid Camera).  Wannan mujalla dai kamar wata shafin gidan yanar sadarwar Google ce da aka buga a shafukan takarda, saboda fa’idojin da take dauke dasu.  Duk da cewa shekaru 35 kenan kafin bayyanar Google, amma mujallar a cike take da nau’ukan ilmi da fadakarwa, kwatankwacin yadda gidan yanar sadarwar Google take a yau.

Stewart, tare da abokan aikinsa dai sun buga wannan mujalla na tsawon lokaci, bayan wasu ‘yan lokuta kuma sai aka neme ta aka rasa.  Amma kafin nan, sun yi bugu na karshe daidai shekarar 1974 – sannan ina matashi kamarku.  A shafin karshe daga baya, akwai wani hoto mai kayatarwa na wani titi da aka dauki hotonsa da safe – irin yanayin da wasunku za su so su taka a cikinsa don watayawa. A karkashin wannan hoto akwai wani karin zance da ke cewa: “Ka zama mai yunwar ilmi. Ka zama mai budaddiyar zuciya.” Wannan shi ne sakon bankwana da suka sa a shafin karshe na mujallar, kafin su daina buga ta gaba daya.  Ka zama mai yunwar ilmi. Ka zama mai budaddiyar zuciya.  Kuma a kullum nakan yi wa kaina wannan fata.  Don haka na ga dacewar yi muku wannan fata ku ma, a daidai wannan lokaci da kuke kokarin fara wata sabuwar rayuwa, bayan barin Jami’a, cewa:

Ku zama masu yunwar ilmi a kullum. Ku zama masu budaddiyar zuciya wajen karbar fahimta.

Na gode matuka.”

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.