Sakonnin Masu Karatu (2014) (13)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

69

Salaamun alaikum Baban Sadik, dubun gaisuwa da fatan alheri zuwa gare ka.  Tambayata ita ce: ina da wayar salula kirar “Samsung” kuma ina amfani da layin MTN na kasar Ghana.  Tun shekaranjiya idan nayi yunkurin shiga manhajar tambaya ta “Google Search” sai a rubuto mini: “735 Failure to Query DNS.”  To don Allah kayi mini bayani; me yasa ake rubuto mini wannan bayani?  Daga: Sirajiddeen, Ghana.

Wa alaikumus salam, barka Malam Sirajiddeen.  Wannan na daga cikin tangardar sadarwa da ake samu tsakanin kwamfuta ko wayar salula mai neman bayanai daga wata kwamfuta ko Uwar Garke (Server) da ke dauke da bayanan da ake nema.  Cikakken lafazin “DNS” na nufin “Domain Name Server” ne.  Duk sadda ka rubuta adireshin wani gidan yanar sadarwa daga waya ko kwamfutarka, za ta je ga kwamfutar da ke dauke da wannan gidan yanar sadarwa ne, dauke da bukatarka, a irin yare ko harshen da kwamfutoci ne kadai ke iya fahimta a tsakaninsu.  Idan ta mika mata wannan sako, sai wancan kwamfuta tayi nazarin sakon, wanda ke dauke da adireshin gidan yanar sadarwar, kafin ta bayar da abin da ake bukata.  Idan aka yi rashin sa’a sakon bai je da kyau ba, ko kuma ita kanta kwamfutar da ke dauke da gidan yanar sadarwar na fuskantar wasu matsaloli na cikin gida, sai nan take ta turo wa kwamfuta ko wayar salularka wannan sako, cewa ta gaza wajen amsa bukatar da aka tura mata.  Wannan harshe ne ko yaren kwamfutoci, wanda masana harkar sadarwa tsakanin kwamfutoci ne ke iya fahimta.  Amma a duk sadda haka ta sake kasancewa, ka sake rubuta adireshin ka sake turawa, a hankali shafin zai bude.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, ina maka fatan alheri kuma Allah kara karfin gwiwa, amin.  Baban Sadik tambayata ita ce: meye amfanin wadannan kalmomin da ke cikin “Settings” na “Opera”: “Protocol” da “http” da kuma “Socket.” Shin, su ma suna da muhimmanci ne a cikin masarrafar “Opera”?  Ka huta lafiya.  Daga: Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Kano.

Wa alaikumus salam, Malam Yahuza barka ka dai.  Da farko dai, “Opera” masarrafar lilo ne ko shawagi a shafukan Intanet ta hanyar wayar salula ko kwamfuta.  Ita ce manhaja ko masarrafar da ke nemo maka shafin da ka bukata a Intanet.  Wadannan kalmomi na ishara ne ga ire-iren kayayyakin aikin da take tinkaho dasu.  Kalmar “Protocol” na nufin “kaida ce ginanniya irin ta sadarwa tsakanin na’urorin sadarwa na zamani.”  Kalma ko gungun harafin “http” kuma shi ne: “Hypertext Transfer Protocol,”  wato “ka’idar sadarwa mai aikin nemo shafukan Intanet masu dauke da rariyar likau kenan.”  Idan ka shiga shafinka na Facebook misali, duk wata alama da za ka matsa ka ga an budo maka shafi na bayanai ko hotuna ko bidiyo, to rariyar likau ce, wato “Hypertext Link.”  Sai kalmar “Socket,” wacce ke nufin “mahada tsakanin na’urorin sadarwa biyu, ko hanyoyin sadarwa biyu, ko kuma tsarin sadarwa guda biyu; da mai karba da mai bayarwa.”

Wadannnan tsare-tsare duk suna da muhimmanci, in ma ba su bane kashin bayan wannan masarrafa ta Opera gaba daya.  Su ne masu taimaka mata nemo shafin da kake bukata daga wayar salularka zuwa inda shafin yake.  Su ne masu hada wayarka da dukkan wata na’ura da ke son hada alaka tsakanin wayarka da ita a babin sadarwa.  Sannan su ne masu budo maka shafuka masu mashigi, daga inda kake zuwa wani shafi, cikin latsawa ko matsawa guda.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Assalaamu alaikum, da fatan Malam Baban Sadik yana lafiya, Allah yasa haka amin.  Don Allah Baban Sadik ina so a taimaka a sanar da ni yadda ake shiga tsarin nan da ke ba da damar mu’amala da fasahar Intanet na tsawon wata guda a naira dubu daya kacal, a wayar Tecno D5, Android.  Kuma, ita ma wannan wayar ana sa mata wasu “Settings” ne don yin mu’amala da fasahar Intanet?  Na gode, Allah ya kara budi da basira da taimako a kan dukkan lamarinka, amin.  Daga: Babani A. Garba, Malam-madori, Jigawa.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Babani.  Ban san da wani kamfanin waya kake son yin amfani ba.  Kowane kamfanin waya na da nasa tsarin.  Don haka kana iya tuntubar kamfanin wayar da kake amfani da layinsa, ko kake son yin amfani da layinsa.  Ko kuma ka tambaya abokananka ko kwararru a harkar waya a inda kake, za su taimaka maka wajen baka bayanai masu gamsarwa.  Sai dai kuma, sabanin yadda kake tunani, shi wannan tsari ba wai daga farkon wata zuwa karshe za a baka daman mu’amala da Intanet kai tsaye babu kakkautawa ba.  Ya danganci yadda kake mu’amala da shi.  Za su baka bayanai ne (Data) wadanda za su zama mizani a gare ka duk sadda kake shiga Intanet.

Idan har ka cinye wadannan bayanai naka kafin wata ya kare, shikenan, ba za ka iya mu’amala da fasahar Intanet ba. In kana da kudi a katin wayarka nan take za su fara jan kudin kai tsaye.  Amma idan baka cinye wadannan bayanai ba, kana iya mu’amala da Intanet har na tsawon wata guda.  Idan wata ya kare baka cinye ba, sai a sandarar dasu, har sai ka sake sa kudi ka sayi wasu bayanan, sai a hada maka da na baya.  Da fatan ka fahimci wannan tsari daga wannan dan gajeren bayani.


Assalaamu alaikum, Allah ya kara maka daukaka, amin.  Tun shekara biyu kenan ina neman adireshinka sai yau Allah yasa na samu.  Allah ya kara maka fasaha amin.  Yaya ake yin rajista ne da Yahoo!?  Daga: 07065102625

Wa alaikumus salaam, ina godiya matuka da wannan yunkuri naka mai kyau.  Allah saka da alheri da wadannan addu’o’i, ya kuma kara dankon kauna a tsakaninmu.  Dangane da tambayarka kan rajista a shafin Yahoo!.  Idan kana iya mu’amala da fasahar Intanet a waya ko kwamfutarka, ka shiga wannan shafi www.yahoo.com daga can sama ta bangaren dama za ka ga inda aka rubuta “Sign Up for Yahoo! Mail,” sai ka matsa.  Kana shiga wajen za a budo maka fom da za ka cika, ka zabi sunan (username) da kake bukata, tare da kalmar shiga (password).  Samun wannan akwatin Imel ne zai baka damar shiga dukkan shafukan gidan yanar sadarwa na Yahoo!  Da fatan ka gamsu.  Na gode Allah saka da alheri.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.