Hira da Edward Snowden (4)

Ga kashi na hudu na hirar Peter Taylor da Edward Snowden. A sha karatu lafiya.

198

Peter Taylor:  A halin yanzu ‘yan majaisar kasar Burtaniya na gab da fara muhawara ne kan wani kuduri da idan ya zama doka, zai baiwa hukumar (GCHQ) damar tatsar bayanan jama’a kai tsaye.  Meye shawararka ga ‘yan majalisar idan sun tashi muhawara kan wannan kuduri?

Snowden:  Shawarata gare su ita ce, dole ne su samar da wani tsari da zai rika baiwa jami’an gwamnati da su kansu ‘yan majalisa da sauran jama’ar kasa, damar tantance ayyukan wannan hukuma da dacewarsa, a kowane lokaci ne.  Wannan zai sa a gano duk wanda ya saba wa doka, a masa hukuncin da ya dace dashi.  Wato babban abin tambaya ma shi ne, waye ya kamata ya rika aiwatar da bincike da zarar an shiga hakkin mutum ta hanyar shiga hakkin sirrinsa?  Shin, minista ne, ko kuma alkali?  Idan na dubi abin, sai inga hanyar warware wannan matsalar kadai ita ce kotu.

Peter Taylor:  A halin yanzu dai an samu ‘yar takaddama tsakanin kamfanonin sadarwa na sada zumunta – Google, da Yahoo”, da Facebook, da Twitter – a bangare daya, da kuma hukumar kasar Amurka a daya bangaren.  Hukumar NSA tace musu: “Muna bukatar ku rika bamu damar tatsar bayanan jama’a da kuke dasu a kwamfutocinku.  Domin wannan ne zai bamu damar gano miyagu da ‘yan ta’adda.”  Su kuma a nasu bangaren, wadannan kamfanoni suka ce, “Dan dakata kadan!  Mu fa hakkin dake kanmu na farko shi ne kare wa jama’ar dake mu’amala damu hakkokinsu na sirri.”  Meye ra’ayinka kan wannan takaddama?

Snowden:  Wannan abu ne da ya shafi tsarin tattalin arziki da ya baiwa kowa damar mallakar hanyoyin cinikayya da kasuwanci.  Tambayar ita ce:  su wadannan kamfanoni na sadarwa, shin, suna yi wa jama’ar dake da rajista dasu ne aiki (a matsayinsu na kamfanoni masu zaman kansu), ko kuma hukuma suke wa aiki?  Sannan ka tuna fa, da zarar wani kamfanin sadarwa ya fara karban bukatun damar tatsar bayanan sirri ga wata hukuma ta gwamnati, to, dole ne kamfanin ya karbi bukatar kowace hukuma a duniya, in kuwa ba haka ba, ya rasa abokan huldar kasuwanci.

Peter Taylor:  Yanzu kana nufin ko da gwamnatin kasar Sin ce, ko ta Rasha suka bukaci hakan?

Snowden:  Tabbas, sosai kuwa!  Domin muddin muka yarda cewa mun baiwa gwamnatin kasar Burtaniya wata kafa don tatsar bayanan sirrin jama’a don samun daman gano ‘yan ta’adda, to, gwamnatin kasar Sin ma na iya gaya wa wadannan kamfanoni cewa: “Muddin kuna son shigo da hajojinku cikin kasar Sin, to, dole ne mu ma ku bamu irin wannan kafa don tatsar bayanan jama’arku.”

Peter Taylor:  Za ka iya tuna wannan hoton?  (Ya nuna masa wani hoto mai dauke dashi da wani tsohon Daraktan hukumar CIA).

Snowden: (Ya tintsire da dariya)

Peter Taylor:  Dole in tuna maka lokacin farin cikinka na baya.

Snowden:  Wannan shi ne Michael Hayden, tsohon Daraktan hukumar CIA.

Peter Taylor:  Janaral Michael Hayden ba ya cikin magoya bayanka.  Ga kuma abin da yake cewa: “Wannan shi ne tonon silili mafi girma da aka taba yi wa kasar Amurka a tarihinta gaba daya, a fannin leken asiri.  Kuma wannan ya mayar da agogon hukumar NSA da kudurarta wajen aiwatar da ayyukanta, zuwa shekaru masu yawa a baya.”  Shin, ba ka ganin wannan zance nashi na nuna cewa kai maciyin amana ne?

