Ciyar da Najeriya Gaba a Fannin Kimiyya da Kere-Kere (3)

A kashi na uku cikin jerin wadannan kasidu, mun yi bayani ne kan wasu ka’idoji shida da ake gejin ci gaban kowace kasa a duniya, don fahimtar a wani mataki kasarmu take. A sha karatu lafiya.

199

Wasu Ka’idoji Shida

Wannan ya kawo mu ga wasu ka’idoji ko ma’aunai guda shida da za mu yi amfani da su wajen gano iya gwargwadon ci gabanmu a kimiyya da kere-kere a halin yanzu.   Malaman Kimiyya da Kere-kere suka ce akwai wasu sifofi guda shida da duk kasar da ta cika su, to ba za a iya cewa ta ci gaba ba a  fannin Kimiyya da Kere-kere, watau Science & Technology.  Siffa ta farko, idan ta kasa kera manyan injinan sarrafa abubuwa; daga nona zuwa kere-kere, misali irin su katafilolin noma da na sharan hanya, da na hako abubuwa daga karkashin kasa, da jiragen kasa, da motoci, da wasu injinan zakulo abubuwa daga kasa ko dora su a sama, to ba a kirga ta cikin sahun kasashen da suka ci gaba.  Idan muka dubi Najeriya za mu ga cewa haka muke.  Ko keken dinki ba na tunanin muna kera shi a kasar nan, balle na hawa, balle babur, balle mota, har a kai ga katafilar nona (tractor).  Sifa ta biyu, idan kasa ta kasa hako (ba sarrafawa ake nufi ba) albarkatun da Allah ya mata daga karkashin kasa, sai ta dogara ga wasu kasashe masu taimaka mata da kayayyakin aiki da kuma ma’aikatan da za su yi mata wannan aiki, to ita ma ba za a sanya ta cikin sahun kasashen da suka ci gaba ba.  Idan muka dubi wannan sifa, sai mu ga cewa daram ta zauna a kanmu.  Ga kamfanonin kasashen waje can a Kudu, suna ta cin karensu babu babbaka.  Ba ma harkar mai kadai ba, hatta injinan hako albarkatun kasa irinsu su zinare da azurfa, duk ba mu da mu. Galibin masu aikin kuza a Najeriya da hannunsu suke yi.  Kai, hatta injinan haka rijiya daga wasu kasashe muke sayowa.

- Adv -

Sifa ta uku, idan aka wayi gari galibin manoma a kasa suna amfani ne da hannunsu (fartanya da garma) wajen nome kasar da suke shuka a kai, to ba za a ce ta ci gaba ba.  Idan muka dubi wannan ita ma, sai  mu ga daram ta zauna a kanmu.  Watakila mai karatu ya ce ai akwai masu amfani da katafilun noma, watau tractor.  Amma mutum nawa ne?  Galibin manoman Najeriya da karfin tuwonsu suke noma abin da ake ci.  Wannan har a babban birnin tarayya ma haka abin yake; duk daya ne, wai makaho ya yi dare a kasuwa.

Ma’auni na hudu, idan kasa tana dogaro ne da wasu kasashe wajen sayen bangarorin mashina ko injinan sarrafa kayayyaki ko albarkatu da take amfani da su, to nan ma ba za a ce ta ci gaba ba.  Ai mun gama da wannan, tunda har ta kaimu ga sayen wadannan kayayyaki daga wasu kasashe, ai dole ne mu koma gare su idan sun lalace. A takaice dai, Najeriya ba ta iya kera bangarorin manyan injinan da take amfani da  su wajen sarrafa arzikinta.  Sifa ta biyar, idan ya zama galibin kayayyakin da kasa ke sayarwa a kasuwannin saye da sayarwa na duniya nau’in arzikin da ta ciro ne daga kasa kai tsaye, ko ta noma kadai, bai wai sarrafaffu ko kerarrun abubuwa ba, to nan ma za a ce bata ci gaba ba.  Wannan a fili yake.  Tabbas muna fitar da karafa, da alminiyon, amma danyensu; domin kamfanonin da ke sarrafa su sun kwanta dama.  Don haka galibin kayayyakinmu basu wuce danyen mai ba, watau Crude Oil, sai albarkatun noma, da wasu abubuwa.

Sifa ta karshe, suka ce idan kasa ta kasa kera makaman da za ta kare al’ummarta da su, sai dai ta siyo daga wasu kasashe, to, nan ma ba za a ce ta ci gaba ba.  Wannan ke nuna mana cewa, hatta kayayyakin kare kasa, sai mun siyo.  Kuma haka ne.  Amma ba wannan bane aibun, aibun na farawa ne daga lokacin da muka kasa yin wani kokari wajen ganin mun samu ‘yancin kanmu dangane da abin da ya shafi kera abubuwa irin wannan.  A karshe, a tabbace yake cewa lallai har yanzu da sauranmu.  Domin cikin wadannan ka’idoji ko sifofi guda shida da muka zayyana, babu guda daya da kasarmu ta ketare shi; duk sun zauna daram a kanmu.  To daga ina matsalar ta faro ne?

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.