Alakar Katin “Shedar Zama Dan Kasa” Da Mahimmancinsa Ga Ci Gaban Kasa (2)

Bincike na musamman kan fa’idar katin shedar zama da dan kasa da alakarsa da ci gaban kasa. Wannan shi ne kashi na biyu.

428

Me Ke Dauke Cikinsa?

Abin da ke dauke cikin wannan kati da za a baiwa kowane dan Najeriya da ya cika shekaru 16 kuwa su ne nau’ukan bayanan da suka gabata.  Kari a kan haka, wannan kati zai kunshi bayanan da suka shafi taskar ajiyarka ta banki (in kana son haka), don taimaka maka wajen aiwatar da hada-hadar kudi tsakaninka da bankinka ko kantin sayar da abubuwan masarufi.  Sai bayanan da suka shafi tuki, wato “Driver’s License Information.”  Har wa yau, nan gaba da bayanan da ke cikin wannan kati Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (wato INEC) za ta rika amfani wajen tantance ‘yan kasa a duk sadda zabe ya tashi.  Har wa yau, wannan katin sheda na dauke ne da tambarin yatsun hannunka guda goma (na hagu da dama).  Wannan tambarin yatsu shi ake kira “Biometric Information,” wato bayanan da suka kebance ka, wadanda ta hanyarsu kada ake iya gane ko waye kai, a duk inda aka sa.

Bayan haka, akwai lambbobi na musamman da kowane kati ke dauke dasu.  Wadannan lambobi su ake kira: “National Identity Number.”  A duk sadda aka tashi neman bayananka, wadannan lambobi kawai za a shigar cikin kwamfuta, sai nan take shafin dake dauke da bayananka dake taskance a Rumbun Bayanai na Kasa (National Database) su bayyana.

Wannan kati an kera shi ne da nau’in roba gasasshe (Plastic Rubbe) mai inganci.  Sannan akwai ma’adana ta musamman (Memory) a jikinsa, wadda a cikinta ne za a taskance dukkan wadancan bayanai da suka shafe ka, kai tsaye.  A jikin wannan kati, abin da ke dauke da wannan ma’adana kuwa shi ne sinadarin tagulla da ake kira “Microchip” irin wanda ke cikin kwamfuta, wanda ke iya rike bayanan da aka shigar masa ta hanyar siginar hasken lantarki irin na zamani (Digital Information).  Idan kana da katin ATM ka dubi bayan katin, za ka ci karo da wani tambari mai launin zinare dan karami; shi ne ma’adanar da ke dauke da bayananka.  To, wannan kati na shedar zama dan kasa ma na dauke da irinsu.  Hukumar NIMC ta tabbatar da cewa nan gaba idan na dan Najeriya ya tashi tafiya zuwa daya daga cikin kasashen da ke Yammacin Afirka (West Africa) ba ya bukatar biza; wannan kati kadai zai goga a na’urar da ke bakin bodar kowace kasa (idan sun sa  wannan na’ura nan gaba kenan).  Wannan ke nuna nan gaba za a shigar da wasu kare-karen bayanai da zasu bayar da damar yin hakan kenan.

Ganin cewa akwai hukumomin gwamnati da dama da ke karban bayanan mutane a duk sadda bukata ta tashi – kamar hukumar shirya zabe, da hukumar lura da ababen hawa (VIO), da hukumar ‘yan sanda, da asibitoci, da bankuna, da kamfanonin sadarwar wayar tarho – Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar Samar da Bayanai na Kasa (National Bureau of Statistics) da ta samar da wani tsari da zai bayar da damar hade wadannan hukumomi wuri daya, don tabbatar da cewa wannan tsari na shedar katin kasa ya zama makoma gare su wajen neman bayanai, ba wai kowace hukuma ta rika karbar bayanai a nata bangare ba.  Domin a halin yanzu, idan kaje bude taskar ajiya a banki, sai ka bayar da bayanan da suka shafe a rubuce.  Idan kaje neman Lasisin Tuki (Driver’s License) sai ka bayar da bayananka.  Idan aka tashi zabe, sai kaje hukumar zabe ta karbi bayananka.  Idan wata matsala ta faru wanda ya hada da jami’an tsaro, sai ka bayar da bayanan da suka shafe ka.  Haka idan lalurar rashin lafiya ta kama kaje asibiti don ganin likita a karo na farko, sai ka sake bayar da bayananka.  Wannan maimaici ne mara tsari, mai dan karen wahala.  Kuma hakan ke nuna babu tsari cikin harkokin gwamnati.  Amma da zarar an samar da wannan tsari na katin sheda, duk zai fa’idantar da dukkan wadannan hukumomi kan dukkan bayanan da suke bukata daga gare ka.

