Tsarin Gadon Dabi’u Da Siffofin Halitta (Genetics) (8)

Cikin wannan mako zamu dubi wata babbar mahawara ce da malaman dabi’a da mahalli suka dade suna arangama da juna kanta. Wannan mahawara tana karkashin tsarin da ya shafi tasirin mahalli ne ga dabi’ar dan adam. A sha karatu lafiya.

735

Matashiya

Ga wadanda suka saba bibiyar wannan shafi a kodayaushe, kasidu kan Tsarin Gadon Dabi’u da Siffofin Halitta, wato fannin da a harshen Turancin ilimin kimiyya ake kira Genetics, sun faro ne tun cikin shekarar da ta gabata.  Idan ba a mance ba har wa yau, mun gabatar da kasidu har zuwa kashi na 7, wadda tayi magana kan tsarin jirkita siffofin da dabi’un halittar shuke-shuke da kayayyakin abinci da ake shukawa.  Mun kawo ma’ana da asalin wannan fanni da har yanzu a duniya ake ta  muhawara wajen fa’ida ko rashin fa’idarsa musamman a bangaren lafiyar jiki da muhalli. Wannan muhawara ce da za ta dauki tsawon lokaci ana fafatawa tsakanin masana masu goyon bayan tsarin, da kwararru da ke ganin wannan babu abin da zai jawo wa duniya illa matsala.

A yau cikin yardar Allah za mu ci gaba da tattaunawa kan wannan fanni na tsarin gadon dabi’u da siffofin halitta, wato Genetics.  Wannan zai zama kashi na 8 kenan, ko kasida ta 8 daga cikin jerin kasidun da muka fara kawowa a wannan shafi cikin wannan fanni. Zan kuma yi kokarin ganin na lazinci jeranta su ba tare da yankewa na tsawon lokaci ba, don kauce wa mantuwa kan abin da kasidar baya tayi magana a kai.  Duk da cewa wannan shafi ne da ke tattaunawa kan jimillar fannin kimiyya da kere-kere, wanda hakan ke bukatar a rika cakuda kasidun kan fannoni daban-daban.

Fannin da za mu duba shi ne bangaren abin da ya shafi Nau’in Dabi’ar Halitta na Zahiri, wato Phenotype.  Idan mai karatu bai mance ba dai, a kasidar farko mun nuna cewa: Nau’in Dabi’ar Halitta, ko Genotype a kimiyyance, shi ne nau’in dabi’u da siffofin halittar da ya kebance kowane dan adam da zuriyarsa.  Shi yasa ma idan ana son jingina wani jariri ko ‘ya’ya ko kokarin gano rashin alakarsu ga wanda ake alakanta su dashi, sai a musu gwajin Nau’in Dabi’ar Halitta, wato Genotype Test. Hakan na faruwa ne saboda ba abu bane da za a iya gani a zahiri, kamar siffar jiki; wajen tsawo ko gajarta ko laushi ko gautsi.  Wannan Nau’in Dabi’ar Halitta (Genotype) da ke kebance mutane daga wadanda ba su ba, ita ce ke bayyana hakikanin yanayin siffa da daibi’ar mutum a zahiri.  Wadannan dabi’u da siffar halitta ta zahiri, wadanda ke samo asali daga wancan Nau’in Dabi’ar Halitta ta boye, ita ake kira Phenotype.  Wannan shi ne abin da kasidarmu ta wannan mako za ta duba, don tattaunawa kan yadda yake samuwa, da abin da ke haddasa shi, da kuma tsarin sauyawarsa.


Kalmar Phenotype

A fannin ilimin kimiyyar sinadaran halitta, kalmar Phenotype ta samo asali ne daga wasu kalmomi guda biyu na harshen Girka (Greek). Kalmar farko ita ce kalmar Phainein, mai nufin “Nuna wani abu…” da kuma kalmar Typos da ke nufin “A kamanta.”  Wadannan kalmomi biyu ne aka gwama su don samar da kalmar Phenotype, wadda a harshen sinadaran kimiyyar halitta ke nufin: “Nau’in dabi’ar halitta ta zahiri.”  Wannan kuwa ya hada da dukkan abubuwan da ke bayyana siffar halitta da ake iya gani a fili, da wadda za a iya gani idan aka bude wani bangare na jiin dan adam.  Ire-iren wadannan siffofi sun hada da: yanayin girman jiki, da tsawon hannu, da launin fatar jiki, da gajarta ko tsawon gabobin jiki, da launin idanu, da nau’in jini (Blood Group), da dabi’un mu’amala, da dabi’un zamantakewa, da yanayin fahimta, da yanayin hazaka, da kaifi ko dakushewar basira, da taushi ko laushin fatar jiki da dai sauransu abin da za a iya gani a kusa ko a nesa.

