Sakonnin Masu Karatu (2020) (4)

Mu'amala da WhatsApp

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 3 ga watan Afrailu, 2020.

67

Kamar yadda muka faro makonni uku da suka gabata, daga wannan mako ma zuwa makonni 4 ko 5 dake tafe, zamu ci gaba da amsa sakonnin da kuka aiko ne. Wannan karo na zakulo sakonnin da kuka aiko ta Imel ne. Kada a mance dai, a rika rubuto cikakken suna da adireshi, sannan ana iya aiko sako ta adireshin gidan yanar sadarwar wannan shafi, wato: wasiku@babansadik.com. A ci gaba da kasancewa tare damu.
———
Salaamun alaikum Baban Sadik, ina daya daga cikin dalibanka tun daga tsohon shafinka. Ni mutum ne da nake son inga ina aiwatar da abubuwan kere-kere, amma hali na rayuwa yasa na tsinci kaina a fannin “Public Administration.” Amma duk da haka na yi farin ciki. Saboda na tarar da darussan kimiyya da fasaha (a sadda nake karatun wancan fanni). Kai kuma ina godiya ga dukkan darussan kimiyya da sauran darussa na al’amuran yau da kullum da ka koya mana. Kuma tun kafin in fara zuwa makaranta, idan mun hadu da mai shedar karatu na BA ko HND muna tattuanawa akan harkokin kimiyya da fasaha, sai a dauka ni ma na gama karatu ne a fannin. Ina godiya matuka. – Haruna Ahmad, harunaahmad120@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Haruna. Wannan zance naka haka yake. Kuma duk da cewa ni ne na gudanar da rubutun, amma cikakkiyar godiya ga kamfanin Media Trust da ke daukan nauyin buga wadannan rubuce-rubuce a duk makon duniya, tsawon shekaru. Kamar yadda na sha fada, wannan shafi na Kimiyya da Kere-kere ya faro ne tun watan Oktoba na shekarar 2006, wato shekarar da aka fara buga wannan jarida ta AMINIYA kenan da Daily Trust. Dangane da samun sanayya da kayi kan fannoni na ilmi kamar yadda ka fada, daman haka rayuwa take: duk abin da ka sa shi a ranka, kuma ka dage a kansa, duk tsaurinsa sai ka yagi wani abu daga ciki. Wadannan rubuce-rubuce da ke zuwa muku ta wannan kafa mai albarka, sakamako ne na binciken tsawon lokaci da jajircewa wajen ganin an samar da abin da zai amfani masu karatu. Ba wai kawai a rubuta abin da aka ga dama ba.
Don haka, ina farin ciki matuka da jin cewa dan abin da nake gabatarwa yana tasiri ga masu karatu. Wannan ba shi ne karo na farko da shaida makamanciyar wannan tazo don tabbatar da haka ba. Akwai da yawa cikin masu karatu da suka shiga makaranta don koyon fannonin ilimi na kimiyya da dama, duk sanadiyyar dan abin da suke kwankwada a wannan shafi mai albarka. Allah albarkaci rayuwa baki daya, amin. Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik. Ina godiya ga Allah da ya bani ikon aiko maka wannan sako, kuma ina farin cikin samun kaina a matsayin daya daga cikin dalibanka, masu bibiyar laccocinka. Bayan haka, ina iya kokarin ganin na fahimci karatun, tare da kwatanta abubuwan da nake karantawa. Yanzu haka ina tanadin mallakar kwamfuta ne, domin hakan ne zai taimaka mini da bani damar kwatanta abin da nake koyo cikin sauki. Fatan Allah yasa muci amfanin abin a duniya da kuma lahira, amin. Na gode. – Lawal Jafaru Isah, Funtua: lawaljafarisahfuntua@gmail.com.

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Lawal. Lallai kayi tunani mai zurfi wajen yanke wannan shawara naka. Na sha sanarwa cewa shi ilimi ba ya tabbata a kwakwalwar mai karatu, kuma ba ya amfanar da mai karatu idan ba kwatanta abin da yake koyo yayi ba, a aikace. Da haka ne karatun zai yi albarka, sannan ya samar da fa’idar da aka karantar dominta. Malamai sun karantar damu cewa magabata, musamman Sahabban Manzon Allah (SAW), idan suka karanta wani bangare na ayoyin Kur’ani, ba su wucewa sai sun fahimci ma’anar ayoyin, sannan sun kwatanta umarnin dake cikinsu, kafin su wuce wata sura ko ayar. Da haka rayuwarsu ta kara albarka. Don haka, ina maka fatan alheri da karuwar arziki da ilimi da fahimta. Allah sa a dace, amin. Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da wannan lokaci, da fatan Allah ya karawa rayuwa albarka, Allah ya kara lafiya da nisan kwana da hikima da basiri, amin. Ina amfani da manhajar Whatsapp ne na JB (GB) lafiya kalau, to amma daga baya idan na aika sakonni ga group sai ya nuna mini sai an jira har tsawon wasu kwanaki masu yawan gaske, alhali kuma ina jin dadin aiki dashi – don yana matukar taimaka mini wajen daukan muhimman abubuwa, kamar “status” din bidiyo da hotuna da kuma rubutu. Shin, yanzu yaya zanyi kenan? Na gode. – Nura Muhammad Mai Apple, Gusau: nuramuhammad3337@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nura. Lallai kamar yadda ka gani a tabbace, shi nau’in manhajar WhatsApp na GB, nau’i ne na musamman da jama’a ke iya aika wa wasu ta hanyar wayarsu kai tsaye, bas ai sun saukar da sabuwar manhajar daga cibiyar Play Store ba. Hakan, kamar yadda ka gani a aikace, yana samar da sauki ga da yawa cikin mutane; ko da ba ka da siginar Intanet a lokacin, za a iya aika maka ta wayarka ka saukar cikin sauki. Amma a daya bangaren, hadari ne ga wayarka. Domin tsohuwar manhaja ce, wacce a lokacin da aka aika maka ta tsufa, kuma idan akwai wasu kafofi masu rauni da dan dandatsa (Hacker) zai iya amfani dasu wajen isa ga bayanan wayarka cikin sauki, a tare da manhajar, to, wayarka da ma rayuwarka na cikin hadari.

Wannan yasa kamfanin Facebook (mamallakin manhajar WhatsApp) a baya ya fara sanar da masu amfani da irin wannan nau’i na manhajar WhatsApp cewa lokacin daina amfani da manhajar ya kusa. Hanya mafi sauki kawai ita ce, ka sanya data a wayarka, kaje cibiyar Play Store, idan kana amfani da waya nau’in Android ce, don saukar da sabon nau’in wannan manhaja, wanda ke zuwa da kare-kare masu kayatarwa da hanyoyin kariya masu amfani, sannan a duk sadda kamfanin ya aiko bayanan sabunta manhajar, cikin sauki wayarka za ta saukar, don baka damar amfani da su. Amma dogaro ga tsohuwar manhaja da ake tunkudowa ta wayar salula, wacce ba ka iya sabunta bayananta ta hanyoyin da tsarin sadarwa ya gindaya, hadari ne mai girma. Allah bamu kariya baki daya, amin. Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.