Kariya ga Bayanan Kasa

Duk da cewa babu wata doka gamammiya ta kasa kan kariyar bayanai (Information Security Law), dokar da ta kafa Hukumar NIMC ta tsara, a takaice, yadda za a alkinta bayanan al’umma.  A sashi na 27, dokar ta tabbatar da cewa Hukumar NIMC za ta tsare bayanan al’umma, ba za ta baiwa kowa ba, sai tsananin bukata.  Kamar ga hukumar ‘yan sanda idan ana neman bayani kan wani kasurgumin barawa da ya bace, ko neman tambarin tafin hannun wani da ya arce, ko kuma don “Manufar tsaron kasa.”

Wadannan, a halin yanzu, su ne tsare-tsaren wannan hukuma don kokarin tabbatar da cin nasarar wannan tsari na samarwa da rabawa da kuma alkinta bayanan ‘yan kasa, ta hanyar amfani da Katin Shedar Zama dan Kasa (e-ID Card).  To amma, bayan bayyanar samfurin katin, kamar yadda aka baiwa shugaban kasa, jama’a sun ga tambarin kamfanin Mastercard a bayansa.  Wannan hakan, kamar yadda masana harkar sadarwa da kariyar bayanai suka tabbatar, alama ce dake nuna dasu dumu-dumu a cikin harkar.  Wannan ya haifar da cecekuce matuka tsakanin ‘yan Najeriya, musamman ma wadanda suke da sanayya mai zurfi kan tasirin hakan ga kasar baki daya, a jumlace.

Kalubale

- Adv -

Kamar kowane irin tsari na rayuwa a bangaren mu’amala, ayyukan dan adam ba rasa kalubale.  Bayan kaddamar da wannan shiri na gwamnati kan batun Katin Shedar Zama dan Kasa, masana da dama sun ambaci matsaloli ko wasu kalubalen da ke jiran wannan shiri, kamar sauran tsare-tsaren gwamnati.

Kalubale na farko shi ne rashin wata doka mai fadi wacce za ta baiwa dukkan wasu bayanai da ake tarawa ko karba daga jama’a, kariya na musamman a bangaren hukunci.  Misali, idan wani ya kutsa cikin Rumbun Bayanan Kasa (National Database) ya sace bayanan jama’a, har a karshe aka kama shi, babu wata doka da tayi bayani dalla-dalla kan ga yadda za ayi dashi, ga irin hukuncin da za a yanke masa, ko tara da za a masa.  Wannan na cikin manyan kalubale da ke fuskantar wannan tsari.  Domin dokar da ta kafa hukumar NIMC bata yi dogon bayani ba.  Ta daidai nuna cewa wajibi ne hukumar ta tsare wa ‘yan Najeriya bayanansu, sannan ba za ta baiwa kowa ba sai da dalili mai karfi, kamar abin da ya shafi tsaron kasa ko makamancin haka.

A sauran kasashen da suka ci gaba, irin kasar Ingila misali akwai doka ta kasa na musamman da ‘yan Majalisar kasar suka samar mai suna “Data Protection Act, 1998” wadda ke bayani filla-filla kan dukkan abubuwan da suka shafi kariyar bayanai, da hakkin jama’ar kasa wajen kare musu sirri da mutuncinsu ta hanyar hana wasu ko wani dan ta’addar Yanar Gizo sace musu bayanansu na sirri, da irin hukuncin da za a yanke masa idan har aka kama shi da wannan laifi.  Haka ma wasu kasashen, suna da irin wannan doka.  Amma a Najeriya har yanzu babu wata doka ta kasa gamammiya, ta musamman wacce ke bayar da kariya ga sirri da bayanan jama’ar kasar.

Masu korafi kan rashin wannan doka sun nuna cewa babbar illar hakan kuwa shi ne, a karshe muna iya samun kasarmu kamar yadda kasar Amurka ta samu kanta.  Kasar Amurka tana da dokoki na kariyar bayanai, amma barkatai suke; babu tsari, sannan babu daidaito kan hukuncin da suka tanada ga wanda ya aikata laifi irin wannan.  Kuma tunda har an samu kamfanin Mastercard, wanda kamfani ne dan kasar Amurka, a cikin wannan tsari, dole jama’a su damu.  Domin hakan na nuna cewa wannan kamfani zai samu bayanan ‘yan Najeriya kenan a tafin hannunsa.  Abu na biyu kuma suka ce buga tambarin wannan kamfani a katin da za a baiwa kowane dan Najeriya a matsayin Katin Shedar Zama dan Kasa, bai dace ba.  Domin hakan na nuna rashin alkinta wa ‘yan Najeriya mutuncinsu ne daga wani sabon tsarin mulkin mallaka, kamar dai irin tambarin da ake wa bayi lokacin mulkin mallaka, idan an debo su a jirgin ruwa za a kaisu kasar Amurka ko gonakin rake dake kasar Burazil.