Asali da Tarihi

Duk da cewa fannin ilmin halitta na daga cikin dadaddun nau’ukan ilmin kimiyya, bunkasar fannin Nau’in Dabi’ar Halitta ta Zahiri bai samu ba sai bayan bincike na musamman da wani masanin fannin mai suna Wilhem Johannsen, a shekarar 1911 ya gudanar.  Wannan shi ne kwararre na farko da ya fara gudanar da bincike na musamman kan wannan fanni da yadda yake samuwa.  Ya gudanar da bincikensa ne kan tsarin gadon dabi’u da siffofin halitta tsakanin iyaye da zuriyarsu, da kuma yadda gadon ke kasancewa a aikace; wato boye da zahiri kenan.  Wajen tabbatar da yadda ‘ya’ya ke gadon dabi’un halitta (wajen siffar tsawo da gajarta da dabi’un zuci da dabi’un halayya) ne ya gano cewa lallai akwai tasirin mahalli wajen samuwar wadannan abubuwa.  Bayan shi masana da dama sun ci gaba da bincike don fadadawa tare da inganta wannan fanni ta hanyar binciken kwakwaf don kokarin tabbatar da wannan ka’ida ta ilimi.

Daga cikin shahararrun kwararru da aka sansu a wannan fanni akwai Richard Dawkins, wanda kwararren masanin ilmin kimiyya ne kuma marubuci.  Dawkins dan kasar Ingila ne.  Ya rubuta littattafai da dama kan fannin ilmin gadon dabi’u da siffofin halitta, wato Genetics.  Littafin da kowa yafi sanin Dawkins dashi shi ne wanda ya rubuta kan wannan fanni, mai suna: The Extended Genotype.  A cikin wannan littafi Dawkins ya nuna cewa, a yayin da ake bayanin tasirin mahalli wajen haddasa sauye-sauye ga halittar dan adam, ana takaituwa ne ga dabi’a ta zahiri, kuma ga wani mutum shi kadai.  Wannan, a cewar Dawkins, nakasu ne ga wannan fanni, kuma shi yasa ya rubuta wancan littafi don tabbatar da wannan kuskure.  Dawkins ya kawo misalai masu gamsarwa da ke nuna yadda Nau’in Dabi’ar Halitta ta Zahiri (Phenotype) ke samuwa ga wata halitta ta hanyar bayyana wata dabi’a da wata halitta daban tayi, a inda ko mahallin da wannan halitta take.  Wannan littafi dai ya samu karbuwa matuka, kuma kundi ne na musamman ga duk wanda ke son karin bayani a wannan fanni na ilimi.

- Adv -

Madogara

Malaman fannin Nau’in Dabi’ar Halitta ta Zahiri sun nuna cewa wannan fanni na dogaro ga abubuwa guda uku ne. Abu na farko shi ne habbaka, ko bunkasar halitta ta zahiri.  Wannan shi suke kira da suna Development. Abu na biyu kuma shi ne madaukan jiki (musamman na cikin jiki), wadanda suka hadu suka samar da dan adam.  Wadannan sun hada da sinadaran jiki da sauran makamantarsu.  Wannan bangare shi suke kira Morphology.  Kalmar Morphology tana da ma’anoni a fannonin ilimi guda biyu; da fannin ilimin harshe da magana, wato Linguistics.  Sai fannin ilimin halitta, wato Biology. Bayananmu sun ta’allaka ne ga bangaren ilmin halitta. Sai a kiyaye, kadan mai karatu da ya kware a fannin ilimin harsuna ya ga wannan kalma da wannan ma’ana ya dauka akwai shirme cikin abin da ake magana a kai.  Sai bangare na uku, wato bangaren da ke lura da yanayin dabi’ar zamantakewa da dabi’ar halayya.  Wannan shi kuma ana la’akari da shi ne wajen yanayin mu’amala tsakanin mutane.  Ma’ana ba abu bane da a zahirin jikin mutum za ka gani, idan ba saninsa kayi ba.  Amma kuma yana bayyana idan bukatar hakan ta taso.  Misali, idan mutum mai saurin fushi ne, ba kowa ke iya ganewa ba don ya ganshi a karon farko, ko ya hange shi daga nesa.  Abin nufi, don kawai ka ga mutum, ba za ka iya cewa ga dabi’arsa ba kai tsaye, muddin ba saninsa kayi ba.  Wannan bangare shi suke kira Behaviour.  Wadannan su ne bangarorin da wannan fanni na Nau’in Dabi’ar Halitta ta Zahiri ke dogaro dasu wajen tabbatar da hakikaninsa.