Snowden:  Michael Hayden shi ne mutum na farko da ya fara bayar da umarnin a rika tatsar bayanan jama’a ta hanyar wayar salularsu a kasar Amurka.  Kuma wannan ya ci gaba har tsawon shekaru 10, kafin nazo na hankado wannan badakalar.  Wanda kuma wannan shi ne abin da ya tsayar da wannan tsari, ya kuma zama dalilin samar da wata doka da ta baiwa kowa kariya a kasar Amurka.  Tambaya a nan ita ce:  a madadin wa Michael Hayden yake wancan zance?  (Da yace ni maciyin amana ne) ban sayar da wadannan bayanai ba, ban kuma amfana dasu ta kowace hanya ba.  Da yawa cikin mutane ma kan ce zaman gudun hijira ba karamar ci baya bane.

- Adv -

Peter Taylor:  To amma ai Michael Hayden na iya cewa, shi aikinsa (a matsayinsa na Daraktan CIA) shi ne ya baiwa al’ummar Amurka kariya da tsawo daga kowace irin cutarwa.  Abin da yake nunawa shi ne, abin da kai kayi ya saba wa wancan manufa.  Domin sanadiyyar hankado wadannan bayanai, ka zubar wa dukkan Amurkawa da kimarsu a idon duniya.  Shin, wannan ba ya nuna cewa kai maciyin amana ne?

Snowden:  Ko kadan, ni ba maciyin amana bane.  Tambayar ita ce:  idan ni maciyin amana ne, to, amanar wa naci?  Domin bayanan da na debo na baiwa ‘yan jaridar kasar Amurka ne, da sauran kungiyoyin kare ‘yancin dan adam.  In kuwa haka ne, to, waye hukuma take wa aiki?  Al’ummar Amurka suke wa aiki, ko kuma sabanin haka?

Peter Taylor:  Mu dawo kan batun rayuwarka nan gaba.  Babban tsohon Lauyan gwamnatin Amurka Eric Holder, yace akwai tsammanin sasantawa tsakaninka da gwamnatin Amurka.  Shin, wannan wani abu ne mai yiwuwa?

Snowden:  Mun ga sauyi matuka daga bangaren gwamnati, tun shekarar 2013 lokacin da lamarin ya faru, inda a baya take ta zargina da cin amanar kasa da sauransu.  Yanzu mun daina jin irin wadannan zantuka.  Wannan yasa nake fatan gwamnatin Amurka za ta canza matsayinta kan abin da ya shafi tuhumar masu bankado badakala a kasar gaba daya.

Peter Taylor:  Yanzu kana nufin nan gaba idan bukata ta kama za ka iya zama da gwamnati don sasasanci kenan?

Snowden:  Sosai kuwa, me zai hana?  Na yi alkawarin ma ko fursuna zan iya yi.  Amma abin da bazan yarda dashi ba shi ne in zama wani zakaran gwajin dafi da gwamnati za tayi amfani dashi wajen tsorata wadanda nan gaba za su ga badakala irin wannan amma su kasa bayyanawa.

Peter Taylor:  Yanzu ko zaman kurkuru kana iya yi kenan?

Snowden:  Sosai kuwa!

Peter Taylor:  Yanzu bazai zama tufka da warwara ba, ace kai da kake tutiyar rajin kare hakkin dan adam da tabbatar da gaskiya, wai kaine a nan kasar Rasha, kasar da kowa ya san sunyi bakin suna wajen keta hakkin dan adam?

Snowden:  Na rubuta bukatar mafakar siyasa a kasahe sama da 20, tun daga nahiyar turai zuwa sauran nahiyoyi, amma kowannensu na shayin bani amsa, saboda tsoron kada su ce sun ki, ya zama kamar sun goyi bayan gwamnatin Amurka.  Wanda wannan zai nuna wa mutanensu cewa su ma suna iya toshe fadin alkabarcin baki kenan.  Ko kuma suce sun amince, su samu matsala da gwamnatin Amurka.  Amma duk da haka, na bayyana a fili karara cewa a shirye nake in koma Amurka.  Zan iya komawa kasar Amurka ko da gobe ne, muddin hukuma a shirye take ta kare mana ‘yancinmu.

Peter Taylor:  Yaya kake kallon mahangar gwamnatin Amurka a yanzu?  Ma’ana, me kake tsammanin zasu yi maka idan kace za ka koma gida?

Snowden:  To da farko dai sun ce idan nace zan koma gida baza su azabtar dani ba.  Wannan dai na ji su ne kawai (ya fashe da dariya).  Amma duk da haka dai har yanzu babu wani cikakken tattaunawa tsakaninmu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.