Bayan damar da wannan kamfani zai iya samu na bayanan sirrin ‘yan Najeriya, kalubale na gaba shi ne, wasu ‘yan Dandatsa (Hackers) na kasar Amurka ko wasu kasashe na iya sace bayananmu ta hanyar wannan kamfani, tunda a kasar Amurka yake.  Wannan mahanga ta samo asali ne sanadiyyar badakalar hankado bayanai da ake tayi a kasar Amurka, inda wasu ke iya kutsawa cikin rumbun adana bayanan hukumar tsaron Amurka ma gaba daya, su sace bayanai, su kuma bayyana wa duniya abubuwan da suka hankado.  Ba wannan kadai ba, ita kanta hukumar kasar Amurka ba amintacciya bace wajen abin da ya shafi leken asiri.  Wannan ya fito fili karara sanadiyyar badakalar Snowden da na Wikileaks, inda ya tabbata cewa lallai hukumar tsaron Amurka na tirsasa wa kamfanin sadarwa (irin su Google da Yahoo da Facebook dsr) su ba ta bayanan mutanen da suke mu’amala dasu a shafukansu, wanda wannan haramun ne a ka’idar yarjejeniya.

Wannan ya dada fitowa fili cikin wani bincike na musamman da kamfanin PEER 1 ya gudanar kan kamfanonin kasashen wajen da ke da rumbun bayanai a kasar Amurka.  Yace kashi 25 cikin 100 na ire-iren wadannan kamfanoni sun janye bayanansu na sirri daga kamfanonin da ke da rumbun adana bayanansu a kasar Amurka, sannan kashi 81 cikin 100 na wadanda har yanzu ake adana musu bayanansu a kasar Amurka, suna son sanin a ina ne hakikatan, ake ajiye musu baynansu?  Wannan, a cewar masana, alama ce dake nuna karancin aminci da kamfanonin kasashen waje ke dashi kan kamfanonin sadarwa na kasar Amurka.  In kuwa haka ne, don me Najeriya za ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da ta shafi bugawa da tafiyar da tsarin biyan kudade ko aiwatar da ciniyyar kudi da kamfanin Mastercard?

A nata bangare, hukumar NIMC ta nuna cewa babu wata matsala kan haka.  Domin alakar dake tsakanin Najeriya da kamfanin Mastercard bai kai iya haddin da ake kambama shi ba.  Na biyu, hukumar tace matsayin kamfanin Mastercard a wannan aiki shi ne baiwa masu dauke da wannan kati damar iya aiwatar da cinikayya na kudi.  A sadda aka zo baiwa kowane dan Najeriya, inji wannan hukuma, kana da dama kace a kulle maka wannan tsari daga katinka.  Idan kuma kana bukatar haka, sai a bude maka.  Wannnan, inji wannan hukuma, zabi ne ga kowane dan Najeriya.  Dalili na uku, hukumar ta nuna cewa a Najeriya ne za a adana wadannan bayanai, cikin kwamfutoci, kuma ‘yan Najeriya ne za su tafiyar da tsarin ba jami’an wannan kamfani ba.  Don haka babu wata matsala.

Kammalawa

A karshe, wannan tsari ne mai muhimmanci, amma kamar yadda bayanai suka gabata, Gwamnatin Najeriya na da sauran aiki a gaba wajen ganin ta tabbatar da tsare-tsaren da ta ayyana.  Domin wannan fargaba da jama’a ke samu ya samo asali ne sanadiyyar rashin amintuwa da suke yi don sakacin hukuma wajen aiwatar da ayyuka masu muhimmanci.  Bayan haka, dole ne ‘yan Majalisa su yi tunanin fitar da doka gamammiya wacce za ta dunkule ta kuma fayyace dukkan dokokin da suka shafi karba, da adanawa, da sarrafawa, da mikawa (in bukata ta tashi) da kuma ladabtar da dukkan wanda yayi ta’addanci kan wadannan bayanai na sirri na ‘yan Najeriya.  Ba kafa dokar kadai ba, dole ne hukuma ta tabbatar an aiwatar da su a duk sadda bukata ta tashi.  Wannan ne kadai zai rage fargaban jama’a, ya kuma kara wa jama’a kwarin gwiwa kan cewa lallai da gaske take.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.