Kamfanin Microsoft Ya Fara Gwajin Sabon Zubin Babbar Manhajar Windows, Mai Suna “Windows 11”

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 2 ga watan Yuli, 2021.

444

Cikin makon da ya gabata ne kamfanin Microsoft ya fitar da sanarwar cewa zai fara fitar da sabon zubin babbar manhajarsa mai suna: “Windows 11” ga kwararrun masana manhajar kwamfuta da ke bibiyar ayyukansa, wato: “Windows Insiders”, don basu damar gwajin wannan sabon zubi kafin ya fitar kasuwa, kamar yadda aka saba.  Haka kuwa aka yi.  A ranar Litinin, 28 ga watan Yuni kamfanin ya fara tunkudowa musu don yin gwaji.  Wannan zubi na babbar manhajar Windows dai zai maye gurbin babbar manhajar da ake amfani da ita ne a halin yanzu mai suna Windows 10, wacce kamfanin ya fitar a ranar 12 ga watan Yuli na shekarar 2015.  Shekaru 6 kenan yanzu.

Manyan Sauye-Sauye

Daga cikin manyan sauye-sauyen da kamfanin yayi ga wannan babbar manhaja dai akwai kare-kare da kuma sauyin siffar fuskar manhajar gaba daya.  Ya matsar da cibiyar manhaja (Start Menu) daga hagu zuwa tsakiyan shafin farko.  Sannan ya kayatar da fuskar bangarorin babbar manhajar gaba dayansu zuwa launi mai daukan hankali, irin launi da siffar babbar manhajar Mac na kamfanin Apple.  Daga cikin kare-kare akwai samun damar saukar da cibiyar manhajojin Android a kan kwamfuta baki daya, sabanin yanzu da sai ka jona wayarka da kwamfuta kafin samun damar isa ga manhajojinka.  Har wa yau, kamfanin Microsoft ya shigar da damar samar da mahallin aiki da kwamfutarka sama da daya, wato: “Multiple Desktop” Kenan.  Ta yadda za ka zarya tsakanin kowannensu.  Kana iya adana manhajoji da bayanai da kuma tsare-tsare nau’uka daban-daban a kowanne, ta yadda duk sadda ka tashi yin wani aiki na musamman ka mahallin da zai fi maka sauki.  Har wa yau an samar da manhajar aiwatar da tarurrruka na kamfanin Microsoft mai suna: “Microsoft Teams” a kan babbar manhajar.  Sabanin yanzu da sai dai ka saukar da kanka.  A zubin babbar manhajar Windows 11, kana iya aikawa da karban sakonnin rubutu da hotuna da bidiyo ko sauti kai tsaye daga mahallin da kake aiki, ba tare da motsa manhajar a inda take ba. Wasu daga cikin sauye-sauyen dai sai an saki babbar manhajar mai karatu zai gansu.  A yayin da wasunsu kuma ana kan aiki ne a kansu, musaman damar saukar da manhajojin Android da kuma mu’amala da manhajar aiwatar da tarurruka mai suna: “Microsoft Teams”.

Mallakar “Windows 11” Kyauta

- Adv -

A cewar kamfanin Microsoft, da zarar ya tunkudo “Windows 11” kafuwa, masu amfani da nau’in babban manhajar Windows 10, ko 8 ko 7, duk suna iya amfani da cibiyar “Windows Update” dake kwamfutarsu don saukarwa kyauta, ba tare da sun saya ba. Duk da cewa wannan ba dole bane, sai ga wanda yaga damar sabunta babbar manhajarsa da wannan zubi.  Wannan al’adar kamfanin Microsoft ne, kamar yadda yayi lokacin da ya kaddamar da babbar manhajar “Windows 10” a shekarar 2015.  Ga wadanda kuma suke da rajista da tsarin gwajin manhajar Windows mai suna: “Windows Insider Program”, tuni an basu damar saukar da wannan sabon zubin don yin gwaji da bai wa kamfanin shawarwari a inda suke ganin ya kamata a dada kayatar da manhajar.  Sauran jama’a kuma na iya mallakar wannan sabon zubi daga sadda aka tunkudo shi dauke akan sababbin kwamfutoci daga watan Satumba na wannan shekara ta 2021.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ba kowace irin kwamfuta bace za ta iya daukan wannan sabon zubi na Windows, saboda wasu dalilai na tsaro da kokarin tabbatar da kariya ga bayanai, kamar yadda kamfanin ya tabbatar.  Mahimman sharuddan dai su ne: sai kwamfuta mai dauke da mararrafa (Processor) nau’in 64-bit, wacce ke dauke da ma’adanar wuci-gadi (RAM) mai mizanin 4GB, da ma’adana mai mizanin 64GB, mai fadin fuska a kalla inci 9 (9-inch display), sannan ya zama tana dauke da tsarin “Secure boot” da “UIFE” da kuma “TPM 2.0”,  a takaice.

Shigowa Kasuwa

Kamfanin Microsoft yace zai tunkudo wannan zubin babbar manhaja ne daga watan Satumba mai zuwa.  Kuma yana shawartan kamfanonin kera kwamfutoci da cewa idan suna bukatar dora wannan sabon zubin manhaja a sababbin kwamfutocinsu, dole su cika wadancan sharudda da aka ambata a sama.  Wannan dai shi ne karo na 16 da kamfanin Microsoft ke fitar da sabuwar babbar manhaja, farawa da babbar manhajar Windows 1.0 da ya fitar a shekarar 1985. Galibi yakan sabunta manhajar ne a duk bayan shekarun da basu wuce 5 ko 6 ba, in ka kebe babbar manhajar Windows XP, wacce sai bayan shekaru 16 sannan ya sabunta ta.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.