Tsarin Tabbatuwa

Don samun cikakkiyar fahimta kan ma’anar wannan fanni, zai dace mai karatu ya fahimci cewa, bangaren Nau’in dabi’ar halitta ta zahiri, kamar yadda muke gani, ba komai bane face “Fassarar” bayanan da ke cikin dabi’ar halittar kowane dan adam, wato Genes.  Idan mai karatu bai mance ba, munyi bayani a baya cewa asalin bayanan da ke samar da hakikanin halittar mutum kamar yadda ake haifarsa, suna kunshe ne gaba dayansu a cikin kwayar halitta, wato Cell.  Wannan kwayar halitta na dauke ne da bangarori da dama.  Daga cikin bangarorin akwai Ma’adanar Bayanan Dabi’ar Halitta, wato Chromosome kenan.

Kowace kwayar halitta (Cell) na dauke ne da tagwayen “Ma’adanar Bayanan Dabi’ar Halitta” (wato Chromosome) guda 23.  Wannan ke nuna cewa a cikin jikin kowane dan adam za a samu guda 46 kenan (23 x 2 = 46).  Dukkan wadannan ma’adanar bayanan dabi’ar halitta iri daya ne na jikin mutum daya, duk da yake kowane dan adam nashi sun sha bamban da na waninsa.  Kowane dayan tagwayen “Ma’adanar Bayanan Dabi’a” kuma yana dauke ne da zaren “Madarar Bayanan Dabi’ar Halitta” da ake kira “Deoxyribonucleic Acid” ko “DNA” a takaice.  Wannan zare a siffar sarka yake, mai harde da juna. Kuma a jikin layin wannan sakakken zare ne ake da “Kwayoyin Dabi’ar Halittar” kowane dan adam.  Wadannan kwayoyin dabi’un halitta su ake kira “Genes”.  Kowane dan adam yana kebantuwa ne da kwayoyin dabi’un halitta daban da suka sha bamban da na wani, wadanda ya gado su daga wajen iyayensa ko kakanninsa ko kakannin kakanninsa, har dai abin ya kai ga Annabi Adamu da Hauwa’u, amincin Allah ya tabbata a gare su.

Sannan muka ce wannan Kwayar Dabi’ar Halitta da ake kira Gene, ita ce ke dauke da dukkan tsarin da Allah ya zuba na halittar dan adam; daga zaman mahaifa zuwa rayuwar duniya.  Idan aka haifi jariri, yakan zo da kirar jikinsa na musamman.  Idan ya fara girma yanayin jikinsa na canzawa daga tsarin halittar jarirantaka zuwa tsarin yarinta, da samartaka, har zuwa tsufa.  A yayin da mutum ke rayuwa ne zai rika girma – ta hanyar tsawo ko gajarta da fadin jiki da dai sauransu – zai kuma rika canzawa ta hanyar dabi’ar mu’amala, zai kuma rika fito da wasu halayya na musamman sanadiyyar zamantakewa.  Sannan idan aka gwada jini ko ruwa ko wasu daga cikin sinadaran da ke cikin jikinsa, za a ga abubuwa masu yawa sun bayyana.  Wadancan bayanai da ke kunshe cikin Kwayar Dabi’ar Halitta (Gene) masu dauke da bayanan da zahirinsu ya fito fili bayan haifar wannan jariri, su ake kira Genotype.  Wato Nau’in Dabi’ar Halitta da ta kebance wani mutum na musamman.  Idan kana son sanin irin naka, ka je asibiti za a maka gwaji kan haka, wato Genotype Test.  Su kuma dabi’un da suka bayyana bayan an haifi wannan jariri, su ake kira Phenotype, wato Nau’in Dabi’ar Halitta na Zahiri.  To amma ta yaya suke iya sauyawa daga lokaci zuwa lokaci? Ta yaya ake samun canzawar dabi’a da kuma canzawar yanayin mu’amala a tare da mutum guda?

