Tsarin “Cashless” Da Hanyoyin Inganta Shi a Najeriya (2)

Tarihin Tsarin "Cashless" a Najeriya

Marhalar farko ya fara aiki ne ranar 1 ga watan Janairu, 2012, inda bankin CBN ya ƙayyade bankunan kasuwanci daga jigilar takardun kuɗaɗe da kansu, zuwa amfani da kamfanonin jigilar takardun kuɗaɗe masu zaman kansu. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a 3 ga watan Maris, 2023.

75

Asalin Tsarin “Cashless”, 2012

Bayan dogaro da takardun kuɗaɗe dake yawo a hannun mutane, bankin CBN ya lura bankuna na kashe kuɗaɗe masu ɗimbin yawa wajen ɗawainiya da takardun kuɗi – daga bugawa, da ɗaukowa, da adanawa, da kuma karɓa daga hannun mutane.  A shekarar 2009 kaɗai, da bankin CBN da sauran bankunan kasuwanci sun kashe naira biliyan 114.5 (₦114.50bn) wajen jigilar takardun kuɗaɗe kaɗai.  Ya zuwa shekarar 2012 kuwa, wannan adadi ya haura zuwa naira biliyan 192 (₦192bn) wajen jigila da tsabar takardun kuɗi kaɗai.

A ɗaya ɓangaren kuma, galibin kuɗaɗen da ake tasarrafi dasu wajen kasuwanci duk takardu ne.  Misali, a shekarar 2010, ƙididdiga ya tabbatar da cewa, kashi 99 cikin 100 na kuɗaɗen da mutane ke ta’ammali dasu duk takardu ne da ke ƙasa da naira dubu ɗari. Kashi 1 ne kaɗai ake aikawa da karɓansu ta hanyar na’urorin zamani.  Bayan haka, a shekarar 2012, bincike ya nuna cewa kashi 33 cikin 100 ne na jama’an ƙasar nan ke da taskar ajiya a banki, ko ke ta’ammali da tsarin banki wajen hada-hadar kuɗaɗe.  Wannan ya ɗaɗa tabbatar da dalilan da suka sa takardun kuɗaɗe suka yawaita a hannun al’umma.

Waɗannan shi ne abubuwan da nazarin bankin CBN yayi a a shekarar 2011.  Daga nan ne kuma ya yanke shawarar da samar da wani tsarin hada-hadar kuɗi da zai rage yawan abin da ke hannun jama’a na takardun kuɗi.  Ya kira wannan tsari da suna: “Cashless Policy”.  An kuma tsari aiwatar da tsarin ne a mataki-mataki.

Marhalar “Cashless” na Farko

Marhalar farko ya fara aiki ne ranar 1 ga watan Janairu, 2012, inda bankin CBN ya ƙayyade bankunan kasuwanci daga jigilar takardun kuɗaɗe da kansu, zuwa amfani da kamfanonin jigilar takardun kuɗaɗe masu zaman kansu.  Sannan ya umarci bankuna da su daina biyan cak da ya haura naira dubu ɗari da hamsin a kan kanta, dole sai dai a sa a taskar ajiya.  Zuwa watan Afrailu na shekarar 2012 dai har wa yau, bankin CBN ya sake umartan bankuna da su fara wayar wa masu ta’ammali dasu kai, kan fa’idar amfani da hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani wajen aikawa da karɓan kuɗaɗe.  Daga nan kuma babban bankin Najeriya ya sake fitar da sanarwar cewa iya naira dubu ɗari biyar kaɗai za a iya cirewa a matsayin tsabar kuɗi ga ɗaiɗaikun mutane.  Ga kamfanoni da hukumomin gwamnati kuma naira miliyan uku.  Duk abin da ya wuce haka, za a caji mai cirewa kashi 3 cikin ɗari na adadin kuɗin da zai cira.

Wannan tsari an aiwatar dashi ne iya birnin Legas kaɗai, kuma an ci gaba da aiwatar dashi har zuwa ƙarshen watan Yuni, 2013.

- Adv -

Marhalar “Cashless” na Biyu

Bayan bitar wannan tsari a marhala ta farko, sai aka ƙara faɗaɗa tsarin zuwa wasu jihohin ƙasar nan, daga 1 ga watan Yuli, 2013.  Waɗannan jihohi kuwa su ne: Jihar Ribas, da Jihar Anambra, da Jihar Abia, da Jihar Kano, da Jihar Ogun da kuma Babban Birnin Tarayya ta Abuja.  A waɗannan wuare ko manyan biranen waɗannan jihohi aka ci gaba da aiwatar da sabon tsarin, har zuwa ƙarshen watan Yuni, 2014.

Marhalar “Cashless” na Uku

Wannan ita ce marhala ta ƙarshe, inda aka sanar fara aiwatar da wannan tsari a dukkan jihohin Najeriya baki ɗaya.  Hakan ya faru ne daga 1 ga watan Yuli na shekarar 2014.  Sai dai kuma, wasu kan tambaya wai shin, ƙasarmu ce kaɗai ta fara wannan tsari ko akwai wasu ƙasashe da suke kan aiwatar da tsarin “Cashless” ko ma suka aiwatar?

Tsarin “Cashless” a Wasu Ƙasashe

A wani ziyarar aiki da na taɓa kaiwa ƙasar Amurka a shekarar 2019, don halartar wani babban taron shekara-shekara kan tsarin hada-hadar kuɗaɗe na zamani da ake yi mai suna: “DC FinTech Week”, wanda kuma ke gudana a birnin Washington na ƙasar, na haɗu da wani bature da ya sanar dani cewa shi har ya mance wace rana ce ya riƙe takardar kuɗi a hannunsa.  Yace komai ta hanyar katinsa yake aiwatarwa.  Haka abin yake a galibin ƙasashen da suka ci gaba, inda fannin sadarwa na zamani ya haɓaka, tare da kyakkyawar zumunci tsakaninsa da fannin hada-hadar kuɗi na zamani.

A shekarar 2019 an ƙiyasta cewa, mutane sun aiwatar da hada-hadar cinikayya ta amfani da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani da ya kai dala tiriliyon 3 ($3 tr).  Wannan ke nuna yadda wannan tsari ke samun karɓuwa a ƙasashen duniya.  Iya bunƙasar fannin sadarwa na zamani iya bunƙasar da za a ci gaba da samu a ƙasashen da wannan tsari ya samu karɓuwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.