Filin Ji-Ka-Karu (2)

Wannan shi ne kashi na biyu na filin “Ji-Ka-Karu”. Kashi na farko ya gabata a makon jiya. A sha karatu lafiya.

178
  • Danyen ganyen bishiya wata masana’anta ce mai zaman kanta da ke sana’anta abinci don amfanin ganyen, kamar yadda muke da masana’antu a tsakaninmu masu amfani da injina, da makamashi, da kuma kayayyakin sarrafawa. Injin da ke taimaka wa kowane ganye a masana’antarsa dai shi ne sinadarin “Chlorophyll da ke cikin kwayoyin halittar da ke cikin ganyen, makamashin wannan masana’anta kuma na samuwa ne daga hasken rana da ke darsuwa a jikin ganyen, kayayyakin da wannan inji ke sarrafawa don samar da abinci kuma su ne ruwa da ke haurowa daga jijiyoyin itaciyar da ke dauke da kowane ganye, tare da sinadaran kabon (Carbon) da ke cikin iskar muhallin da itaciyar ko ganyen yake.
  • Babu abin da ya fi saurin ciyar da al’umma gaba a fannin kimiyya da kere-kere irin bincike (watau “Research”) don nemo hanyoyin yiwuwan wasu abubuwa, ko hana faruwarsu, ko nemo dalilan da ke haddasa su, ko assasa asalin ci gabansu da dai sauransu. Da wannan dabi’a ta bincike ne kamfanoni suka samo hanyoyin kere-kere  a yanayi daban-daban, likitoci suka gano cututtuka da dama da dalilan da ke haddasa su, likitocin hada magunguna suka yi bincike kan hanyoyin magance wadannan matsaloli ta hanyar samar da magungunansu, likitocin fida suka gano hanyoyin cire su daga jikinmu, sannan kwararru kan yaduwar cututtuka kuma suka zage dantse wajen samar da hanyoyin kariya baki daya.  Ta wannan hanya ce har wa yau, masana kan harkar sadarwa suka nemo hanyoyin sadarwa a tsakanin jama’a, da hanyoyin inganta murya a yayin da yake bin tafarkin da aka tura shi don isarwa, da hanyoyin taskance bayanai, da hanyoyin nemo su daga inda aka ajiye su da dai sauransu.  A takaice dai, idan mutum na son gano tasirin binciken kimiyya cikin shekaru dari biyu da suka wuce misali, to, ya kwatanta ci gaban da ke wancan lokaci da halin da muke ciki yanzu.
  • Shekaru hamsin da suka wuce babu wanda zai yarda idan aka ce an farke cikin mutum, an ciro zuciyarsa, har aka sake dasa wani, mutumin ya tashi, ya kuma ci gaba da rayuwa. Haka ba kowa bane zai iya yarda da labarin da ke nuna yiwuwar yi wa mutum tiyata cikin kwakwalwarsa ba.  Amma a yau ire-iren wadannan al’amura sun zama jiki, babu wanda yake mamakin aukuwarsu, ba don komai ba, sai dai a wancan lokaci ba kowa zai iya hankalto yiwuwarsu ba, a yanzu kuwa, ba ma su kadai ba, duk yadda ka ga damar kiyasta yiwuwar abubuwa ana iya yarda, saboda akwai dalilan da ke sa a yarda.  Wadannan dalilai kuwa kashi saba’in cikin dari daga cikinsu a fannin kimiyya da kere-kere za a same su.
  • Duk da yake ba ma iya ganinsa, sinadarin Naitirojin (Nitrogen) na nan tare da mu dare da rana safe da yamma. Wannan sinadari yana da matukar tasiri wajen tafiyar da rayuwarmu a doron wannan kasa baki daya.  Dalili kuwa shi ne, yana dauke ne cikin iskar da muke shaka.  Wannan iska, watau Oksijin (Oxygen), ita ce wacce ke shawagi a tsakaninmu har muke shaka don tafiyar da rayuwa baki daya.  Idan muka numfasa ciki, ita muke zuka, idan kuma muka numfasa waje, muna fitar da sinadarin Kabondaiokzaid (Carbon-dioxide) ne.  Wannan ke nuna mana cewa da ace za mu fitar da iska, mu kasa shigar da wani iskar ta hanyar numfashi, to mutuwa za mu yi.  Ina amfanin sinadarin Naitirojin a nan?  Tasirin sinadarin Naitirojin na samuwa ne wajen rage mana gubar da ke cikin sinadarin Oksijin da ke muke shaka kuma yake tafiyar da rayuwarmu.  Wanda da a ce zallar sinadarin Oksijin din ne muke shaka, da tuni ya cutar ko ma halaka mu.  Kai ba ma rayuwarmu kadai ba, har da muhallin da ke gewaye da mu. Saboda kaifin da ke tattare da zallar sinadarin Oksijin, da babu sinadarin Naitirojin garwaye da shi, to, da an dinga samun gobara a duk sa’adda ya hadu da wani abu mai saurin kamawa da wuta, irin man fetur da sauransu.  Amma sai Allah cikin hikimarsa ya samar da cuta da maganinta a lokaci daya, a waje daya, kuma suna aiki a lokaci daya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.