Amsa wannan tambaya ne ke tabbatar da hakikanin ma’anar wannan fanni na Phenotype.  Malam ilimin halitta suka ce wadannan dabi’u da siffofin halitta na zahiri da ke bayyana, babban dalilin da ke samar da su shi ne tasirin mahalli.  Malaman wannan fanni suka ce bayan an haifi mutum, nan take sai a fara samun alaka tsakanin wadannan bayanan halitta da ke cikin Kwayar Dabi’ar halittarsa da kuma irin mahallin da yake rayuwa a cikinsa.  Wannan nan ke tabbatar da sauyawar dabi’unsa na mu’amala, da dabi’unsa na zamantakewa, da kuma yanayin dabi’ar sinadaran da ke cikin jikinsa.

A yayin da ake wannan zamantakewa tsakanin Kwayar dabi’ar halitta da ke can cikin kwayar halittar mutum, da kuma muhallin da yake rayuwa a ciki, tasirin wannan mu’amala ne ke aikin wadannan sauye-sauye da muke gani a zahirin rayuwarmu.  Ko dai na launin jiki, ko na girma ko gajarta, ko na nau’in sinadaran jiki, ko na nau’in dabi’ar zamantakewa, ko na nau’in halayya.  Tasirin mahalli ne ke da alhakin wannan sauyi.  Wannan tasiri ne ke daukan tsakanin kashi 20 zuwa 60 na dabi’ar halittar dan adam, a yayin da bangaren dabi’un halitta da ya gado daga kwayar dabi’ar halittar iyayensu kuma ke da alhakin samuwar tsakanin kashi 40 zuwa 80 na wannan sauyi.  Nan take kwararru a fannin bincike suka ce a talakance, kowane bangare (tsakanin bangaren dabi’un asali da aka gado ta kwayar dabi’ar halitta, da kuma bangaren tasirin mahalli) yana daukan kashi 50 ne cikin dari na samar da wannan sauyi na halitta baki daya.

Babbar ka’idar kwatancen ilimi (Formular) da Malamai suka samar don samar da kyakkyar fahimta kan wannan fanni na ishara ne ga wadannan alaka.  Don haka suke cewa: Nau’in Dabi’ar Halitta ta Zahiri (P) = Nau’in Dabi’ar Halitta (G) + Mahalli (E).  A wani kaulin kuma suka ce:  Nau’in Dabi’ar Halitta ta Zahiri (P) = Nau’in Dabi’ar Halitta (G) + Mahalli (E) + Cakuduwarsu (GE).   Kwatancen farko ta nuna alakar dake tsakanin wadannan abubuwa ne guda biyu; da Nau’in Dabi’ar Halitta (Genotype) da kuma Mahalli (Environment).  A kwatance na biyu kuma, an bayyana hakikanin mai sabbaba wannan sauyi ne a fili, wato cakuduwar wadannan abubuwa guda biyu.

Duk da cewa wannan ka’ida ta kwatancen ilimi a sawwake take kamar yadda kwatance ya nuna, amma kokarin tabbatar da hakan abu ne mai matukar wahala, kamar yadda masana suka nuna.  Dalilinsu kuwa shi ne: duk wani abin da ya shafi Nau’in Dabi’ar Halitta (Genotype) da ke boye a kwayar halittarsa –  irin su Sinadaran kuzari (Protein) da ke cikin kwayar halitta (Cell), da Nau’in jini (Blood Group) – sun shafi Nau’in Dabi’ar Halitta ta Zahiri (Phenotype) kai tsaye.  Don haka, bambance tsakaninsu a aikace abu ne mai matukar wahala.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Abbas s lawan says

    Muna jin dadin kasancewa da wannan shafi
    Matukar jin dadi Allah yadada karo fahimta da sani

Leave A Reply

Your email address will not be published.